Sashe 12
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read
Zaman gidan da mukayi baba kabiru ne yake tallabe damu da lalurorin mu bai taba nuna gajiya da abinda yake muna ba komai zai sayowa iyalin shi tare da namu ne. A hankali muka fara shakuwa da jamilu don gurin wasan mu daya ne dasu ba wani fin mu girma sukayi ba sosai dan abinda ya saka shakuwa a tsakanin mu shine. Karatu zamu zauna mu dinga fadar kalman turanci ina fasaara masu suna jin dadi ko in fada masu wani kallama yadda ake fadi da turanci. Ranan kwatsan sai ga mahaifin mu ya dira gari murnan ganin shi gurin mu ba,a magana ba laifi yazo ya nuna ma yan uwa da abokan arziki kauna a garin. Inda yake sheda ma umma da yan uwan shi samun sauyin wurin aiki ya samu yasa bamu ganshi da wuri ba don lokacin mun share kusan wata shidda a gida. Don haka tare dashi zamu tafi idan ya tashi tafiya haka yasa muka fara shiri inda ba wani shiri sosai mukayi ba don ba wani abin mama ke da shi ba da zata dauka anan. Satin shi biyu hutun daya samu ya kare don haka zamu koma jamil ya rubuta min wasika shifa da gaske yana so na ba wasa yake ba kada in manta da shi idan mun je. Ban dauki takardan dawani muhinmanci ba don haka na tura a kasan bage na kawai muka dauki hanya sai garin abuja inda can yanzu aka mayar da mahaifin mu. Kubuwa ya samu gida inda zamu zauna wani quaters ne da mai,aikata ke kamawa a cikin su ya samu ya kama daya muka tare a ciki. Kamar gidan da ya saba kamawa ne dakuna biyu sai falo da makeyi da kitchen sai karamin filin tsakar gida kin dai san yadda zaman bariki yake a birni. Satin mu biya muka shiga wani makaranta sai dai an mai dani baya ga karatuna don a katsina zan shiga primary five ne sai nan suka mayar dani primary four. Banda matsalan karatu don bawai na daga Allah ne don haka nake saurin haddatace duk abinda aka koya min da sauri a kaina. Ba laifi don mahaifin mu yana wadatar damu da abinci da sauran abubuwa sai dai fannin sutura ne bai faye muna tufafi ba akai sai sallah yake sai muna tufafi. Mama na zama da makwabtanta lafiya saboda rashin hayanitar ta don ita haka Allah yayi ta bata faye shiga jamma,a ba sosai. Don haka irin gulman bariki din nan da akeyi bata daga cikin masuyin don rashin hayaniyar ta tana gidan ta a ko wani lokaci. Idan kaga mahaifiyan mu bazakace itace matar mahaifin mu ba don idan baki manta ba na fada maki mahaifin mu farin mutum ne dan gaye sosai mai jin lokacin shi. Sabanin mahaifiyar mu da take baka yar kauye mara jiki ba wani kyau ne can da za a fada ba a kanta haka yasa matan bariki suke kawowa mahaifin mu hari kamar yadda sukewa maza idan sun shiga bariki. Ko baka da kudi zaka samu mata bila,adadi iya yadda kake so wanan bai dauke hankalin mahaifina gare su ba don ya tsaya ga iya iyalin shi. Akwai wata makwabcciyar mu ma,aikaciya ne da idan ta dawo aiki take shigowa gidan mu tana hira da maman mu daidai lokacin da tasan mahaifin mu yana dawowa a wurin aiki. Ashe ita mahaifina take kyarkyara a ranta ga kudi da take kashe mu idan taga abu zata sayo muna zata kaimu kitso har mama itace ta gwada mata gidan kitson mu. Sosai mama ta sake da wanan matar da sunan tana musulmane amma addini bai zauna a kanta ba sosai don mama tana yawan mata huduba sosai akan addinin ta. Shakuwa ce mai karfi a tsakanin su don har harkan da take da wasu maza takan fadawa mama idan mama taga rashin dacewa da abinda tayi takan mata nasiha akan abin. Ranan kanina baffa baida lafiya har yakai an kwantar dasu asibiti an basu gado yasa aka barmu gida daga mu sai mahaifin da idan ya dawo yake zama damu. Idan ya tafi aiki ko asibiti muke komawa mu kadai a gidan, kwana biyu da zaman su mama asibiti ranan matar da muke kiranta da anty sady ta shigo take tambayan mu har yanzu ba a sallamo mama daga asibiti ba nace eh ance sai an kara ma baffa jini kuma. Take tambayan mu a can mahaifin mu yake kwana nace a, a agida muke kwana tare dashi can mahaifin mu ya kusa dawowa gida daga asibiti sai ga anty sady ta kwankwasa gida na bude mata ta shigo. Nan ta zauna damu tana hira wanda ni hiran nata yayi min nauyi sosai amma haka muke ta hiran har barci ya dauke mu muka barta a zaune tana kallon tv. Can mahaifin mu ya dawo sai ya samu gida a bude da fushi ya shigo da zuman muna fada sai anty sady ya gani a zaune tana kallo munyi barci. Da