← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 31 OF 89

Sashe 31

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 4 min read

tsaya ga kudin kawai basu taba lafiyan shi ba sai dai ban yarda na nuna wani abinda zai kara tayar mashi da hankali ba a wanda yake ciki. Sai da dare muka samu kebewa dashi yake ban labarin abinda ya samay shi din inda hankalina yayi matukar tashi sosai na daiyi wa Allah godiya da ya dawo min dashi lafiya a lokacin. Satin shi daya sai gashi yazo min wai zai yi tafiya wani abokin baban shi yaji labarin abinda ya samay shi yace yazo ya taimaka mashi. Nayi murnan jin hakan sosai mukai sallama ya tafi akan washe gari zai tafi amsa kiran abokin mahaifin nasa a can birni. Abinda ban sani ba ashe kudina zai shiga birni yasha garalin shi dasu don abinda ya faru yana barin yankin kauyen mu da jarkokin daya dauka na sawo mai na bat da kama dayayi ya watsar dasu a hanya a cikin jeji. Ya shiga gari ya yi sayayan yadudukan shi na maza dasu takalma da sauran abin da yake da burin bukata a rayuwan shi. Sune ya koma ta karbi dinkunan shi ya karasa kashe kudin daya saura a hannun shi don rashin tausayi da imani da bai dashi. Nabi ruwa nabi iska na bi rana da sanyi na samo su rana daya jamil ya zo yaci amana ta ranan ko barci ban yi ba sai faman sakawa da kwancewa nake a raina. Ina kallon kayan sana,ata da dan abinda ya rage min a ciki wanda basu taka kara sin karya ba a lokacin wanan abin har zazzabin dole ya ja min sai da nayi jinya akan hakan. Bayan kamar sati uku ina dan bubugawa har tiren sana,an ya dan fara dagowa kaya ya fara samuwa min ga kuma kewan shi dake damuna a lokacin don tunda ya tafi ban samu labarin shi ba. Kwatsam sai gashi ya dawo garin kowa sai da ya girgiza da ganin canzawan da yayi a dan kankanin lokaci ya murje yayi kiba ga shiga ta alfarma da yakeyi kamar ba dan kauyen mu ba. Ban dai san inda umma taji rabarin ai nice na bashi kudin da yake karyan sun zube ba sai ji nayi tana fada tana fadin dama wanda baiji bari ba yaji hoho gashi yanzu ya fara nuna maki irin gidan su mayaudara. Na fada maki ki rabu da yaron nan ba dan arziki bane da yake ke mai taurin kan tsiya ne kika dauki kudi kika bashi ya shiga birni yasha garalin shi dashi. Yar nan kina arziki kuwa da wanan yaron da kika lakanta dama na fada maki ko mutuwa nayi sai na taso maku fatalwa idan kika ce wanan shegen yaron zaki nacewa. Yanzun dai ga magana ta nan ya fara fitowa fili ai ya yaudare ki ya raba ki da komai naki sai kamay kamay da ya barki kina yi a gari yanzu. Gabana ne ki faduwa don jin abinda umma take fada sai dai ni yace min abokin mahaifin shi ne ta bashi kudi ai yace ya sai kaya ya kuma koma karatu idan yana son ci gaba. Sai dai yaga ni banci gababa saboda shi ta yaya zai tafi ya barni a cikin wani hali ire iren dadin bakin da yai min ke nan lokacin daya dawo garin na gashi a cikin wadatan da ya dawo dashi. Na kasa hakkuri da dare daya zo sai dana fito mai da wanan maganan da umma tayi min ya dan yi shiru kafin ya hau fada yana fadin . Kai mutane basu son suga mutun ya samu karuwa yanzu, yazun kuma sherin da aka lakakamin ke nan shiyasa sai da na nunama baba sabo cewa ya bani kudin inzo in rage maki hasaran da mukayi. Amma ya nuna min ba haka ba yace in har kina sona tsakani da Allah aike ba zaki yarda da hakan ba a tsakanin mu. Jin wanan maganan ne yasa jikina yayi sanyi na kara yarda dashi hundred pacent naji ina son shi sosai a raina na watsar da maganan umma da na hau da farko. Yanzu bini bini Jamil sai yace yayi birni idan yaje sai ya share makonni a can yana sheke ayar shi kafin ya dawo gari duk wanan baisa naga laifin a raina ko kadan. Sai ma nake ganin na faso gari ai ina da saurayin da duk garin mu ba mai irin sa a garin kamar ni a yanzu mutane suna ganan min illar cutar da yake da buri a kaina wanda ni ban taba hango hakan ba. Gashi duk zuwan da zaiyi gurina sai ya fito min da zancen kudin mu na gado wanda ni ban kawo komai ga hakan sai ganin nuna damuwan shi ne da kulawa a kan mu yakeyi. Sannu a hankali mutanen dake ara min kudi ina bunkasa sana,a ta suka fara janye kudin su a gurina sai sana, an ya koma min gashi na yika nakeyi a yanzu. Ga kuma yan canjin da yake karbe min daga yace ya tashi bai da ko kobon da zai kashe sai ya kawo min wani lalura can ya aza min dole in lale kudin in bashi ya shige birni yaja garalin shi dasu.
Chapter 31 · 0% Book details