← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 82 OF 89

Sashe 82

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 4 min read

kawai. Nakan tuna maganan anty da takan fadi kafi auren mu da cewa sun hada bakine su aure mu do sun ga akwai ci cikin al,amarin mu nan gaba. Gashi ko maganan nata yana zama gaskiya akan mu yanzu muna ganin ishara kala kala daga mazajen namu. Muda kan bamuji dadin aure ba ko kadan wallahi musanman ma ni dai baka saye kobo a gidan miji sai dai ga wata na wanan bai kan damay ni. Nidai bukatana shine mu zauna lafiya dashi hakana tunda naji na gani ga auren shi sai dai hakan bai samu ba gare ni tundai yanzu da yasan banda komai da zai kadar nawa. Sai zaman ya koma kamar na dole yake dani don inda sabo na saba da zaran yaga banda komai ya shiga min wulakanci ke nan kala kala a rayuwan mu ina shanyewa ni kadai. Babu wanda zan iya fadaw don zurfin cikine ko may ye ban sani ba do ban iya fadawa kowa halin da nake ciki dashi waini may rike sirin aurena . Haka ma yar uwata take bakajin zancen ta a gurin kowa garama nawa ana gani ana fadi tunda a garin nake zaune tare da yan uwa. Ita ko ba, a ganin ta ma balle a fadi sai ita ke gani tana shanyewa gara ita idan tazo tana zama da anty da ta yarda da ita su zauna ta fada mata matsalan ta ta sama mata mafita nan take na yadda zarayi. Niko ko nazo na fada yanzun anty zatace ba ruwanta inje in hakkuri ko an fada min zuwa zanyi in fada ma mijina ya kama masu rashin kunya. Raina kan baci idan tace haka dani har nazo na daina fadi don ba anty ba duk wanda nakaiwa kukana haka ake ce min kada mutum yace wani abu in kwashe in fadawa mijina. Ranan ina gida da rana ina wanki sai ga baba ya aiko yana nemana wani tsale na daka ina murna don nasan baba baya nema na a banza saida dalili mai karfi. Kafana kawai na wanke na jawo kofana zuwa gida tare da dan aiken muka koma gida wurin kira baba din da yake min. Aikuwa zancen kudin mu ne baba ya nemo ni nan yake min bayanin mutanen sun kirashi akwai wasu takarda da zamu saka hannu a cikin shi kwanan nan don haka in zauna a cikin shiri ke nan . Nafi kowa murnan zuwan wanan kudin duk da kowanan mu a matse yake kan zancen kudin nan dama a cikin mu. Sai dai ni nawa yafi na kowa don ga Amira ta isa shiga makaranta mahaifin ta yace shi sai priravert zai sakata bai kaita na gwanati. Har kaita babban wan mu yace zaiyi wani makaranta dake kusa damu na gwaunati amma ya hana hakan. Wai sai lokacin da ya samu kudi zai kaita makarantar kudi irin na yayan masu shi karya da burgan aiki irin nasa. Wai isan baka isa irin na dan tallaka daya dauki duniya da fadi kamar jamil sam shi baison yin abin kananan mutane. Bai gida ko da baba ya kirani sai da ya dawo nake fada mai kiran da baba yai min din har ya fara fada yana huci wai na fita ban fada mai ba. Saida nace akan kudin mu ne kuma ka bani baki ko baka nan idan an kiranika ace udn in tafi. Sai naji yace yanzu akan kudin ne suka neme ki nace eh baba yace sun kira kudin zasu iya samuwa ko wani lokaci. Sai naga ya kai zaune yana fadin saboda Allah yausje ke nan nace yadai ce zasu samu ko wani lokaci daga yau za a iya kiran mu. Nan fira ya kaure a tsakani mu duk akan kudin da zasu zo muna ya fara sabon tsare tsaren shi ina kallon shi harda tsuki yana fadin. Sai dai tsiyan kudin naku kuma sai anjawa mutane rai dashi kafin ya fito mm nace ba dai in ya fito ba za a mu samu. Sai bude baki yayi yana fadin na matsune kudin suzo wallahi don a uzurce nake dasu dama na rasa inda zan samu kudi wallahi ina da lalura mai karfi a gabana. Nace idan ma kasarai ga kudin nan gara ka fitar don wallahi dakina zan gyara da sana, a wanan karo ba zan bawa kowa ba gaskiya. Fadin hakan danayi ya kalle ni da mamaki tare da fadi haka kikace nace haka din ne ma wallahi don ni zaman nan haka ya ishe ni. Wasa wasa daga fadin haka ya fara daure mun fuska yana wani sham kanshi dani tun ma kudin basu iso ba gare mu ke nan.
Chapter 82 · 0% Book details