← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 65 OF 89

Sashe 65

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 7 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA
5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Kamar yadda Jamil ya damu da isowan kudina haka mijin yar uwata ya damu da zuwan su shima sai dai bai yarda ya nuna zalaman shi a fili ba kamar yadda nawa mijin ya nuna .
Don ya fishi shekaru da ilimi da ma wayewa sosai don ni nawa mijin iya secondary ya tsaya shiko wanan har masters yayi a karatun boko.
Wasa wasa har aka share wata uku ba labarin kudin sai abubuwa suka fara canzawa ga matsi da yai muna yawa na talauci .
Mahaifin Jamil har gida yazo ya saka min magana wai sunji rigi rigi sakwat mana ance ga kudinan tafe sunji shiru kuma.
Nace baba lokacin zuwan su ne baiyi ba tukun aida sun sunzo abinda bana mutum daya ba ai sai hakkuri kamar yadda kowa yayi.
Allah karimun rahimun a ckin wata na hudu sai ga kiran baba wai kudi sun sauka muna a cikin dare ya kirani yana fada min haba kamar in jawo safiya a ranan.
Don lokacin Jamil baya gari na kirashi ina fada mai ya yanka wani ihu a waya yana jin dadi kamar wanda ya biyo dare sai gashi koda goma tayi yana cikin garin.
Ina tsaka ga gyara gida ya iso ina yana shiga daki yake fadin to yaya an raba ne nace har yanzu baba bai kirani ba yace kaji ko ?
Kin ga halin yaudara ko in ba haka ba kudi sun zo araba aba kowa nasa mana an tsaya jan rai sallon ayi yaudara da aka saba kuma.
Kallon shi nake da manaki yadda ya hakikance yana fada kan kudin da baida kaso a ciki koda yake shine mai kason nawa wanan zuzudin da yakeyi haka.
Misalin sha daya ya kasa hakuri yana kwance a daki ya kwala min kira na amsa na shigo yake fadin kije gidan nan kiga abinda ake da idon ki zaifi gaskiya.
Ke ma banda abinki an kiraki tun cikin dare an fada maki ba sai kiyi sakkon zuwa gidan ba amma kin tsaya kina shininiki irin wanda kika iya.
Ba abu mai wuya bane gare su su rage yawan kudin kuma nace a a gaskiya yaya za a rage yawan su abinda ke rubuce.
Sai fa baba yaba kowa waya munga yawan kudin ake fara rabawa yace ke dan Allah ja can ke may kika sani don Allah.
Haka ya matsa min dole na shirya na tafi gida naje na samu baba baya gida lokacin don haka na tsaya jiran shi har ya dawo ban raba dayan biyu tunda na tambayi kani Baffa akace sun fita da baba nasan banki sukaje tare cire kudin.
Komai na baba yana kokarin yaga ya fitar muna da hakkin mu amma huduban su Jamil yasa bamu ganin hakan da yake muna sai ma ganin laifin shi idan kudi sunzo da muke yi.
Nan na zauna ranan ba ko sakin fuska suma yan gidan sai suka share ni suna harkokin su kamar ban gidan.
Nakai kusan awa daya sai gasu sun baba sun dawo duk yayi zufa zufa dashi daya shigo, shima kani ya wani daure fuska a lokacin sai da gabana ya fadi na dauka ba kudin ne da sukaje banki ko kuma wani abin ya faru.
Ashe tsare gidane na irin kada aga walenshi ai muna rainin wayau kamar yadda aka tsara mashi din yayi.
Daga inda nake zaune naji hayaniyar su baba musa sun shigo ana bude masu falo ta baya na sauke ajiyan zuciya nasan kudi sun samu ke nan tunda suka zo.
Araina nake zagin su ina fadin ko kunya basu ji da angansu an san abinda suka zo amsa ke nan wai suce suna cin gadon mahaifiyar su.
Kanwata ta shigo da yar diyar ta suna gaisawa da mutanen gidan mu ana wasa da dariya da kowa sai lokacin naga wautana na gimtse masu danayi da farko.
Nan naso saka baki sai wata kanwata diyan baba kabiru mara kunya tace a, a anty hadiza ke da kika shigo kina daure fuska yanzu zaki ce zaki mana magana kuma.
In dai kudine karewa zasuyi mu zama daya kwana nawa ne ance ma mara mata gwauro raina ya baci sosai da maganan ta.
Ina ganin tun kudin basu shiga hannuna ba tayi min baki aiko nan na hau bakina da fada da ita sai inda na tsaya jin muryana da baba yaji ya kirani tana fadin ashe ma na zo don da ya shigo bai lura dani ba.
