Sashe 79
kanin Ajali Part 1 Complete Hausa · about 8 min read
ZAINAB IDRIS MAKAWA SEENABU 5/18/21, 11:57 PM - 🤔🤔🤔: Yau da gabe muna zaman jiran kudin mu kin san yadda alamarin kudin suke yau zamu gansu gobe zasu fito shiru har wata uku da maganan da baba kabir yayi min yanzu babu labarin kudi. Ga bubuwa sun taru sun min yawa a kaina zuwa yanzun duk da Jamil din bai faye zama damu a gari ba yanzu. Sai yaje ya share wata uku hudu har shidda yanayi ba tare da mu ba a can na ramay nayi baki na lalace babu mai taimaka min a cikin dangina . Baba kabiru ne yanzu shima yana fama da kanshi baida karfi irin na da can baya da zai taimakamin dashi. Sai dai duk da halin da yake ciki ina dan samun kyautan dari biyar dubu daya idan Allah ya ciyar dani daga gareshi. A cikin rashin nan da yake fama yake kokarin ganin ya kwato muna hakkin mu da ya saura muna bin gwaunati a yanzu. Duk wani kokari don ganin kudin sun fito baba kabiru yana bin hakan da karfin shi da arzikon shi don dai ya sauke nauyin da dan uwanshi ya barshi a duniya. Wanan karon kan huduban Jamil a gurin mu bai samu karbuwa ba kamar yadda ya saba yi muna idan kudi zasu fito ya shiga hada muna meeting kenan da fada muna abinda zamuyi. Sai ya kasance wanan karo ba fuska a gurin kanne na ga baki daya nice zai samu ni din ma idan ya tambaya nakan ce dashi ban san komai ba har yanzu sai dai idan an kiramu din. Hakan bai mashi dadi a ranshi sai dai kuma baiyi fushi da zancen ba don yasan zai samu idan sun fito din nan gaba yasa bai fasa tuntuba na ba. A cikin hakan da muke ne yayi tafiya a cewar shi yake fadin ba zai dade ba idan ya tafi din sai bayan ya tafi ne na samu labarin da ya girgiza min rayuwana a gamay dashi. Don ba komai naji ba sai zancen zaman shi da wanan matar da suke zaman da ban san fassaran shi a gurina ba yanzu. Don wanda ya fada min din mijin wata yar uwatace ta jini shi driver motace da ake ma lakani da kanta na daukan kaya shima sun kai kaya garjn ne yaga jamil a can din. Sai dai yana ganin shi yace don Allah ya rufa mai asiri kada ya fada a gida ya ganshi a garin sai dai ya ki fadin yanayin daya ganshi a can din kawai ya furta Jamil mayaudari ne na kwarai. Kowa yasa halin da Jamil ke ciki da wata acan sai dai an rasa wanda zai iya fada min gaskiya a cikin su. Haka muka tafi da rayuwa ina shan bakar wahala a gidan aure na banda tsayayen da zai tsaya min tsaye kan alamarin. Ba komai ne ya jawo min haka ba sai sanin halina da kowa yayi na rashin fahintan da banda shi da kwanciyan hankali yasa kowa ya fita batuna yanzu. Don mutum zai iya zuwa mi da magana ba zan bari ya tadhi ba sai na bata mashi rai ina ganin kowa baiso zamana da Jamil din ne don suna kallo shi a mayaudari. Ni ko hakan na min haushi a raina sosai don may yan uwa zasu saka min miji a gaba da hattara da tsangwama shi kadai haka. Ni dai ko yaya yake tunda bai kini ba ina son abina hakana a wautana hakan shine zaman lafiyan da zamu dore a tare da yan diyan mu mu kadai. Ashe abin ba haka yake ba yadda kake so da wuya ka samu hakan a wuri namiji ban taba kawo wai zai iya kara aure ko hadani da wata ba a rayuwan mu. Sam bani wanan tunanen a raina ko kadan don gani nake haka zamu tabbata dani dashi sai yan diyan mu ba zai kara kallon wata mace ba, da sunan aure har kuma harsu haihu ma. Na mance da abinda sharia ya dorawa maza kan tara iyali rashin shiga mutane ya cutar dani sanin halin rayuwa na yauda kullun dake gudana ga al,umma yanzu. Ko gidan mu zan iya share watanni ban lekasu ba duk da kamar a unguwa daya muke zaune dasu ban damu da kowa ba suma basu damu dani ba tunda sunyi lurar dani ban fahinta ba. Idan do ta anty ce tu farko da ban auri Jamil ba don ta fada kuma ya tabbata hakan da ta fada gamay da mazajen namu. Rashin karfi ga al,amarin namu da bata dashi ne yasa ta saka muna ido kamar yadda kowa ke kallon mu yanzu kara zube don nakasa da muke dashi bamu daukan kowa a matsayin shi. Mu dai mazajen mu sune uwa uban mu da muka dogara dasu muke gani zasu tsaya muna ga komai duk mun ture kowa ga al,amarin mu har kanina Baffa haka baijin maganan kowa daga iyayyen mu din. Autan mu karamin mu ya kama dangin anty sosai ya mayar dasu yan uwan shi