← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 80 OF 89

Sashe 80

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 5 min read

Jin haka yasa jamil din ya mike kafa yana jiran saukan su don ya kwallafawa kudin rai sosai saboda halin da muke ciki a lokacin. Ranan da zamu tafi shida kanahi ya tashi ya dora min ruwan wanka don kada in makara na shirya ga abin karyawa daya sawo tunda dare ya aje min kamar wata basaraka dani can. Munyi tafiya lafiya munje hannu muka sa ga wasu takardu da aka gabatar muna inda matar ta yi min bayanin komai dala dala yadda zan gane komai da akeyi wurin. Bayan mun gama muka dawo a cikin dare don bamu kwana ba saboda sokoto ne zone din mu nan muka cika komai na karshe daga takardun mahaifin mu din na komai nasa. Tun a cikin daren nan da muka dawo ya sani gaba da tambaya nikan ban gane ba yasa nace mai ina ganin kudin milayan goma sha shiddane zasu fito muna. Ihu Jamil din yasa yace kin ga shike nan ai mun warke idan wanan kudi ya sauka muna kuma bamu ba sauran wahala kuma yanzu ai. Duk yan uwana muna murna da yawan kudin da zai fito muna din kamar yadda nace dasu ga abinda na gani a can cikin takardun da muka cika din a sokoto. Yau da gobe muna zaman jiran fitowan kudin kowa ya saka rai yana jiran saukan su a cikin ko wani lokaci da zamu jisu don an gama komai na fannin kudin da ya kamata ayi ko. Jin shiru har sati uku ya wuce yasa jamil din ya fara jan tsuki yana bakar magana kan rashin fitowan kudin akan lokaci ni dai ban tankashi ba iyakata ido dashi kawai. Ranan sai ga wayan baba da rana tsaka yana kirana ina waje ban sani ba ina aikin girki sai jamil ne ya dauki wayan a fitsaran ce ya amsa wa baba da fadin ina aiki idan na gama zan zo. Hakan daya fadi yaba su baba da duk suka hallara suna jirana mamaki hakkuri irin na baba ya shigo cikin gida yana fada ma matan shi abinda jamil din yace dasu a waya. Ran anty ya baci sosai don shi baba kabir da hakkurin shi cewa yayi a barshi wani lokaci su baba musa sai su dawo a raba kudin. A hasale anty tace ai kudin ba ni kadai ke da hakkin su ba don haka ta tayar da yaro yaje ya fada min da baki cewa nifa su baba ke jira duk sun hallara ko. Yaron da yazo yasamay ni ina kwashe abinci yake fada min yadda ran baba ya baci da amsan da Jamil din ya basu a waya ban tsaya jiran komai ba na fada daki na dauko hijjab dina yana kwance a dogon kujera falo yace min. Ina zaki kuma nace kiran dasu baba ke min don ance kowa yana nan yazo ni ake jira in zo ina fadin hakan na juya na fita tare da kanina daya zo kirana muka tafi. Tun shiga gidan naga bacin rai a fuskan su na nufi falo bayan mun gama gaisawa dasu ina shiga baba musa ya tare ni da fadin. An buga maki waya mijin ki yana fadin wai aiki kike wazai ci kudin naki bayan shi da zai fadawa mutane maganan banza a waya tunkan a haife shi matan mu suke aiki ai. Baba kabiru ne yaba baba musa hakkuri yabar maganan don fada yake min sosai kan Jamil din da bai ganin kowa da mutunci a cikin su yanzu. Baya baba kabiru yayi bayani sai aka fara gabatar da kudin wanda milayan hudu ne da dubu dari takwas bayan wanda aka cire dari uku akaba wa yanda sukai muna hidima acan sama. Ga yadda komai ya koma sai da hanya yanzu idan kana son abinka yazo hannun ka kuma baba bai yi hakkan ba sai da yardan mu dukan mu. Nan na fara ajiyan zuciya ina saukewa a fili don ba haka mukai tsamani ba bani kadai bace har kanina baffa a cikin halin da yake ke nan don bamuyi tsamanin ganin kudin a haka ba. Muryan baba ne yaci gaba da bayani kan kudin inda yace idan an hada kudin dana farko sun kama miliyan goma sha daya ke nan cif. Ya rufe da addua ga iyayyen mu da nasu mahaifiyar aka shafa sai dai har lokacin bamu a cikin hayacin mu ko kadan. Sai baba kabir ne ya farga da halin da muke ciki yake tambayan mu ko yaya akayi sai kanina Baffa ya kalle ni yace kiyi magana mana ke. Nace ni mai zance yanzu tunda haka aka bamu da sauri baba kabiru ya tambaya yace yaya akayi ne ko kudin basuyi maku bane? Baffa yace baba kudin nan fa miliyan goma sha shidda ne zasu zo muna ke ko ba haka kika gani ba a can kika sa hannu ? Na gyara zama ina fadin hakana na gani an rubuta da matar ta ban takarda da muka sa hannu. Innalillahi baba kabiru ya fara maimaitawa a hankali yana girgiza kanshi tare da dauko wayan shi yana bugawa lokaci guda cikin tashin hankali. Baffa kanina yace don may ba zakiyi bayanin abinda kika gani kika sa hannun ba a gaban kowa kina wani noke noke da kai kuma. Baba musa ne ya tambaya nawa ke kika saka hannu a ciki a can a takardan nace miliyan goma sha shidda ne na gani a rubuce na bashi amsa daidai lokacin da aka amsa kiran da baba kabir yayi ga wayan shi da ban san wanda ya kira a wayan ba lokacin. Anan kuma yana jin abinda na fada ya furta subbahanallahi hadiza kiji tsoron Allah ki fadi gaskiya nace. Wallahi baba shi nagani a rubuce ni ba wani ya fada min ba don har matar da ta bani takardan nasa hannu ta nuna min nagani.
Chapter 80 · 0% Book details