Nan muka mike muka nufi falo muka samay su kamar kullun baba musa ya bude da addua sai baba kabiru ya dora bayani kamar kullun tare da miko muna wqyan shi yana fadin.
Ga sakon saukan su nan ga fitarwa yana miko muna wayan ga wautana har zan karbi wayan sai kanina baffa yace ai tare mukaje baba ba sai sun karbi wayan ka ba aci gaba dai kawai.
Nan aka fitar da na mahaifiyar su sai aka fara kasafin namu kuma akayi lafiya aka kare kowa ya kama gaban shi don ko minti ashirin bamu kara a cikin gidan ba muka wuce.
Gidana muka yadda zango kamar yadda muka saba yi idan mun fito wurin su baba din nan muka shiga kullawa da warwarewa a tsakanin mu.
Muka gama shaci fadin mu da komai aka shiga kasafin abinda kowa zaiyi shidai karamin mu wanan karon ma cewa yayi duk yadda mukayi ya fita ya barmu nan.
Kamar hadin baki sai ga Jamil da adam sun shigo gidan a tare da Ahmed mijin kanwata sai wani washe baki sukeyi.
Nan mukai masu bayanin komai tare da fada masu yawan kudin da kowa ya samu da wanda aka fitar kason hajiya umma.
Ahmed din yace yanzu abinda za ayi a cire kudi da zai isa kowa sayen uncomplet building a samu a saya kada kudin su lalace muna.
Saura sai muyi lalurar mu dashi shawaran shi anyi na,am dashi sosai already dama ashe sun yanke hakan har sun cigiya muna ko an samu boyewa dai sukai muna kan hakan .
Sukai muna sallama suka tafi haba shiko gogan nawa kamar jira yake su fita cikin tsare gida yace ina kudin naki nace suna ciki na boye.
Ganin yana kallo na nasan abinda yake nufi yasa na mike na shiga na dauko mashi kudin na kawo mai ya karba yana juyawa tare da tambayan na tabbatar kudin sun kai yadda akace ?
Nace sun kai mana ko a na gida sai da baffa ya sake kirga min yawan su yace to may kike ganin za a saye dasu yanzu in an cire wanda za a sai gidan da ba a kammala ba.
Don dai data nice sai in ce kada asai wanan gina ki fara juya kudin har suyi tsoka daidai sayen gida ginane kinga sai ki zuba yan haya a ciki ko may kika gani ?
Ya tambaye ni yana tsure ni da manyan idanuwan shi nace ni dai ayi yadda yan uwana sukace kada ya zamo na fita daban a cikin su bayan mun shirya yin hakan da su.
Tun da yamman nan ya ware wasu kudi wai zai sayo abinci ya fita ban ganshi ba har dare ya dawo min babu kayan abincin wai sai gobe idan ya fita zai karbo.
Washe gari ko sai ga kanwata da mijin ta sunzo sunce an samu kangon gida jamil da baffa suzo suje su gani idan yayi masu.
Sun je sun duba kangaye nada dama sosai don gina da aka fara sun tasa sosai kuwa sukace sunyi masu sai Jamil ne yaso kawo rikici wai kangon yayi tsada ga yadda akace kudin shi.
Nan dai Ahmed ya kara fahitar dashi har ya yarda a saye din aka saye bado yaso haka a ranshi ba ba dai yadda zaiyi ne.
Bayan sun dawo sukai muna bayani har sauran kudi sun rage tun nan a gaban su muka fada masu shawaran da muka yake kan zamu gyara dakunan nmu ne.
Jamil bai so haka ba yana ganin an takura mai da yawa mijin summaiya yace zai tambaya muna set din kujeru masu kyau mu saya zuwa gobe.
An ko samu kijerun shi Jamil ya kawo shawara wai a na saka ties a falo na don shima kunyan azo aga dakin babu ledan kwarai yakeyi.
Shawaran shi ya karbu a waje na da tan uwana sukace tunda zanyi gyara ya kamata a sa ties din a falon sai a bar dakin .
Kamar wata amarya haka dakina ya koma ga ties ga tv plastma harda tauraron dan adam da fridge sabo ga su center kafet an saka a dakin.
Duk da jamil yayi na kasa wurin sa ties di dakin ya kara kudi ga abubuwa da dama sosai amma haka aka gyara dakin .
Duk ko da na bashi nasa kaso daga cikin kudin sai dai kuma bai hana shi yin na kasan ba a cikin dan abinda ya rage min din.
Chapter 65 · 0% Book details