← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 77 OF 89

Sashe 77

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Sannu sanu zance ke zuwa min ban yarda akan jamil da dadiron shi wai basu rabu ba sun canza gari ne har yanzu ya tare da ita. Da farko wanan zancen ya tayar min da hankali sosai don har yangida mu naji zancen a gurin su sai ban yarda da su ba. Sai dai abinda ke daure min kai kuma shine yanzu zaman may yake a gida hakan ya kara ban kwarin gwiwan rashin yarda da zancen. Karshe dai na kasa hakkuri na tunkare shi da maganan da nake jin din a bakuna da yawa na mutane. Nan ya shiga fada yana zagi sai na fada mashi wanda ya fada min don kotu zai kai mai shi kara hankalina ya tashi yadda naga yana fadan nayi ta bashi hakkuri. Yace daga karshe idan na sake kawo mai wana magana ni zaiyi karan bata mai suna inyaso zan fitar da wanda ya fada min din. Hakan yasa na yarda dashi na basar da zancen duk wanda ya tare ni da maganan sai i nuna mai ba gaskiya bane wanan magana . Gani ban iya boyo ba don har gidan mu naje na fada masu yadda muka kwashe dashi din kan maganan. Nan sukai min caaa a kaina suna fadin yasan su suka fada yasa yace hakan da in kyale shi yai karan nasu daga wanan lokacin suka kara daukana shasha wace dai bata san abinda takeyi ba ma. Kowa ya kawo ido yasa mun a kan zancen ga gaskiya ana gani aka kyale ni dashi mu tafi a hakan . Kunci da talauci ya isheni babu sauran inda zan tafi in kai kukana kuma a tausaya min don ansa ko an bani shi zai karbe. Yasa yanzu babu sauran dan uwa da ke tausaya ma al, amarina kuma sai dai irin su baba kabir dana zama ma kamar dolen shi. Don abinda yake muna bai ko yiwa "ya"ya cikin shi gaskiya don yana matukar tausaya muna sosai a rayuwa . Ba dai yadda zaiyi ne mun riga da mun zabi mazajen mu dasu yasa suka saka muna ido sai dai taimakawa idan suna da halin yin hakan. Ga yanzu abin na baba kabir yaja baya sosai do yanayin da kowa na kasan nan ya shiga yanzu shima ba samu yake kamar can baya ba. Babu sauran abin kwarai da yarage min a daki sai kujerun dake falona kawai kula na kwarai da idan nayi baki ko na Jamil banda na fita kunya a gidana. Haka nake ta manejin rayuwa a wahalce don rashin da yai min katutu a gidana kamar ni kadai ce iyayyena suka fara mutuwa a duniya su barni. Yau ma ina kwance saman dogon kujeran falona tun safe nake aikin sakawa ina warwara a zuciyana don rashin samun mafita gashi ko kudin sayen garin kwaki banda shi. Balle shika ko wani abinci da zamu sarrafa a gidan. Shawara na yake a karshe in sayar da da gadona daya saura min a dakin wands shi kadai na saura dashi daga cikin kayan da akai min tun gida. Duk da ina fargaban hakan a raina amma kuma shine kawai mafita a gareni yanzu don in rufawa kaina asiri a gidana. Tunda ba kowa ke shiga min dakina ba dama iyakar bakona falo don ko banza ina jin kunyan a shigo aga dakin hakana ba katifan kwarai a dakin. Ya shigo nake fada mai shawaran dana yanke sai washe baki yayi yana fadin tuntuni naso in baki wanan shawaran ina gudun ki ce wani abu. Yanzu ki samu mai sayen gadon ne nace a,a dama kai nake jira ja shigo in fada ma idan ka yarda sai In nemi mai saye din. Yace kiyi ki shirya to ko za a samu ya shiga a lokaci nace ban samu abinda na dan dafa muna ba yau gaba daya ma ban karya ba tun safe. A, a ina ko da dari biyar barin baki ku samu abinda kukaci tunda ga kudi zasu dan shigo ya sa hannu a aljihu yana kumbiya kumbiyan ciro kudin kada in gani na tabe bakina tare da kawar da kai gefe daya. Ya ciro kudin yana miko min duk da lankwashe kudin da yayi alama ya nuna ba shi kadai bane a aljihun shi. Ni dai na karba tare da daukan hijjabina zan fita don samo muna abinda zamu sarrafa muci da rana don yanzun safiya ya wuce. Inda na barshi zaune nan na dawo na samay shi yana zaman jiran in dawo ina shigo yake ce min wai nace ai ya kamata a kwabe gadon kada tazo ta samay shi a kafe tace yana da wani bakasu kuma. Nace hakane kuma fa yanzun dai girki zan dora idan nagama sai in kwabe kafi in tafi yace bari dai in tayaki kwabewa zaifi sauki don in rage maki aiki. Na fita ya shiga aikin kwabe gadon kafin in gama hada abinci har ya gama ya fitar da gadkn wajen gidan ya jingine su. Arzikina daya ta kofan baya ya aje kayan gadon ba tare da yan