mamaki yake kallon ta tace mashi sannu da zuwa ya mai jikin fa fuska daure yace da sauki don kallo daya yai mata ya kawar da kanshi gare ta saboda shegen kayan dake jikin ta rabin jikin ta duk a waje yake. Mikewa tayi ta dauko mai ruwa da abincin data girka ta aje a gaban shi yana zama ya dago yana kallon ta tana wani farr da idanu tana kada jikin ta ko ina rawa yakeyi. Wanan kuma daga ina ya tambaye ta tace nice na dafa don ka na dade ina son wanan daman da zan samu kebewa dakai in gwada maka irin yadda nake jinka a raina. Kina da hankali kuwa ya fada ta dago daga inda take zaune tazo inda yake cikin wani tako na yan iska tana kokarin ruguman shi. Cikin zafin rai ya dago ya wanka mata marin da sai data dafe kuncinta don zafi yace stupid idiout ki fice min daga gida banza kawai. Bata dadara ba ta kara yowa cikin shi zata kara rungumar shi tana fadin na kasa controling din kaina akanka ba komai naka nake bukata ba ka yarda dani kawai shine muradina. Mikewa yayi ya turata waje tare da wulgi da kayan abincin suka bare can ya rufo kofan gidan da karfi ya dawo yana mai sake tsuki. Ranan ta saka shi kwana a cikin bacin rai don har ya kwashe mu yakai mu dakin kwanan mu ya dawo ya kashe kayan wutan falon ya kwanta ranshi a bace yake. Da safe da muka tashi nayi gyaran falon mu da na saba yi duk safe kafin in wuce school ya hada muna breakfast da kanshi muka karya a gida muka je da wani. Mun dawo gida da yamma mun samu an sallamo su mama daga asibiti har ta gyara ko ina na gidan ya koma fes dashi badai tsabata ba a gurin mahaifiyar mu kan don bata son kazanta ko kadan. Wata makwaciyan mu ne ta shigo duba jikin baffa sun dan taba hira da mama a cikin hiran take fadawa mama tayi hankali da anty sady don bata yarda da ita ba. Don sun dawo cikin gari da mijin ta da dare sosai ta ganta ta fito gidan mu alhalin tasan mama din bata gida. Mama bata dauki wanan wani abu ba sai take ganin ai don dai mutuncin dake tsakanin su ne kawai yasa tazo gidan don duba yara. Kwana biyu sai ta dan lura baba baya son zancen anty sady sam ko ya dawo ya samay ta a gidan tana gaida shi baya amsa mata zai kama fushi har ta tsagu ta fita. Ranan ma haka ya kasance bayan fitanta muna falo dayaji firanta ya fito ya zauna a falon sai mama tace ban san abinda yasa kakewa matar nan haka ba yanzu idan ta shigo gidan nan. Wani tsawa ya daka mata tare da fadin ko ke idan baki fita harkanta ba sai na saba maki rai don ban son alakan ki da irin yan iskan matan nan don haka ki fita harkan ta. Kada in sake ganin takawo wani abu a gidan nan kin karba idan na ga haka zan saba maki sosai kinji na fada maki gaskiya. Baidai fito fili ya fada mata abinda ya faru a tsakanin su ba sai wanka da kamar jurwaye da yai mata kan anty sady kawai haka yasa mama shiga damuwa sosai a ranta yadda zata kakabe ta a jikin ta alhalin itace ke binta. Don gudun bacin ran mahaifin mu dole mama ta fara sakewa anty sady din ko ta shigo sai ta tsiri aikin karya da zai dauke mata hankali har ta gaji ta wuce don kanta. Da anty sady ta fahinci haka da kanta ta jaye a gidan sai dai can takan shigo jefi jefi neman wani abu ko tace tazo gaida mune. Shakaran mu biyu a madalla har mukai comman intrance na shiga secondary school na gama primary dina ke nan sai gaba zaman gida nake ban fita ko ina sai islamiya da muke zuwa wanda ke da dan nisa sosai da gidan mu. Ranan amaryan baba kabiru ta shigo abuja wurin yan uwanta sai gata a gidan mu muyi murna sosai da ganin ta itace ta farkon zuwa wurin mu a cikin yan uwan mu na gida. Kwanan ta biyu a wurin mu naji kamar kada ta wuce yarta ko yaushe tana gurina ina giyon ta ranan da zata tafi nayi kuka sosai da tafiyanta. Saboda ban raina abin kuka bayan tafiyan ta da kamar wata biyu na dawo daga islamiya na samu mama tana ta hada kayan mu da mamaki nake kallon ta ban hakkura ba na tambaye ta. Take fada min baba yace zamu tashi mu koma garki ne sai naji ba dadi a raina ko ina sai mun saba da mutane sai kuma mu tashi. Wurin tone tone nane na tono takardan da jamil ya bani da zan mu zo abuja din na dauka na bude karo na farko da kyat na iya karanta abinda ke cikin takardan wanda a lokacin na fara fahintar may yake nufi dani. Ranan haka na kwana karanta takardan a boye kada mahaifana su gani barci ne ya dauke da takardan a hannu na har baba