Sashe 74
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 4 min read
yaranta ta debo ta bamu mu kara duk da banda su hakana na amsa sai dai na raina kayan . Har fada mata nayi yanzun ke wanan raggadudan zaki bamu don Allah tace ai itama bata da wadattacen kaya da zata bamu wanda yafi wanan din. Bayan kwana biyu suka fara shiri komawa kano har lokacin Jamil bai dawo ba sai ana jibi zasu koma ne ya dira a garin. Abin mamaki ga wanda yaje nema ana sa ran zai dawo da abin arziki baje baje sai dai shi Jamil sabani haka na gani a gare shi. Don daga shi sai yar jakkar tafiya irin ta maza ya dawo garin babu komai a tare dashi. Sai na dauka kudi ya riko ya dawo dasu gidan don wahalan daukan kayan da zaiyi daga can . Sai dai har aka kwana aka wuni banji wani abu daga guri shi ba sai kwasan barcin da yake faman yi tun da yadawo a gida bai fita ba. Abinci lafiyayye na hada mai har da ciwo bashin kayan miya a makwabatar mu na hada mai abincin. Ya tashi daga barci ya nemi ruwan wanka nakai mai da soso da sabulu ya fito lokacin na gama abinci sai da ya shirya idan ya gama zai fita. Yar karamar yar mu ce tazo wurin shi tana fadin baba mai ka sawo muna can da zaka dawo shafa kan yarinyar yayi yana fadin.. Ka dai ba kinga babanki ya iso gida lafiya ba mamana da yanzu yan fashi sun kashe maki baba a ganya ai. Cikin faduwan gabx nace yan fashi kuma ban ya shiga rabtabo min karyan da ya shirya mi duk nabi na rude. Hankalina ya tashi yadda yake bamu labarin a cikin tashin hankali nan nayi muna barka da arziki da Allah ya tsirar muna dashi daga hannun yan fashi basu kashe shiba ko su illanta shi. Yana ganin karyan shi ya kamani yace zai tafi gidan mahaifan shi ya gaida su ya fada masu arzikin daya auna a hanya. Nace tunda dai rayuwan ka ya tsira ai mun gode ma Allah arziki kuma idan da rabon muyi mayi a gaba ai. Yaji dadin magana na yace wai da Allah yasa yazo gida da kudin nan da mun warke wallahi mun fita daga talaucin don ya samo kudi sosai acan. Nace ba rabon mu mare masu bane Allah ya kawo hakan nan nayi ta kwantar mai da hankali da dadden magana har ya samu ya fita daga gidan. Yana fita na nima na fita wurin yan hayan mu ina fada masu suyi min barka da arziki yan fashi Jamil ya hadu dasu a hanya sun kwace mai komai nasa da zai dawo. A gabana sun min jaje sosai da Allah ya kare gaba kuna sai dai ina basa baya sukace wawiya ya tsarata ta yarda. Nan dai suka zauna suna gulmana a gurin suna zagina kan irin watauna gurin miji daya tsara ni sai in yarda da karyan shi. Yinin rana duk wanda na gani sai ba bashi labarin mijina ya auna arziki da yan fashi a hanyar shi na dawowa gida. Komai basu barshi dashi rayuwan shi kawai ya tsira dashi a gurin su wasu suna yarda wasu kuma suna mn kallon shasha ban sani ba. Da yamma yar uwata tazo nake fada mata abinda ya faru da jamil din a hanya. Sai cewa naji tayi kai amma Jamil din nan bai ma ko iya karya ba wallahi da wani irin kallo mamaki na dago kai ina kallo ta. Ban bari ta karasa maganan ta ba na hauta da fada harda zagi inda nake shiga ba nan nake fita ba don raina ya baci sosai da kalamin ta. Tace Allah baki hakkuri anty nima rigima na ya kaini fafin haka ai ta mike tare da fadin zata karasa gidan baba kabiru tayi masu sallama. Ko kallon arziki bata samu ba a gurin balle a dawo lafiya yadda muka saba yi idan tazo gurina sai mu dade muna zuba hira dasu. Ba yar uwata ba a lokacin duk wanda yayi gigin tara ta ya fada min wanan magana wanke mai shi zanyi tas don idona da rufe. Sai kuma yadda na yarda da Jamil ya sa ban iya gano illar shi ta ko ina aka fito da zancen sukan shi a gabana. Don haka kowa yaja bakin shi yayi shiru tunda ban bari a fadi har wasu na zuwa gida yi min jaja suna muna barka da arziki. Niko sai rabbata masu labarin yadda abin ya faru nakeyi kamar a gaba hakan ya faru yadda nake bada labarin kamar yadda ya fada min. Kwana biyu muka fara dan ciye dan kudin dake hannu na ina dan juyawa ya fara karewa sai kama kama ya rage munayi. Gadai miji yaje nema amma haka ya dawo muna hannu rabbana babu ko ledan burudi ya dawo muna gida.