← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 3 OF 89

Sashe 3

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 7 min read

wa da safe haka ya karaso gaban umma din yana gaida ita da kwana. Yana fadin umma barka da kwana an tashi lafiya ban san kin fito ba ai sai yanzu danaji muryan ki a waje. Ai kasan na tashi tunda kaji murya na din ai kasan garau na tashi ke nan yayi yar dariya tare da fadin haka ne kuma umma muryan mama ne ke gaida Abba din da kwana. Ya juya gareta yana fadin saude an tashi lafiya ya gajiyan tafiyan ya kuka bar mai jikin kuma ta amsa a sanyaye da fadin da sauki yaya mun samu an sallamo ta daga asibiti tana gida. Umma ce ta katse su da fadin kayi ta kaunar uwarka ka fita zance na ai tunda duk ta hade ku gidan ta shanye baki daya. Kuna jina da safen nan ina masifa da ita shi wanan ya fito yana wani juya laifin a kaina kai kuma ka fito kana wani gaida ita. Kaga ke nan ta zama lami kanwata gare ku ta juya tana fadan ta dauko ma baba kwano tana nuna mai tare da fadin ka duba wanan dan kokon da Saude ta zuba min don Allah. Ita baga nemowa ba sai idan an nemo dafawa yazama rowa a gare ni baba yace haba umma ai naji abinda kabiru ya fada maki yanzu ina daki. Yace kiyi hakkuri da abinda kika samu kin san ko banza saude mijin ta baya gari ba wai abincin suke dashi ba kamar ko wa. Ki bari idan sauran sun dama a kawo maki nasu tayi mai wani kallo gami da jan tsuki tana fadin ai gara saude din har naga nata matan ku da suke saraki ko fitowa basuyi ba balle su dora wuta. Suna daki sun mike kafa sai idan an kawo min su turo yaran su karya a gurina idan na hana kuma aji dadin yin gulma na na hana jikokina abinci. Baba yace haba umma su sun isa ma su zage ki ko suyi gulman ki tunda su basu girka ba sun baki akan lokaci. Murya a sanyaye mama tace umma barin in dauko maki na wurin yushau don dama ke dashi kadai na sawa sai ku kara idan ya fito na diba mai gwaben yaci. Ta shige daki sai gata da kofin silver mai marfi dan madaidaici da take zubawa baba yushau kanin mahaifin mu abin karyawa a cikin sa ta kawo gaban umma din ta aje mata. Ta kalli kofin da fushi ta bude tana dan jujuya kokon dake cikin kofin tana fadin ji wanan wai shi za a ba mai karfi kamar yushau ya karya dashi da safen nan sai ra dauko wanda aka zuba mata din ta kara mai kofin ya taso kokon yai yawa ta rufe ta aje a gurin ta. Bata mika ma mama kofin ba baba kabiru ne yace umma ki mika sauran wa yaran su sha tunda basu samu ba in yaso ida saura sun dama a kawo maki sai ki, , , Bai kai karshe ba ta tare shi da fadin kabiru ka fita idona wallahi kafin in saba maka wanan kokon na matan ku da suke damawa ruwa ruwa kamar ruwan kasari ai sai ku da yaran ku. To kuma umma kike mata wanan masifan haka bayan kin san gaskiya idan ba girkin saude ba baki son na wani. Ta bishi da harara ya bar shiyan namu zuwa waje bai wani dade ba sai gashi ya shigo da tuwo irin na sayarwa dinnan ya kwala ba hadiza data gama sallah kira. Ta fito yace su dauka suje suci da kannen ta a dakin su ta karba tare da godiya don haka maman su ta koya masu yi din idan an basu abu komai kankantan shi suyi godiya. Umma hauwa itace mahaifiyar iyayyen mu maza ta haihu da yawa wasun su sun mutu tun suna yara sai iyayyen mu ne suka rage su kadai a raye su hudu maza mata biyu. Baba Sahabi baba gwago habiba gwago laure sai mahaifina da baba kabiru sai