Sashe 39
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read
Duk wani abin al,ada na buki angama lafiya sai fatan Alheri ga auren mu da yan uwa da abokan arziki ke gabatarwa a gare ni. Abokan ango sun rako ango daki daya sha gyara sai kyali yake don katan alatun dayaji wanda a kauyen mu kaf idan da ca muke nabar tarihi a kauyen namu don haduwan dakin namu. Sai dai may bayan tafiyan abokan ango da kamar minti goma Jamil ya dawo daga rakiyan su yace hadizatul kubura yau dai Allah ya cika muna gurin mu akan jajircewan mu da juna. Ina dan murmushi na bude fuskana ina fadin bisa ga taimakon baba kabiru bawan Allah muka samu wanan cikan gurin namu da yake Allah yace ni matar kace jamil. Banda abinda zance da baba kabiru sai fatan Allah ya saka mashi da alheri yadda ya rike zumuci Allah ya bashi ladan zumunci kamar haka. Duk maganan da nakeyi jamil sai bin dakin da wani irin kallo yake wanda ba zan iya fassara shi a lokacin na burgewa ne ko na wani abu ba. Budan bakin shi bayan na gama magana sai cewa yayi dani amma dai ke har yanzu yarinya ce khadija wani kokari sukai maki a nan daki kamar na kauyawa. Da mamaki na juyo ina kallon shi ya ce eh duk irin dukiyan da mahaifin ku ya bari da wanda ya tara maku wanan abin zasuyi maki ga auren ki ? Yanzu dai ai kinga abinda nake fada maki ko da ina fada baki yarda yanzu don Allah wanan kayan yan kauyen tsohon yayi ya dace ace sunyi maki ? Tsaye nayi galala ina kallon shi don jin abinda yake fada a lokaci wanda ban san amsan da zan bashi ba kan maganan da yakeyi din. Yace eh na fada kuma gaskiya nake fadi da ke yar su ce wallahi ba zasuyi maki wanan wullakancin ba haka da komai na zamani zasu kawo muna. Amma da yake ke baki da wayau har wani addua kike kokarin zabga mashi irin haka ni har kunya naji da abokai na suka shigo suka samu dakin namu a haka. Yanzu jamil duk wanan uban kayan basuyi maka ba kake nufi yace wallahi basuyi min ba hadiza duk sake su zamuyi musai na zamani da ake yayi mu saka don abin kunya ne a gurina abokai na su zo suga dakin matana haka a wullakance bayan sun san yar gidan wanda na aura. Na fada maki ba son ku suke da zuciya daya ba kece baki yarda kin kasa fahinta na duk lokacin da nake fada maki sai ki dinga daukan magana kamar ina son hadaki dasu ne. To ai yanzu kin gani da idanuwan ki abinda sukai maki yar bare kike a gurin su kin fi nan gare su jima wani karamin tv da wasu kujeru na raini da suka saka maki a daki don Allah. Yar su da suka aurar haka kikaga sunyi mata ke baki tunanen haka da bakin ki ke fada min irin tsaruwan dakin hajara yadda suka gyara mata dakin. Kasa magana nayi sai tsayjn danayi galala ina kallon shi don yau na tabbatar mutum bai da kunya shi da ko pant ya kasa saya ya kawo min a matsayina na wace zai aura da kowa nasa ya kasa yi mai wani abin azo a gani a matsayin shi na dan su. Sannan iyayyena sunyi min abin arziki zai zo ya rena mamakon ya yaba da kokarin su a kaina da yake dan duniya ne sai yace koda yake ke har yanzun baki san komai ba ai. Don wallahi wanda suka sayar da gidan mahaifin ki a abuja ya fadi inda ba a karya kudin da aka sai wanan gidan naku zai iya sai maku ukun wanan ma don girman gidan mahaifin naku. Kuma kin san gida a abuja tsadane dashi nina dauka ya aje sauran kudin ne ai don laluran ku kawai wallahi nan hankalina ya daga sai dai ina tuna zancen baba kabir akan maganan baba na bashin da banki ke binshi sai nace niko ina ganin baba kabiru ba zai muna haka ba gaskiya. Ya bata rai sosai yana fadin ke may kika sani don Allah an barku a duhu ana cutan ku ya ja tsuki yana cire tufafin dake jikin shi fuska a daure. Idan akwai abinda naki baga jamil ya daure mun fuskan shi shima yasan da hakan yaune daren auren mu dashi duk da ba farkon kasancewar mu tare ke nan ba. Amma sai na koma fadin sun cuci kansu wallahi don mu basu cuce mu ba don amana muke a gare su dan uwansu ya haifa ya bar masu amana duk abinda sukayi mun barsu ga Allah. Wanan maganan da nayi yasa ya dan sassauta daure fuskan dayayi da farko don ya fara shawo kaina ke nan don duk takona ya sani kamar yunwar cikin shi. Mun raya dare mu kamar na sauran ango da amarya sai dai da safe kuma ya tashi yana cika yana batsewa duk a kan maganan dai dakin baiyi mashi ba. Ban fito