← Book details kanin Ajali Part 1 Complete Hausa Local reading mode
READING PART 68 OF 89

Sashe 68

kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 6 min read

Labarin baba kabir kuwa tunda ya bamu hakkin mu bai kara bi ta kan mu nasan don tsage rancin da muka nuna masu ne lokacin rabon kudin da Baffa yace wai dole ne sai an cire na mahaifiyar su .
Sai kuma wanda baba ke bi a ciki na fafitikan neman muna kudin ya fito da yake kai cin hanci da sauran su wurin duk wanda ya dace ayiwa.
Kuma gashi mun sani baiyi shi kadai sai da sanin mu idan za a yi don ko an lalubu mu kudin bamu dashi balle mu bayar din.
Dole haka aka fitar mai da abin shi duk da ma bai cire na jigilan shi ba yace ya yafe muna su amma duk da haka sai da dan hakin shi ya tsone muna ido.
Kada kukaga laifina masu karatu gama in kun tuna na fada maku sai da suka raba mu da kowa namu sai su mazajen namu da kannen mu biyu kawai muke shawaran mu.
Do haka komai sukace sai muga ai sunyi daidai ba ba mu ganin rashin dacewan hakan a gare mu tunda yanzu su zama muna uwa da uban mu a yadda suke fadi ko yaushe.
Don haka muka dauke su da zuciya daya ban ko tuna saura saki daya fa tsakani na da Jamil din duk da dai ban fadi a gidan mu ba kowa ya sani.
Dakina yanzu har zuwa kallo akeyi koda yaushe tv na aiki a falon yan diyana suna zaune suna kallo basu zuwa dakin kowa na gidan da sunan kallo.
Yanzu zamzam muke da Jamil baison ko kuda ya tabani ko diyana a gidan sai dai ban sani ba ashe har lokacin suna tare da Ruth farkan shi.
Ba wanda zai iya fada min don ban iya boye mutum wurin magana shiyasa kowa ke tsoron fada min gaskiya koda an gani sai a kyale ni gashi wanan kawar tawa sun tashi tabi mijin ta can kasa ibo inda yake.
Don da tana nan data fada min idan ta san da hakan ba zata boye min ba kamar yadda mutane suke boye min yanzu.
Duk da na gyara daki yanzu tsiyan daya tsiro min shine sai yace bai iya kwanciya a dakin wai zafi yayi yawa a daki waje shi zai fita ya kwanta.
Ashe in ya fita ya rufo mu ta baya wai kada barayi su shigo muna sai ya wuce gidan Ruth ya kwana sai asuba zai dawo gida idan yaga gari ya waye.
Duk ban san wanan ba na dai dauka yawan jin zafin shi ne yasa bai iya kwana a cikin gida ashe munafuki dawata manufa yake min hakan.
Ranan ko da na fito da dare sauro ya damay mu sai ban gashi ba wurin da yace yana kwanci din abin ya ban mamaki sosai a raina.
Da safe daya shigo nake tambayan shi ina ya kwana an dauke wuta bamu da maganin sauro na fito da dare ban ganshi ba.
Yace cikin dakewa ai wajen gida ya fita inda samarin unguwa ke kwanci da dare can yake kwana tare dasu sai ban kawo komai a raina ba danaji ya fadi hakan.
Ranan ina zaune na gama girki da rana sai ga matan yayan shi din nan sun shigo gurina na tare su tare da basu ruwa da abincin dana gama.
Sunci sun sha nake tambaya su ina suka fito suke ce min sun fito duba watace a cikin unguwan nan sai ban mai da hankali in san ko wacece suka zo gani ba .
Wai ashe guri Ruth suka zo duba bata da lafiya sai bayan kwana biyu nake ji a gurin wata yar unguwan mu wai ta gansu ranan sunzo gaida Ruth tayi fama da zazzabi.
Abin ya matukar bata mi rai naga yadda muke dasu wai ace sun zo duba farka miji na kuma gashi banda gidan zuwa sai nasu idan na tashi fita unguwa.
