← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 22 OF 89

Sashe 22

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 4 min read

ne a banza idan yasa maki asiri a ciki fa garin bakin kwadai ki bishi kamar karya kuwa. Dan maltinan dana fara sha ne nake kokarin amayarwa don abinda naji umma ta fadi don ina tsoron asiri kamar yadda umma din ta fada. Kanina yace humm, abin da a gaban mu ya sai muna wani magani zai sa a ciki kuma ni dai tsoron maganan umma ya kamani don haka naki cin komai a cikin kayan suka cinye shi tas suna santi. Kamar yadda mukai alkawari da su da dare sai gasu sun aiko inzo da yake mai wayau suka aiko sai umma bata san na fita ba har na dawo bata sani ba . Daddan kalaman shi gare ni sunyi tasiri sosai a raina tun daga wanan ranan muke haduwa duk dare ba tare da kowa ya san da haka ba cikin iyayyena har umma din. Sai ranan ne ta gane hakan aiko mun sha masifa dan gaba dayan mu ta hade tayi muna tas tare da alkawarin sai ta fada ma mahaifin mu wanan maganan. Tsoron kada ta fadi yasa na kama kaina kwana biyu don ina matukar tsoron mahaifin mu din tunda ya muna warning akan hakan da dadewa. Sai dai dadadan kalaman jamil suna min yawo har yanzu a zuciyana sun ki fita min a raina sai nake ganin duk duniya babu mai kaunata da yan uwana irin shi. Haka yasa alamarin shi yaki fita a raina sam hakana nake samun in dan kebe dashi mu danyi hira sama sama dashi ba tare da an fahunci hakan ba a gida. Don ita umma tana ganin na fita batun shi a yadda nake nunawa a gabanta gashi dogon hutu muka samu zamu share wurin wata biyu a gida kafin mu koma lokacin ana bada hutu yadda ya kamata ba irin yanzu ba don damana ne. Jamil dai dan kauye ne amma ya banbanta da mutanen kauyen mu wuein iya tsara kwaliyan shi da shigashin daban yake shi sai dai gajere ne baida wani tsayi sosai irin na wasu maza. Zan iya cewa ko mu dake abuja bamu fishi iya kwaliya ba don haka yake kamar mace wurin tsara ado da shiga kamar dan wasu manyan mutane can. Niko irin matan nan ne daba wani kyau gare ni ba can ina dai tsaka tsakiya ne kawai don banda abinda za a zuzuta a gare ni sai dai ilimin kawai da Allah ya bani. Baba kabiru ya kawo muna ziyara a dan zaman mu na kauyen da mukeyin hutun mu tare da wasu kayan da zamuyu amfani dashi irin sabulun wanka su omo da man shafi sai taliya da idomie daya zo muna dashi. Kwanan shi daya a tare damu ya koma tare da fadin idan lokacin komawan mu ya matso umma ta sheda mashi da wuri. Munji dadin kayan dama wanda mahaifin mu ya sai muna ya kusa karewa sai maneji mukeyi dasu kawai gashi bai kara bi ta kan mu ba tunda ya turo mu kauyen. Kanne na na yawan maganan shi akoda yaushe sai ince dasu aiki ne yayi mashi yawa sun san yadda aikin su yake. Hakan kan sa su manta da zancen don ko kadan ban bari su shiga damuwa a garin koda yaushe ina tare dasu sai mazab dakan dan fita yawo duk da muma ba wani shamaki akai muna da fita ba kowani lokaci. Ban san yadda akayi umma tasan da wanan zancen ba na ina kebewa da Jamil ranan ta haukace muna sosai tace ko mutuwa zanyi ba zan auri jamil ba wahal da kaina kawai nakeyi a banza. Kuma ko bayan ranta mukai aure dashi sai ta taso muna fatalwa ta hana mu zaman lafiya wanan zancen nata ne ya kara tsoratani. Sai ma na matsu mu koma abuja mu bar garin don samun salama a raina da saukin komai don fitinan ta ya isheni har muka kusa komawa schoool muka fara shirye shiryen komawa abuja. Duk da muna sa rai zamu koma da umma ne tunda ita ke zaune damu a can dama tun bayan rasuwan mama. Ashe abin ba haka yake ba don umma ta tace bazata koma wanan gari ba sai dai mahaifin mu ya barmu a nan mu zauna tare da ita din. Ranan sai ganin baba kabiru mukayi yazo garin sun dade daki da umma dasu baba yushau da baba musa suna tattaunawa akan zancen mu ne ashe. Bamu dai san yadda akayi ba baba kabiru ya fice da bacin rai yakai dare a garin mun dauka a nan zai kwana sai da yazo sallaman mune yake fada muna tare da wata gwagon mu zamu tafi don haka mu shirya nan da kwana uku zamu wuce. Bamu san matar ba da akace zamu tafi da ita mudai burin mu kawai muga mun koma Abujan gurin mahaifin mu ko ta halin kaka. Ranan tafiyan mu yazo motar da baba kabiru yayo muna shata zata kaimu har abuja ta iso muka shirya sai lokacin ne muka san matar da zamu koma Abuja da ita ta zauna damu a can. Muka dauki hanyan abuja cike da bacin ran rabuwa da yan uwa da abokan arziki da zamuyi a nan gida Allah ya sauke mu lafiya.
Chapter 22 · 0% Book details