← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 27 OF 89

Sashe 27

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read

Dawowan su baba kabiru daga abuja muna ta jiran muji wani bayani sai mukaji sheru ba suyi muna bayanin komai ba ga hutun makaranta ya kare ana shirin komawa a lokacin. Hakan ne ya kara tayar muna da hankali so sai ganin bamu san mafitan mu ba a wanan lokacin zamu koma ko ba zamu koma abujan ba mu dai gamu nan dai ne. Baba kabiru ya shigo garin ya samay mu yake fadin mu shirya muzo birmi don a san abin yi a kan karatun mu. Da muka tashi zuwa tare muka zo da wanan yarinyar da umma taje muna abuja da ita don itama yanzu daukan kanta take a cikin mu take. Itama ta zama yar abuja a cewan ta don haka take abubuwa irin na yan birini sosai don abinda take mu ko makamancin sa bamu iya yi ai. Gidan babs kabiru muka sauka mu biyar daga mu sai yan kayan mu wanda a lokacin ba wani kaya bane masu kyau don sun sha jiki sosai a gurin mu. Dakin anty amaryan baba kabiru muka sauka don ta fi sakin fuska a gida don haka ne da zaran mun shigo gidan muke sauka a wurin ta. Yau ma kamar kullun mun iso suna ta faman tausaya muna kan abinda ya samay mu din na rashin mahaifin mu da mukayi mun danyi kukan mu mukai shiru bayan an gabatar muna da abunci muka dan taba. Nan muka hade da yaran baba kabiru don yanzu shima yaran nasa sun tasa suna secondry schools su ma. Kwanan mu uku a gidan muna jin dadin zaman garin duk da baikai abuja ba amma yanayin garin yai muna a lokacin don yanzu bamu da zabi a rayuwan mu sai yadda akayi damu. Da safe ne bayan anty amarya ta shirya zata fita aiki take tambayan mu ko yanzu aji nawa muke na fada mata ss2 zan shiga kanwata kuma zata shiga jss 2 ne. Batace damu komai ba tayi muna sallama suka fita da yaranta zuwa makaranta gidan ya koma daga mu sai kananun yaran su sai uwar gidan baba Kabir da bata aiki ita amma tana sana,an dinki da sauran su. Mun yi wanka kamar yadda ta umurce dayi don ka,idan gidan ne idan gari ya waye za a sa ruwa zafi kowa yayi wanka tun safe wanda mu bamu saba da hanka ba can sai bayan azahar ko la,asar muke wanka don haka muka saba dashi. Kallon tashan mbc muke a dakin baba kabiru ya shigo dakin yana fadin yau yake son ya kai kannen mu ai masu interview a makarantar da yake son ya saka su a nan. Mukai ta murna da jin dadin don dama shine damuwan mu don muna ganin ba wanda zai damu da karatun mu anan. Sai gashi kanin mahaifin mu uba a gare mu yanzu don mun fi daukan shi a matsayin uba duk cikin iyayyen mu tunda dashi muka bude ido mu ga iyayyen mu suna hurdan arziki sosai. Shamsiya ne tace wai ana nufin anan zamu zauna ke nan ni dai nafi son mu koma abuja da zama da son samu ne gaskiya. Sai summaiya tace gurin wa zamu koma Abujan da kike magana yanzu ina dai baba ne kuma ya rasu shima yanzu. Ina jin su ban iya magana ba a lokacin don irin yadda nake jin mutuwan mahaifan mu sabo a zuciyana. Zuwa rana sai ga anty ta dawo tace zasu kai kannen mu makarantane yasa muka dawo a lokacin. Makarantar da yafi kudi sukaje inda akaiwa yaran gwaji sai dai basu ci ba don sun ce sai dai idan zasu mayar dasu baya ne hakan ya batawa baba rai yabar gurin dasu zuwa wani makaranta again a can suka dauke su a ajin da suke makarantar shima yana da kyau sosai. Kannen mu suka fara zuwa makaranta a satin sai mu muka rage a gidan ga wanan yarinyar duk irin kokarin da baba da iyalin shi su keyi a kan mu bata gani sai kushewa take wanda har na fara yarda da hakan. Ranan baba yazo yace za a kaimu makarantar kwana na nan garin dani da summaiya kanwata ita kuma shamsiya zata tsaya day don mahaifinta yace bazai iya lalurar makarantar kwana ba akanta. Shiri sosai baba kabiru yayi muna da shi da matar shi mun shirya aka kaimu naso ganin jamil muyi sallama kafin mu tafi sai dai hakan bai samu ba. Makarantar akwai dalibai sosai a cikin sa sai dai yanayin karatun mune ya dan banbanta dasu a nan ba laifi don dama ina da kokari sosai sai haka yasa nake ganewa banda wani matsala karatu na a nan. Munyi sabbin kawaye da ma wa yanda muke da zumunci dasu duk mun hade a nan din a dan lokaci kadan sunana yayi fice a makarantar sosai don kokarin da nake dashi din. A wurin abinci duk makarantar babu mai nuna muna abinci don baba kabiru yafi ma mahaifin mu yi muna provition mai yawa haka ya kara samu sake