Ban kyale su ba har gidan su na samay su suna faman yi min rantse rantse wai ba can suka fito ba ban wani tsaya ba na dawo gida.
Wanan abin sai da ya hadamu fada da jamil yake cewa wai bakin kishi zai kashe ni idan banyi hankali ba nan dai muka kwasa dashi ranan sosai.
Sai banda wani damuwa yanzu sosai don ban gama turmuje yan kudaden dake hannu na ba lokacin don haka yake bina a sannu.
Mijin yar uwana ya samu aiki koyarwa a university da ke kano don haka ya tafi ya barta a nan inda take dan zuwa wurina tana debe min kewa a gidana.
Nan take fadin ba zata yarda ya barta a garin mu ba bin shi zatayi idan ya samu wuri banga laifin ta ba, da take fadin hakan lokacin don zaman mace kusa da miji yafi.
Sai dai ida bata samu anje da ita din ba tayi hakkuri zuwan shi biyu yana komawa inda suke daukan rikici dashi.
Har dai ya yarda zai tafi da ita bayan iyayyen sun sa baki a cikin maganan nan ta fara shiri sai dai bamu fada a gida ba duk shirin da takeyi sai daga baya muka je tare muka fada masu batun tafiyan nata.
Sun yi murna da farin ciki sosai don sam babu bakin ciki ga alamarin su damu sai nuna kulawa da kauna a gare mu.
Wanan abin wani lokaci yana samu jin kunya har da muka fito muke maganan nan dai take fada min wallahi inbi yan uwa in daina bin zancen Jamil da yan uwanshi.
Sosai taimin magana a cikin natsuwa yadda zan fahince ta na kuma fahinta da abinda take nufi don banyi sanyi a gwiwa ba na fara zuwa kai da kai ina ziyaran su.
Tun kan Summaiya ta bar garin sai dai wani abu daya bata muna lamarin shine ita kanta summaiya tayi abinda har ni ya bata min rai da ita sosai.
Don kaya dakin ta gaba daya har kujerun da muka canza ta sayar ba tare da ta fadi a gida ba bayan munce gyara muke son yi a gurin baba kabiru da iyalan shi.
Don sun muna komai da akeyi a duniya nan gaskiya wanan abin da tayi ya bata ran mutanen gidan baba kabiru din sosai don ta fifita uwar mijin ta gare su.
Kayan dakin nata ma karshe akace uwar mijin nata ke amfani dashi kin san abu ga mai kishiyoyi su suka kwarmata ma gidan mu wanan zancen.
Ba yadda zasuyi damu dole sukai hakkuri suka bar zancen duk ko da ransu ya baci ga hakan da tayi masu din don sun fahinci dai bamu dauke su a maysayi iyayyen mu ba.
Mun fi fifita mazan mu a kan su dole kowa yanzu ya kawo ido yasa muna aga iya gudun mu da mazajen namu da muka dauka uwa uba a gare mu.
Sai bayan wucewan su magana ya fara tashi wai da kudin ta mijin ta ya nemi aikun daya samu wai wanan kangon da muka saye babu nata a halin yanzu.
Waya na nema na kirata na fara mata korafi sai bata bari nakai ayya ba ta hau fada tana fadin wai ni a ina naji wana zancen wanan magana ba gaskiya bane duk wanda ya fada mun kuwa.
Haka dai magana ke faman yawo kan mazajen mu sun cinye muna kudaden mu duk wanan maganan da ake fada baba kabiru baice damu kala ba kan zancen mazajen namu.
Kuma ya hana iyali shi suyi muna magana don haka ne zancen bai daga sosai ba yadda wasu suka so cikin dangi a dauki mataki akan mu.
Yakan ce kubar yaran nan inda kuka gansu idan masara taji wuta da kanta zatai kara ai ba sai an tambaye su ba duniyace.
Don yanzu ana magana zasu ce kuna son ku kashe masu aure ne don baku kuka haifesu ba sai yan uwa suce kwarai kuwa Alhaji kabiru.
Chapter 68 · 0% Book details