ba sai da gari ya dan haska zuwa gaida iyayyen shi dake cikin gidan inda na zube daga kofan su ina gaida su da kwana ban san jamil yana dakin zaune ba tare da mahaifi nasa. Jin muryana mahaifin nasa yace in shigo daga ciki yana fadin ashe kuma haka mayaudaran ubannen ki sukai maki ya tabbata ke nan sun cinye maku gadon ku ko ? Nace baba basu cinye ba har yanzu kudin bai fito bane na baba yace sunciye mana waye bai san wanan maganan ba ya ta. Yanzun dai kuyi hakkuri da dan abinda suka kawo maku din tunda kin shigo cikin mu komai zaizo da sauki don ba zamu saka ido muga ana cutan ku ba haka ai. Nayi maki alkawarin zamu tsaya maki akan komai dake da yan uwan ki muddin muka samay ki a yadda muke son ki mai biyayya a gare mu. Nace insha Allahu baba mun gode yadai dan muna fadan zama tare da nusar dani akan saurin yarda da iyayyen nawa da nakeyi. Nayi godiya na bar sashen nasu don tsakanin mu dasu ba wani nisa bane kusan ma dakunan a hade suke sauran yan hayan da ba a tayar ba suna a dayan bangeren su uku. Ya ganin amarya suna ta zuwa daga gidan mu wasu kuma suna zuwa yi min sallama don komawa gidajen su an bude dayan buhun shimkafan da iyayyenba suka kawo na gara a gidan suna dafa ma yan uwan su da suka zo gurin buki. Sai dai abinda ke ban mamaki duk wanda yazo yana yaba kyawon dakin nawa in ka debe daidaikun yan uwan jamil dake tabe bakin su. Dangin mahaifiyar shi da suka zo buki a wurin su nake jin ashe su suka zo da turamay nan da aka kai gidan mu ke nan, nan iyayyen shi su basu kashe mai komai ba kenan. Ranan dai wuni nayi ina taron baki a gidan sai dai yakan shigo jefi jefi yana wani cika yana batsewa na rasa gane kan shi a gidan ga baki daya. Zaman sati dayan da mukayi kullun a cikin korafi yake akan shi shirin dakin bai mai ba har dai na hakkura na tambaye shi yanzu yaya kake son ayi ke nan yace yanzun kikai magana dai. Abinda nake so shine mu sayar da wanan kayan a sai wasu wanda ya dace damu a dakin ina ganin haka zaifi bada ma,ana sosai nace kana ganin haka zai yuyu tun ban kai wata daya da aure ba ace na sayar da kayan dakina. Baka ganin zasu ga na rena da abinda sukai min a baya yin hakan zai kawo wani rigima a tsakanin mu nan gaba a hasale ya furta ina ruwan su dake yanzu ina sun sauke nauyin su da ke kansu suke gani da wanan abin da sukai maki suna ganin burgewa ne a gurin su. Yanzu muke da ikon ki basu ba don nauyin ki ya dawo gare mu ke nan ba ruwan su da abinda zamuyi maki anan kuma yanzu. Nace to shike nan yace da kaina zan kai kayan nan can kauyen mahaifiyana a sayar muna dashi muzo mu cika kudi a sai maki na zamani wanda ake yayi. Nace idan kana ganin haka zaifi a kai a sayar din na kuma gode da kaunar da kake mun din dani da yan uwa na ya saki wani shu,umin murmushi a fuskan shi. Bai bar dakin ba nan ya zauna muna hiran yan uwan mahaifina na zage ina fadin karya da gaskiya ga irin rikon da suke muna a gidan baba kabiru din. Yana ta faman zugani ina hawa ina ganin gaskiya yake fada min don banda masoyi bayan shi a duniyan nan kaf baki daya. Washe gari ya bude kofan falona ta baya ashe tare da motar daukan kaya yake ina ji ina gani Jamil da wasu mutane suka kwashe kayan falon nan kaf suka fice dashi a gidan. Sai da yai kwana biyu bai dawo ba a cikin kwana na uku ne ya dawo garin fuska a daure ya shigo min ina jin muryan shi yana gaisawa da iyayyen shi bayan ya gama dasu ne ya shigo yana kara sha min kanshi. Ba daman in tambaye shi zancen kayan don banga fuskan haka ba a gurin shi abinda ban sani ba ashe ya fita yaje gidan wata dillaliya ya juye mata kayan ta bashi kudin shi ya biya bashin da ake bin shi na party bikin daya hada sai sutura na alfarma da turararuka daya kara saye. Sauran kuma ya hole da yan matan shi sai da kudin suka kare ya dawo gidan a lokacin shine yake cika yana batewa don kada inga fuska shi in tambaye shi yadda akayi da kudin kayan. Sai da yaga ban tambaye shi zancen kayan ba wanda ni a zahiri tsoron haka nake ji yasa ban tambaye shi ba amma zancen kaya yana a raina. Don ina jin kunyan mutane suna shigowa suna ganin dakin haka ba komai a cikin sa alhalin kowa gari yasan amin kayan daki na alfarma. Matsalan farko dana fara fuskanta shine akan ibada sam Jamil baya sallah ko wani iri da safe sai sha dayan