Sashe 34
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 4 min read
da fadin ban taba tsanmanin zakuyi wa wanan bawan Allah butulcin ba kabiru akan irin kokarin da yake a kan ku. Hakkuri muka shiga bashi muna fadin ya yafe muna munyi a kan kuskure da zufan mutaje ne don bamu san haka zancen yake ba ai. Muka mike simi simi don barin sakin don shi baba kabiru bai iya furta komai ba a lokacin sai baba yushau yace ai ba tafiya zakuyi ba. Ku zauna muka dawo a inda muke yace yanzu ku bakuji nauyi da kunya ba kan rikon da bawan Allah nan yake maku don mu din nan badon shi yana a cikin mu ba ina zamu shiga zuwa nemawa mahaifin ku dukiyan shi a kasan nan. Umma ne ta karbe da fadin duk wanan tsegumin yana gurin wanan mai shegen idanuwan kanana da kuke gani ba kowa ke zugata ba kuma sai wanan famfararen yaron da ta lakanta Jamil. Na fada maki ko mutuwa zakiyi sai dai ki mutu don ba zamu aura maki shi ba muddin ina raye sai dai ki mutu naji haushin wanan maganan da umma tayi a kaina a gaban iyayyena maza da suke da Alhakin daura min aure koda kuwa ace iyayyena suna raye ne sune dai din ma daura aure na a duniya. Ban iya cewa komai ba haka muka bar dakin a cikin bacin rai muna shiga daki kanwata sumaiya ta hauni da fada sosai tana fadin sai da tace muna kada muyi wanan maganan muka zo mukayi. Budan bakin Baffa sai cewa yayi da ita ke dole fa mubi ba ba,asin dukiyan mu don muna da gaskiyan mu yanzu ba cewa akayi wanan gidan da baba kabiru din yake ginawa ba yana cewa nasa ance da dukiyan mu ne yake gina sa ba. Don may zamuyi shiru akan abinda yake hakkin mune ba zamu tambaya ba tace yanzun da kuka tambaya ai kunji abinda bai muna dadin ji ba don ashe baba ya tafi da bashin banki ne tare dashi kuke wanan haukan. Bata bar baba kabiru ya dawo ba sai shiryawa tayi tana fadin ita binshi zatayi ba zata zauna ba don zaman kauyen ya isheta gaskiya. Dole muma muka shirya muka biyo shi birni har muka dawo bai nuna muna komai na bacin rai ba a tare da mu sai ma dan hiran da yake jan kanne dashi a motar. Gaskiya baba kabiru mutum ne da yasan hakkin rike maraya sosai don irin kokarin da yake ya yaki zuciyar shi a kan mu da kuma iyalan shi. Don bai taba yarda a kawo sukan mu a gurin shi koda ko mune bamu da gaskiya yanzun zai ma mashi fada sosai tare da fadakar dashi illan yin hakan gare mu. Mun dawo haka rayuwa ta ci gaba da tafiya muna inda yanzu shirin auren diyar baba kabiru mace ake yi wanda yaso ace nima a lokacin tunda ba karatu nake ba na samu wani tsayayye na tsayar ya hadamu tare yai muna aure. Sai dai banda Jamil ban kula kowa har yanzu gashi shi kuma jamil din baida ranan zancen auren mu din don bai aje ba bai ba wani ajiya ba. Dole haka aka fara gabatar da bukin yar uwata a gidan inda yan uwa da abokan arziki birni da kauye suka cika muna gida. Ayi lafiya an watse lafiya kowa ya koma gidan shi a cikin farin ciki zuwa lokacin baba kabiru ya karasa ginan shi muna shirin komawa ciki ke nan. Ranan laraba muka kwashe zuwa sabon gidan mu inda a nan dakin mu daban na yara da muke zama mu yan matan dakin anty amar mu biyar ne nata daya sai mu biyu da wata diyar baba yusha,u da mahaifiyar ta ta rasu a gurin haihu. Da suka je gaisuwa ta biyo anty muka tashi mu biyar sai kannen mu maza dake zaune da ita da nata biyu muka tashi mu takwas a gurin ta. Duk da wanan yawan rayuwan mu ba zaka ce ba itace ta haife mu ba don gaskiya babu banbanci a gurin ta da wanda ta haifa damu din haka muke rayuwan mu a cikin jin dadi. Don yanzu Allah yaiwa baba din budi sosai zaman mu gwanin ban sha,awa a gidan ana cikin haka ne umma ta kawo masu ziyara a garin. Munji dadin zuwan nata sosai inda muke zama gwanin ban sha,awa babu wani tsangwama a tare damu sai dan dan gulman mutane da ba a rasa ba dake zuwa yana dawowa a tsakani.