Sashe 57
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 5 min read
Jamil data rasu watau maryam. Kayan basu dauki lokaci ba aka bayar aka dawo min dasu kamar dai yadda akeyi idan an haihu ga al,adan gidan mu idan ka haihu zaka cire wa mahaifiyar ka da mahaifin ka turmi ka basu su saka maka albarka. Amma haka nayi mirsisi na hana ma kowa wanan irin al,adan na hana masu ban basu komai ba nace nima na rama ai haka dai dan kudin da ake kawo min gudun mawa . Na fitar nake bayarwa ana sawo min biscuet da butan da nake rano ina ba mutane don wanda ya sawo min ko dangin shi bai isa ba lokacin. Na dai samu aka watse lafiya duk dan abinda na samu ya tafi gurin mutane sai dai ban damu ba don ni Jamil ya gama min komai tunda ya fitar dani a kunya. Na gyara dakina da taimakon yar uwana data kai har dare a gidan mu ta soya min nama tare da wasu aiyuka muka gyara ko ina na gidan . Muka gyara akwatin tsab har ta roke wani zani nace ta bari sai Jamil ya dawo naji kudin shi zan bata shi mijin ta yazo ya dauke ta suka tafi. Gidan ya rage sai ni da yan hayana wanda suke part din su Jamil ya dawo abinda ya fara tambayana shine ina naman da aka kawo na mike na dauko mashi. Ya karbi roban ya dan jujuya ya girgiza kai tare da fadin wanan naman za a bar muna duk rago dayan nan kato daya yanka sai wanan zamu ci. Nace gidan ku fa sun cire nasu ankai nawa kason gidan mu suma sun cire na iyayye kamar yadda akeyi baiga laifin wanda yan uwan shi sukaci ba sai wanda yan uwa na sukaci ya hashi haushi. Ya dan tsince tsoka daga ciki ya zauna yaci da drinks mai sanyi ya kora ya kwanta na dauki roban na duba babu komai sai kasusuwa suka rage. Dole haka na fara amfani dashi wa gida dashi nake muna girki ina watsawa a cikin abinci idan zanyi. Kwana biyu da suna tun da safe da yake ba sallah nakeyi ba ina barci ban ko tashi ba sai hayaniyar kattai naji suna fita da buhun abincin da baba kabiru ya aiko min na kunu da tuwo. Don shine abincin da mace da ta haihu ya kamata taci nasan shine dalilin da baba kabiru ya saka min su don samun sauki a gare ni. Sai gashi Jamil ashe ya sayar ya soke kudin shi bai min maganan komai ba ina kallon shi yana kallona ba dama inyi maganan komai ya hauni da fada kuma. Kafin kwana uku da suna duk Jamil ya zauna ya tsotse kasusuwan nan daya rage ya cinye komai dana tanada wa kaina don haihuwa na in samu inci in sha indan na haihu din. Ranan muna zaune dashi muna dan hira duk akan wa yanda suka zo min gun suna muke hira sai na jefo mai zancen ina son in danyi dinki daga cikin turamay nan daya saka min . Sai cewa yayi idan ya shirya kai mun dinki shi zai kai da kanshi don haka in saka mai ido kawai yace tun wanan lokacin ban kara mai magana ba ni kuma. Haihuwa na da sati biyu matar wani wanshi da suke zaune a gidan da wansu ya gina tare da mahaifiyar shi ta haihu . Tun haihuwa da kwana uku ya turani wai in je in kama masu aiki nace kada ka manta nima haihuwa nayi ai waya zo ya kama min aiki lokacin har ya tare haka a gurina cikin su. Yace ra,ayin shi ke nan shi don haka in shirya kawai in tafi in ba bacin ranshi nake son gani ba ba wanda ya sani haka na shirya na tafi ina mai jin kunya yadda zan tare wa mutane a gida nima da jego na haka. Da zan tafi yasa na dauki turmi daga cikin wanda na samu buki a gidan mu nakai wa mai jego cewan in ji shi nashi gudun mawan ke nan. Na Kai ba wani godiya suka karba a na wani yatsune baki don gaba dayan su ba sona sukeyi ba a gidan don karara ake nuna min bambamci ba boyo. Ina gidan har sati daya don ko bayan da akai suna sai da ya yasa na kara kwanaki a gidan kuma ranan dai da dare yaje ya dauko ni na dawo gida. Na samu dakin yayi kaca kaca kin san yarda daki keyi ida an kwana biyu ba,a cikin sa dole na zage na shiga gyaran dakin kamar yadda ya kamata sai dai sama sama nayi aikin ba ko ina na gyara ba lokacin. Sai waini faman daure fuska Jamil ke min wanda ban gane hakan ba a raina nace ai dole kai bakin ciki da dawowan mu tunda zamu hana ma jin dadin da yakeyi idan bamu nan. Ban bi ta kanshi ba sai da muka cika kwana uku da dawowa ne nace bari dai in gyara dakina da kyau don har lokacin banga ya koma min daidai ba a idona. Na shiga gyara inda na fara da falo ganin na gama da wuri yasa na shiga kuryan dakin don in gyara sharo nan kwakwalo nan har nakai wurin akwatuna na sai kawai naga sun biyo ni alaman dai babu komai a cikin sa ke nan. Ban san lokacin da na yarda tsintsiyan dake hannu na ba na shiga bude akwatunan na sama na bude wanda kayan baby na ke ciki babu komai a cikin sa hatta permpers din ciki an kwashe. Da sauri na jawo wanda kayan nawa ke cikin sa shima dai hakan na samay shi wayau ba komai a cikin sa hannun na dora akai na zurma ihu ni kadai a dakin. Ba wanda ya jini jiki na rawa da makyarkyata na fito falo na zauna ina tunane kala kala idanuwana suka birkici a lokaci guda. Sai wani zufa ke yanko min ta ko ina tunanen duniya na yishi a lokacin yafi a kirga a cikin dan lokaci kada ni kadai a daki ina jin hayaniyar matan gidan daga bangaren su. Sai nake jin dariyan su kamar dani sukeyin shi sun san abin da ya samay ni ne suke rahan su a cikin gida.