← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 37 OF 89

Sashe 37

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 6 min read

iya taro shi da wanan maganan haka babu kunya babu tsoron Allah a cikin sa. Sai a lokacin ya kara hasko maganan mahaifiyar su umma sosai akan zurian su Jamil din da take fadi har ta kwanta damanta ba mutanen arziki bane su. Ya dawo gida da zancen nan matan shi suka shiga tofa albarkacin bakin su kan zancen don mai zai yardan masu da hakan yasan ai ba ni kadai bace da gadon gidan da za a mamaye ma yan uwana samun su a hana su don wasu. Fada baba yayi kan su bar zancen a dai samu ayi auren kowa ya hutu zaifi alfanu idan anyi hakkuri komai sai yazo ya wuce ai dole suka ja bakin su sukai shiru akan zancen. Ni dai duk hakan ina ganin ai ba illa bane a gareni don an taimaka masu da wurin zama ba zai zama abin magana ba kuma. Ga abin magana mutaje na gani babu halin a maganta don baba ya hana maganan sai dai ayi a bayan shi don bai ba da kafan yin hakan ba shi dai gurin shi ya sauke nauyin daya rataya namu a wuyan shi yanzu. Dole ba don anso ba kowa ya saka ma zancen auren nawa ido aga iya gudun mu da baba kabir din har iyayyen nasa da suka zo da wanan korafin . Sannun a hankali kamar yadda ko wace budurwa takan yi shiri bukin ta nima haka din ne a gurina sai dai mai karatu idan nace maki ko cibi ban aje ba na kaina duk ko da Sana,an danayi a baya kada kiyi mamaki. Amma haka baba kabiru ya fitar da makudan kudi ana mun sayayya yakuma ce a tambaye ni irin kayan da nake so na daki ai min anty ta ritsani sai cewa nayi ni roses nake so tace dani yanzu an bar yayin du ka crystal nan sun fito su ake yayi nace ni dai roses nake so a lokacin haka yasa ta shiga nema min roses din ta samo masu kyau da daukan ido aka saya min. Duk wani kaya na jin dadin amare sai da baba kabiru din ya saya min su don dai kawai ya fitar min da hakkina a kanshi nan aka fara kudindumin a cikin dangi kan zance shi dai baice da kowa kala ba kan bukin. Ance rana bata karya sai dai uwar diya tayi kunya don ranan buki yazo saura sati uku bukin mu da jamil iyayyen shi suka tare a gidan namu. Babu kunya ko nauyin hakan a tare dasu alai,alai abinsu a gidan namu na gado babu nauyi ko kunyan hakan a tare dasu udan anyi magana sai suce ai gidan diyan dan uwan su ne suka zauna ciki. Don dan su dake soja ya nuna masu bacin ranshi kan hakan da yake mahaifin nasu mutum ne mai bin ra,ayin matan shi sai bai ganin illan yin hakan don ita amaryan nasa burin ta tabar gidan dan kishiyar nata da take zaune a cikin sa a lokaci. Ni kuma na samu daurin gindi a gurin baba kabir ba wanda ya isa ya fada min gaskiya abinda ake kullawa kan hakan akwai illa a cikin sa. Gani raguwa inji anty yaya zama da sarakai zaiyi dadi irin yadda nake nan ban san ciwon kaina sai dai ance fadan dayafi karfin ka sai ido kawai. Haka yasa dole suka saka ido har saura yan kwanaki buki dangi suka fara halara gurin bukin inda a bangaren Jamil ma haka ne don dangin shi sun fara isowa gidan. Kai duniya wanda baida mafadi baiji dadin duniya ba wallahi don rawan kan da nake wai ni a dole ga amarya kowa na kallo na a hankade niko ban damu ba gurina kawai inga na malki mijina a hannu na a lokacin. In huta da zama gida cikin wahala da maraicin iyayye dake damuna ko yaushe don duk wanan gatan da kokarin baba kabiru a kan ni ban ganin hakan komai da ake muna ragaggene a gurina. Don nakan ce da mahaifana su na raye da abinda za ai min sai yafi hakan ai ga gulman dagi yan hana ruwa gudu da suke zugani wai ai da dukiyan mu ne baba kabiru yake mun komai. Wanda wauta da kurciya a lokacin ya hana ni hango gaskiyar maganan da zufan shi yake muna komai da yake yi din bada dukiyan mu bane don har lokacin komai na mahaifin mu bai fara fitowa ba. Har aka sakani a lallai babu wani motsi na al,ada daga gidan su Jamil da akewa amare irin kayan da ake kawowa din nan. An gulma ya fara tashi a tsakanin yan uwa da abokan arziki kan rashin wani motsi daga bangaren angon nawa inda shi jamil sai harkan yadda bukin namu zai kawatar yake a bangare shi. Sai ana saura kwana biyu ne daurin aure wata yar shi da suke uwa daya suka zo gidan mu anyi masu taro na mutunci sosai inda suka kebe da anty uwar amarya suna bada hakkurin rashin jin su da ba ayi ba din akan lokaci. Anty cikin fara,a take fadin ai babu komai duk gida ne damu dasu bata nuna masu komai a fuska sun dan zauna sai can dai a kunyace ta bude hijjabinta ta fito da yan turamay ko a leda tsiya bai bari sun saka su ba guda shidda wai gasu nan in fitan buki dasu daga baya idan sun samu hali ina gidan su zasu saya min. An karba da godiya da sa albarka sai dan shin kafa shima kwano biyar da suka gabatar mata wai a kara ayi hidimar buki dashi. Anty tace ai da baku wahal da kan ku ba don mahaifinta komai ya tanadar muna a nan sukace a daiyi hakuri a karba din Allah. Bayan tafiyan su ne ta fitar da kayan wa mutane nan kuma zance ya tashi karshe sai fita daga gidan nayi don ban iya sauraren maganan su. Dama baba ya saya min set din akwatuna da yan tufafin da yai min da zan saka aka kara zuba kayan da suka kawo a cikin akwatin. Shi dai baba sai fadin Allah dai ya bamu zaman lafiya ace gara da akayi albarkan auren ake nema ba kyalekyalin auren ba. Ga gida ya cika da yan uwa da abokan arziki ta ko ina a gidan don bukina kawai suka hallara wasu tsakani da Allah suka zo wasu kuma gulma aga karshen abin ne ya kawo su daga kauyen mu. Shiko gogan sai waya muke a tsakanin mu inda yake kara karfafa min yadda nake a rayuwan shi da irin taimakon da nayiwa rayuwan shi din. Anje an gyara min dakina komai tsone gwanin ban sha,awa dai kowa ya dawo yana yabawa irin kokarin da baba kabir din yayi don ba a ma maganan matan shi duk da suma sunyi iya kokarin su kan sha,anin. Party kan har kala biyu aka sha don jin dadin buki wanda ya shirya da abokan shi yan karya anci ansha an gwangwaje a gurin an dawo ana bada labarin komai.
Chapter 37 · 0% Book details