autan ta baba yushau da baiyi aure ba. Mahaifna shi ba mai zama a karkaran mu bane don yafi fita zuwa neman kudi sai ya kwashi watanni yake dawowa da dan abinda ya samo. Sai ditan kishiyan kakan mu da suma suna da yawa a dakin su don sun fi iyayyen mu yawa duk muna zaune ne a gida daya dasu sai wa yanda basu garin ne basu zaune a gidan. Auren zumunci iyayyen sukayi don hadin gidane da mahaifina da mahaifiyata diyan mace dana miji suke don haka umma ta zama gwagon maman mu ke nan. Amma wanan baisa mama ta samu ragwamay a gurin umma ba duk da zumuncin dake tsakanin su don Umma ta kasance mace ce mai fada da jinini ga saka ido sosai a gareta. Duk kusan haka take da matan baban nin nawa ko yaushe babu mai fari a gurin ta ita a ko yaushe kusan kanta ta sani fiye da kowa. Iyayye na kaf sunyi karatun zamani gaba dayan su sai matan ne basu samu yi ba don akidar mahaifin su ne mata basu karatun boko a gidan sa. Bai bari su wani tasa sai yai masu aure wanan dalilin ne yasa yanzu iyayye mu suka fara saka mu karatun boko mu dake tasowa a cikin su. Duk wanan fadan na umma tana kokari wurin hada kan diyan ta matsalan ta ya tsaya kawai iya sarakanta da diyan ta suke aure sai ko mu jikokin ta da bata faye wani wasan jika da kaka damu ba. Nice ta farko a gurin iyayyena sai kanwa ta da ake goyo yanzu iyayyena suka haifa hakan baisa umma ta wani jamu a jiki ba kamar yadda muke ganin wasu kakan ni sunawa jikokin su a wani gidajen. Sai dai duk da karancin shekaruna zan iya fahintar wani abin don na fahinci umma tana da dan nuna bambanci a tsakanin jikokin ta mu sanman jikon diyan ta mata da mu. Da kuma wasu dake zaune a gidan tare damu wana baya damuna tunda iyayye na suna nuna min gata a tsakanin su har ma da yan uwan mahaifina suna ina suka saka dani da yar kanwata shamsiya da maman mu take goyo. Tsakanina da shamsiya akwai yar tazaran haihuwa sosai don maman mu tana haihuwan diya maza suna mutuwa har sau uku sai akan shamsiya ne ta tsaya. Don yanzu shamsiya nada shekara uku a duniya da dan kai har yanzun kuma ba a kara samun wani rabon ba. Mahaifiyar mu muka biyo a kama don mahaufin mu fari ne sol dashi don umma ya kwaso gurin fari sabanin mu diyan shi da muke chaculate colour mu ba bakake ba kuma ba farare ba. Hanci da gashi ne kawai muka kwaso na iyayyen mu wanan kaman namu ne don duk jikon umma mun dan fita daban dashi umma ke zagin mu gurin fadan ta idan ta tashi cin mutuncin ta gare mu. Zaman karkara bawani sana,a ne akwai ba na zamani amma cikin hukuncin Allah haka mahaifiyar mu ke zama damu a cikin rufin asirin Allah kafin mahaifina yayo mata sako. Wanda sakon yana fadawa ne wani lokaci a hannun umma sai abinda taga dama tabawa mahaifiyar mu daga ciki sai dai idan sakon ya fada hannun baffa kabiru ne. Zai ba wa mama su a boye ba tare da ita umma ta sani ba ko wani ta dan yi muna lalurar mu a boye batare da wani faca ka ba na zamani. Kin san yadda uwa take fama da lalurar diya mace tun daga haihuwanta har zuwa tasowan ta don ba karamin lalura kega tayar da diya mace ba. Tun daga dankune kumshi zuwa kayan sakawa dasu pant da lalurar kayan kwaliya ga kitso da sauran su amma a haka mahaifiyar mu ke kula da alamuran mu a cikin yardan ubangiji. Batare da kowa ya fahinci halin da take ciki ba muke rayuwan sai ake ganin ai don mahaifin mu yana birni ne muke ko yaushe fes fes damu.
Chapter 3 · 0% Book details