← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 84 OF 89

Sashe 84

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 5 min read

duk kudin namu yana gurin shi ga baki daya ya rike ranan dai munyi fada sosai dashi kan kudin. Da safe kamar baffa ya san munyi wanan fitinar sai gashi ya sallama min da kudi daya lissafa min din zai bawa kowa ya fara fitar wa sai ga Jamil ya fito daga daki fuska a daure yana shan kanshi kamar wani Alhaji dashi. Sun gaisa da baffa a tsatsaye baffa ya kirgo kudin daya ware mai daga cikin kaso na dubu hamsin ya miko mai kallon kudin yayi shekeke tare da fadin wanan fa kudin may ye ? Shima cikin daure fuska ya bashi amsa da fadin kason kane daga cikin kudin matan ku dana cire makowanin ku. Kallon kudin yayi kamar ba zai karba sai kuma ya karba yana juya su a wullakance tare da fadin wanan ne kason nawa wanan karon? Eh su muka cire maku inji baffa shima ya kara bashi amsa a wullakance kamar yadda yai mashi magana shima. Yace kasan yadda mukai tsamanin kudin ba haka suka zo muna ba don haka ayi hakkuri da abinda aka gani kamar kowa. Ya juya inda nake yaci gaba da fadin sai kudin da za a rabawa mutane gasu nan naso nakai masu amma ina ganin banda lokacin yin hakan don zan koma wurin services dina wanan satin. Fita jamil yayi a dakin rai bace bai kara bi ta kan mu ba kuma ya fice gidan ga baki daya har muka gama maganan mu da baffa din. Ashe komawa yayi kofan gida wurin wani icce ya zauna yana hadiyan rai don bakin ciki da takaicin da ke diban shi a lokacin. Shi a ganin shi an mashi rainin wayau don may za a yanka mai abinda za a bashi daga cikin kaso na kuma don wullakanci. Ya dade gurin zaune yana sake sake a zuciyar shi har ya gaji ya mike ya shiga gari don kudin basu usan shi ko biyan bashin gari balle na can inda yake zuwa din. Cikin dare ya dawo har lokacin fuskan shi ba wani walwala a tare dashi sai bacin rai zalla da yake tare dashi. Muna zaune da yarana muna hira ya shigo falon ya samay mu a zaune muka gaida shi da dawowa gida. Ya amsa muna wani iri dashi ni dai ina zaune ina jiran jin abinda zai ce min din wuri ya samu ya zauna tare da bude abincin dake rufe nasa. Ya juyo yana kallo na da tambayan yaya naga miyar ba komai a cikin sa kuma ? Nace ba komai da zan saka ka fita baka dawo ba tu dazun kuma naga yamma bayi na dora hakana. Na bashi amsa ina kawar da kaina gefe daya yace naga alaman kun shiry yi min cin mutunci ke da yan uwanki a gidan nan . Kuna son mayar dani wanda bai san ciwon kanshi ba ko wani gara can dai kuke kokarin mayar dani ? Wanan ai wullakanci ne da rainin wayau ni ake gudu da kudin ki ko may yanzu don ban gane may kuke nufi dani ba haka ? Shiru nayi ina kallon shi yaci gaba da fadin don kun raina ni za a dauki wani dubu hamsin a bani anga mabukaci ko may ? Na kasa hakkuri da maganan da yake fadi din nace ni may ye nawa a cikin maganan nan tunda bani na tsara hakan ba. Idan bake kika tsara ba waya tsara hakan kudin su ne ko naki idan ba da yardan ki aikai hakan ba yaya zasuyi hakan da kudin ki ? To bari kiji ni ba zan yarda da wanan tsarin da aka fito dashi ba yanzu dole ne ki karbi kudin ki hannun baffa ki bani in juya su yadda muka saba. Nace ni wanan ba magana na bane ka samu baffa din kuyi magana dashi zaifi amma kazo ka samay ni kana fadin kai baka yarda va nima naga kudin nawa ne. Yace sai sun cire kudin su da kaci na haya aciki saura kuma kadan kadan zai dinga bani ina sayen abu dashi idan bukatan hakan ya taso min. Bai bari nakai aya ba yace a harzuke ida baki karbo kudin na ba wallahi sai rayuka su baci a gidan nan ni za a kawo wa raini hankalin banza ko wa ? Ya kare da fadin don rashin tausayi zakiyi wa yara abinci haka babu komai a ciki may ye amfanin kudin da kika samu yanzu yana fadin haka ya shige daki ya bar ni a gurin zaune. Wasa wasa ya tayar min da hankali sosai kan kudin ya hana mu zaman lafiya shi kuma ya kasa yiwa baffa maganan kufin da bakin sa sai ni yake turawa in mashi. Tun ina boyo har yakai na kira baffa din na fada mai halin da ake ciki akan kudin baffa yace idan yana son kudin ya nemay shi mana ai bani zaiwa magana ba. Kudin da baffa ya bani in kai wa yan uwana a kauye yasa ni gaba a kansu su da yake gani a kusa sai da ya kwaci dubu talatin a cikin su da fada da komai kuwa. Sai lissafin ya bace min yadda zan raba kudin wa mutane tu ina boyo har dai najewa anty da naganan bata so saka muna baki ha amma haka ta hakkura ta yi min bayani. Ta gane cewa Jamil ne ya karbe duk da na boye nace ban gane kan lissafin da baffa yai min bane. Da taimakon shawaran ta na samu na dan tsankwarawa mutane kudin abinda ya zama abin magana daga baya gareni ke nan. Don baffa yayi fada yayi jininin yadda nayi da kudin har ya gaji ya kyale ni hakana ga Jamil ya kasa hakkuri sai da suka zauna da baffa kan yana son a ra mai kudi daga cikin kudina ya juya. Baffan yaki ya bashi a cikin lalama sai ya shigo ya samay ni yayi min bambami ya fice kan zai iya sakina kan maganan nan don baiga amfanin aure na ba yanzu tunda zan iya samu in hana shi.
Chapter 84 · 0% Book details