na jini suma haka yana zuwa gurin yan uwanta kamar dan ta haifa da cikin ta ya koma. Baka taba jin zancen shi kudin shi ma yana hannun baffa ko kwandala zai cire sai da yardan baffa din don tsamay kowa da mukayi cikin al,amarin mu. Suma din ido suka sa muna tunda sun gane muna zargin su da dukiyan mu da muke ganin ya ishemu rayuwan duniya ba mai yarda ya rabe mu muce abin mu yake so yaci. Duk da nasan ba kudin nake da shi ba bai sa na bi yan uwana na jini yadda ya kamata ba ina ganin duk basu son mu sai diyan su suke so kawai. Wanan ya kara ja muna bakin jini a cikin dangi ko ance abina ya tashi zakaga ana ja da baya ba mai kullawa sosai sai yan gidan baba kabir dana zama ma kamar dole su. Babu yadda zasuyi dani haka yaran su sune masu lekani jefi jefi don sun mafi zuwa wirina akan yar uwarsu don haka kuma idan sun zo zan saka su aiki ko in aike su suje min ko na tambaye su kudi su bani idan suna dashi duk da kanana ne sosai kuwa. Jamil ya dawo inda ya kwatanci biyan kudin yan hayan gidan mu yayi a lokacin ya dawo yasa su a gaba sai da suka bashi ba tare da sani na ba. Sai bayan ya karba ne yake fada min sun bashi kudin ya karba nan na nuna mashi kuskuren taba kudin da yake son yi don ba ni kadai keda kudin ba ya sani. Nan ya hau fada yana fadin ko bani kadai bane ai nike wahala da gidan da sauran su da dai naga yaki yarda da maganana na kawo ido na saka mai da kudin yayi yadda yake so dasu. Ba a sati biyu ba da ya karbi kidin sai ga kira daga wurin kanina Baffa yana tambayana lokacin biyan kudin yan hayan mu yayi fa. Nace sun biya sati biyu daya wuce ko yace kudin suna ina nayi shiru ba abinda zance dashi lokacin don ko banda su a gurina. Nan ya shiga fada sai abinda ya fito a bakin shi dadai naga fadan yayi yawa ne nake fada mai gaskiyan wanda ya karbi kudin bani bace. Nan ya kara hawa yana fada sosai yace ba zasu yarda ba dole in biya wanan kudin idan kudina sunzo na dauka wasa yake sai daga baya na ga da gaskiya yake maganan shi. Shiko gogan da ya shigo na fada mai sa tsaki yaja tare da fadin baida hankali shi yasan wahalan da akeyine kafin su biya kudin da zai fadi hakan. Bajima ba ya tattara ya koma dama kudin ya kawo shi garin ya karba kuma mai zai zauna yi kuma duk wanan tafiyan da yake da sunan yana zuwa neman kudi ne yake yin shi . Muna nan a haka kira yazo min daga wurin baba ban tafi ba na daga yar wayan da kanina dan wirin anty ya saya min nokia . Kafin ya saya min wayan sai da nasha kwakwazo kada in sayar da wayan nan don ba zai kara saya min ba idan na sayar yace. Shina samu ina amfani dashi don wayan yana min rana sosai yanzu na kira Jamil dashi ina fada mai baba na nema zan tafi. Yace lafiya ko nace dashi sai dai idan naje zanji abin da ake nemana dashi din yace sai na dawo zai kira na kashe wayan. Na samu baba a gida bai fita ba baya mun gaisa ne yake fada min mutanen nan sun kirashi zamu shiga sokoto ranan talata sgabiyu ga wata ke nan don haka in shirya tafiya don asuban ci zamuyi . Ina hanyan komawa gidana ne jamil din ya kirani yana tambayana idan naje nake fada mai abinda baba din yace dani a gamay da kiran da yayi min din. Yace okay kawai ya kashe wayan washe gari sai ganin shi nayi kwatsam ya fado min daki nayi mamakin ganin shi don bai sanar dani yana tafe ba a lokacin. Tafiyan dagani sai baba zamuyi shi don haka jamil din ya hau bakin shi da fadin in kula in sa ido idan muje don in gane abinda ke gudana acan. Yake fadin tafiyan da ake dani da Baffa yanzu don may za a cire shi idan ba wani manufa a cikin tafiyan kuma yanzu. Wanan maganan da Jamil yayi ya sake tunzura sauran yan uwana suka fara kananin magana kamar yadda Jamil din ke son yaga ya samu kan mu yana juyawa a hannun shi sai yadda yayi damu. Abin mamaki sai kuma gashi mun koma hannun Jamil din don muna gama waya dashi washe gari kwatsam sai gashi ya fado min da safe . Babu ko kunya don jin zamu samu kudi jamil din ya dawo gari babu shiri nan ya fara kule kule a tsakanin mu duk da rashin bashi fuska da basuyi sosai kamar farko. Yanzun dai ya samu yadda yake so haka yasa ya share wuri ya zauna yana jiran tsamani don baba yace kila da munje ance kudin zai fito ba da dadewa ba insha Allahu.