jiki sosai muna karatun mu hankali kwance. Lokacin da muka samu hutu muka koma gida mun samu yan uwan mu a cikin kula da tarairaya suke sai dai dawowan mu shamsiya ta fara aikin zugamu wai mu gudu mu koma gida. Don mun cewa baba muna son zuwa kauye ya hanamu haka yasa ta oawo muna wanan shawaran na guduwa daga wirin shi mu koma gida. Har naso yarda sai summaiya kanwata ta ban shawara da cewa gara da ita iyayyen ta suna a raye idan mun gudu daga wurin wanda muka samu yana tallafa muna ina zamu tafi. Kin dai san ita iyayyen ta suna a raye bata da matsala muko fa wanan shawaran ya dawo da hankalina na daina sauraren ta gaba daya. Don aiki muna aiki kamar wanki da gyaran daki duk da anty bata bari muyi shi mu kadai tare da ita mukeyi wanda kusan wankin duk na mu ne dana yan uwan mu don ita yaran ta hudune kawai. Sai dai wanan ne shamsiya take ganin ai duk wahalan duniya yana a kan mu ne yake karewa wanda ni a lokacin kanwata summaiya tafini zafin nama a gurin aikin. Iya kata in gyara daki shinr aikina rayuwan da ba tare da mahaifan ka kake yin sa ba sai ya zamo duk abinda ake ma baka ganin kokarin mai shi sai zargi da tsangwama ya shigo ciki. Hakan ne ke faruwa don yan uwan mu idan su zo daga kauye sun kan kebe damu suna tambayan mu irin rayuwan da muke ciki a nan din. Bamu kan boye masu komai mukan fada masu duk irin kokarin da akeyi damu a nan din sai su juya maganan da ana cutar mu ne ana cin amanan mu don wai da kudin mahaifin mu ai ake muna komai da ake muna na rayuwa. Tun ban daukan wanan maganan a raina har maganan ya fara tasiri a zuciyana wani hutu mun dawo ne muka samu an kawo kayan lefen da mahaifin mu yakai kaduna wai yanzu kayan ya zama na magada. Don haka suka dawo wa yan uwan mahaifin mu da kayan sai da muka kwana biyu da dawowa ne aka fitar muna da kayan baba kabiru ya kasa muna aka cire lwa umma nata kason a cikin kayan don ita ma tana da gadon kayan. Kurciya ke damun mu a lokacin sai murna muke mun samu kayan banza baba kabiru ya biya kudin dinki aka shiga dinka muna kayan bai dauki komai ba a ciki. Sai matar sa anty ne muka cirewa turmi daya da man shafi daga ciki sauran mu muka dinka abin mu muna sakawa mu a dole ga yan mata a lokacin ba abinda ya damay mu. Hura ma baba kabiru wutan da mukayi akan muna son zuwa kauye muyi hutu ne yasa ya barmu muka tafi kauyen wanda ni da biyu na tafi don ina son ganin jamil a lokacin wanda yanzu tsakanin mu sai wasika don bamu amfani da waya. Wanan zuwa kauyen da mukayi ne aka fara zuga mu kan iyayyen namu yan uwan mahaifin mu dake kula da alamarin mu tankar iyayyen mu na raye. Don suna iyakar kokarin su damu a lokacin wani dan wan mahaifin mu ne da mahaifin shi ya riga namu rasuwa ya fara tun kara na da maganan. Yace bayan mun gaisa ashe kun zo garin nace eh mun zo shekaran jiya sai yake cewa wai yaya zancen dukiyan ku ne har yanzu shiru. Nace wallahi bamu san komai ba akai don su baba ne ke da maganan a hannun su yake fadin ba naji ance an sai da motar marigayi din ba da gidan shi na Abuja . Wanan gidan da Alhaji kabiru ke ginawa yanzu ance da dukiyan ku ne yake gina sa ai maganan ya bani mamaki kwarai ban gaskanta maganan ba sai da jamil yazo muna hira ya kara fito min da wanan zancen na yarda. A lokacin naso in tayar da hankalina sosai na kebe da yan uwana ina fada masu halin da ake ciki sai baffa kanina ke fadin shima yaji wanan zancen sai dai ba yadda zamuyi yajzu don mu din ai kanana ne ga maganan . Amma an bashi shawara idan lokaci yayi ai dole za a fitar muna da dukiyan mu ne don haka mu bar zancen har mu tasa tukun na . Da wanan shawaran muka bar maganan iya mu don summaiya kanwa ta cewa tayi dani wai da nake magana kan dukiyan mahaifin mu ni ban ganin irin kokarin da kanin mahaifin namu yake damu ne. Maganan ta ya ban haushi sosai nake fadin kin ji nace baya kokari da mune ko kin ji na fadi wani abu ne mara kyau akan zancen. Maganan yaso ya zama muna fada a tsakanin mu sai da na taushi zuciyana don kada wani yaji mu muna magana akan zancen ai muna wani fassara na daban. Wanda ni zancen dukiyan ba wai ya damay ni bane sosai don maganganun mutane ne a kai har zancen ya fara tasiri a raina yanzu. Munyi hutun mu lafiya mun dawo inda bamuyi wani dadewa ba muka fara shirin komawa makaranta. A daren da zamu koma ne baba kabiru ya kiramu
Chapter 27 · 0% Book details