haya gidana sun sani ba balle abin yazama abin magana. Bata na gama aikina muna zaune muna cin abinci yake fadin idan sauran kudin ku sunzo sai ki samu gado na zamani mai kyau na yayi ki saye. Ina mamakin Jamil ba wanan ne karo na farko da yake cika min baki kan kudin mu idan ya fito ba sai dai idon kufin sun fito kuma sai abi wani hanya dasu da ban sani ba. Na samu wata dillaliya mai saye tana sayarwa na kayan daki muka shirya da ita zata zo taga kayan sai tai mashi kudi idan zamu shirya. Kamar yadda tace din tazo taga gado tace kuma yayi mata nan muka fara cinikin kayan gado da ita. Dubu talatin ta saye da kyat ta karamin dubu uku sama nace ta kawo kudin an sayar mata take a gurin ta lale mun kudina ta bani ta fita neman wanda zai kwashe matasu Har aka fitar ba wanda ya sani a gidan shine rufin asirina saidai mai washe gari ina karyawa da safe sai gashi ya fito falon . Ya samu wuri ya zauna yana fuskanta na nasa yana da magana ke nan si kuwa bamu fi minti ralatin ba ya kawo zancen kudin. Yana fadin may kika yanke zaKiyi da kudin gadon nan dago kai nayi ina kallon shi nace. Sana,a nake son yi da wanan kudin ya gyara zama yans fadin sai nake ganin da zaki ban in fita garin nan zuwa wani gari da zaifi. Dago kai nayi tare da dakatar da abincin da nakeci ina kallon shi ya wani gyara zama yana fadin ko baki yarda dani bane . Abinda mutane ke fadi zaki dauka ni ba komai yasa nace hakan ba kinga ni wanan zaman da nake haka ya isheni. Gashi na saba yanzu da sana,a kinga in na fita na juya muna su ba,a san iya albarkan da zasu koma muna ba ai . Nan dai ya dinga kawo min dadin baki irin nasa yana tsarani har na yarda inda yace wanan karon ba Abuja zai tafi ba zai canza gurine. Zuwa bakin boarder ance sana yana daukuwa can sosai kamar may kin ga zama haka bazai yuyuba gare mu yanzu ga yaran nan suna tasawa. Amira na ina son idan na dawo mu sakata makarantar boko ta fara zuwa yakare tare da fadin ko may kikace ga shawarana. Dan shiru nayi ina nazarin sa sai naga maganar shi kuma gaskiyace idan ya fita din zaifi sana,an da zanyi a nan din samu. Sai na buda baki nace hakan za ayi sai kaje da kudin mu gani ko Allah zai sa muna albarka a cikin al,amarin. Wani shu,umin dariya yayi yana cabe yar karamar yar mu tare da fadin mamana babakin ya samu mafita ku tayani da addua, don ance addu,an yara tana kamu sosai. Tun ranan ya fara shiri kwana daya kawai yayi a tare dani ya kammala kudin shi ya bar garin ya barmu a cikin wani sabon wahala kuma. Sai da ya tafi naga wautana daga baya na yarda dashi danayi na bashi kudin yanzun gashi ya tafi ya barmu a cikin wahala nida yara. Nan sabon fadi tashi ya dawo min ina nema abinda zamu ci don ko na omo da sabulu ya ishe ni fama yanzu. Ance anbin duniya baya boyuwa koda ko kai kadai kayi shi ban san inda yan uwana sukaji wai na sayar da gado na ba. Sai ranan da na shiga wurin kanwata yar gurin baba kabiru muna ckin hira ta jefo min zance da cewa ke anty may ya kaiki sayar da gadon kwancin ki kiba namiji kudi yayi tafiya. Mutuwan zaune nayi don ban taba zaton wani yasan da wanan maganan ba sai ni sai shi muka sanda wanan maganan. Gashi yanzu magana ya fito fili har an sani wani irin bata rai nayi tare da faman rantsewa ni ban sayar da gado na bashi kudi ba. Nan dai ta dinga min nasiha akan namiji tana nuna min illolin dake cikin sakar, wa mijin bakin aljihun ka. Banji dadin da akaji wanan zancen ba dukda na nuna mata ba komai a haka ban bashi kudin bani. Dama mukan danje gurin ta mu cika cikin mu ne faman da abinci dagani har yaran sai mun koshi mu dan taba hira mu dawo gida. Amma yau wannan maganan data fito min dashi yasa naji raina ya baci da ita sosai ban ko tsaya yaran sun gama cin abinci ba nace da ita mu zamu tafi. Duk da ta gane nufina sai batai min magana ba a lokacin ta kyale ni na fice hakanan tunda ta fahinci rainane ya baci kan maganan da ta fito min dashi din. Niko damuwa da bakin cikina bai wuce ace yan gidan mu sun san da wanan maganan ba a gida tunda ko ita ta sani ke nan kowa ya gama sani a cikin dangin mu. Waima yaya akayi wanan maganan har ya fito fili akaji shi shine tambayan da nakewa kaina har na iso gida ina wanan tambayan a raina. Ga Jamil din tunda ya tafi wata biyu ke nan yanzu
Chapter 77 · 0% Book details