← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 111

Sashe 95

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gaida ummy yayi cikin girmamawa yana dora kanshi kan kafadarta

Shafa kanshi tayi tana amsawa tana tambayarshi ya gajiyar jiya

Amarairaice yake amsamata da alhamdullilah

Maganar breakfast tayi mashi yace A'a zaiyi acan yanzu sauri yake

Haka yatashi sukayi sallama da ummy yana qara satar kallon saudart da batasan wainar da akeyi ba ya fita

Abakin kofa yaci karo da baby itama zata shigo

Gaidashi tayi ya amsa yayi gaba

Binshi tayi saurin yi tana fadin
"Please yaya inzo ka ragemin hanya?"

Banza yayi daita kamar bazai amsaba saikuma yace
"Don't waste my time"

Da sauri tajuya tashiga dakin ummy tayimata sallama a tsaitsaye ta fito tana gyara zaman jakkarta dake dauke da few books ta sauka da sauri gudun karya wuce yabarta

A parking space ta ganshi yana niyyar shiga mota hakan yasata saurin qarasowa itama ta bude dayan side din ta shiga ya kunna motar yaja suka fice daga gidan

Sai wajajen 9:30 saudart ta tashi barcin da ummy tasata dole takoma

Dama tana gama sallah da azkar dinta ta tashi zata gyara dakin ummy tasata takoma ta kwanta ganin haryanzu komai sukuku take yinshi kamar marar lakka

Tana kwanciya ba dadewa wani barci mai shegen dadi yayi gaba daita kasancewar dama jiya bawani barcin kirki tayiba

Batafi minti 15 da barci ba ashraf shikuma yashigo

Addu'ar tashi ta karanto tana yaye bargon jikinta

Dumm gabanta ya bada jin qamshin da mutum daya tasani dashi waige waige tashigayi a dakin kafin ta sauko qasa tana qara shaqar qamshin

Tabbas qamshinshi ne, hakan na nufin yashigo dakin? When?

Bude kofar da akayi yasata dagowa ta kalli saitin kofar

Ummy ce tashigo cikin fara'a tana cewa
"Daughter kin tashi? Ya jikin?"

Murmushi tayi tana cewa
"Da sauki ummy"

"To masha Allah, maza kiyi brush ki sauko ki karya"

Da to ta amsa tashige toilet domin yin yadda ummin tace

Koda ta sauko har an ajiye mata abincin, abakin maid dinsu takejin baby ta tafi makaranta tarema suka fita da Ashraf

Sosai ranta ya dagule fiyeda jiya ma, jitake komai yabar mata dadi, jitake kamar ta shekara bata ganshi, she's missing everything about him

Yauma haka ta wuni sukuku saidai she's trying her best wajen nunama ummy she's normal don sosai ummy ke nuna damuwarta akanta.

Wajajen two baby tadawo gidan hakan yasa tadanji sauqi sauqi saboda surutu da ban dariyar baby yadan rage mata damuwarta

*6:15pm*

Saukowa tayi daga sama hannunta riqe da qaramin bowl data gama shan farfesun cow leg da ummy tabata wanda yaji kayan qamshi da maggunguna masu inganci

Shiga tayi kitchen ta dauraye bowl din ta maidashi ma'ajinshi sannan tafito daga kitchen din tana dan yarfe hannayenta

Cak ta tsaya da abinda take tana kallonshi zuciyarta na chanza bugu

Ashraf da dawowarshi kenan yana zaune akan kujera ya duqa yana zare socks din kafarshi ya dago shima idanunsu suka gauraya

Kasa janye idanunta tayi akanshi tacigaba da kallonshi wani emotional feeling na tasomata daga Chan qasan zuciyarta

Shima hakan take agareshi, kafeta yayi da idanunshi kamar zaiyi devouring dinta yana sake jin kewarta acikin zuciyarshi

Sun kai kusan two minutes suna kallon juna kafin ashraf ya tashi ahankali ya nufota

Kallonshi tacigaba dayi idanunta na kawo kwallar da batasan dalilinta ba harya qaraso gabanta

Sai a lokacin ta sauke idanunsu qasa wanda yayi daidai da digar hawayen idanunta

Dago ha6arta yayi yana kallon fuskarta hakan yasata saurin lumshe idanunta wanda hakan yaba sauran hawayen damar gangarowa

Da mammaki yake kallonta don besan dalilin wadannan hawayen ba

"Saudart..."

Saurin juyamashi baya tayi gabanta na bugawa sosai yayinda hawayen ta yaqi tsayawa

Ganin haka yasashi zagayowa ta gabanta yasake fuskantarta

Saurin rufe fuskarta tayi da tafukan hannu don batason yaga hawayen gashi ita ta kasa tsaidasu

Shiru yayi yana kallonta na wani lokaci kafin yace
"Saudart.."

Nanma shiru kuma bata sauke hannunta ba daga kan fuskar

"Are you still angry?" Ya tambayeta a tausashe

Nanma bata motsaba saima qara gudu da hawayenta sukayi

"Am sorry uhm? I don't mean to scared you" yafada almost in wishper

Nanma batace komaiba

"Please open your face"yasake fada amma bata bude ba

"Are you still angry?" Yasake tambayarta cikin damuwa

Shiru tayi bata kuma janye hannun daga fuskarta ba

"My presence is irritating you ko? Intafi?" Yaqara tambayarta cikin sanyi

Samun kanta tayi da girgiza mashi kai ahankali

"Then ki bude fuskarki please" yafada yana janye hannunta hakan yasa tayi saurin Zamewa ta zauna qasa tana cusa fuskarta a tsakankanin qaffafunta

Murmushi ya su6uce mashi shima yabita qasan ya zauna yana kallonta na wasu daqiqu yace
"Wai 6oye fuskar dikna menene?"

Banza tayi dashi takuma qi dagowa

Murmushi yasake saki sannan ya matso da fuskarshi dab da tata yace
"Did you miss me too?"

Sai a sannan ta dago fuska sha6e2 da hawaye ta gallamashi harara ta maida fuskar a inda ta dagota

Dariya sosai tabashi hakan yasashi yin kayanshi

Sake dagowa tayi ta kalleshi ta 6ata fuska ganin yadda yake mata Dariya

Yunqurawa tayi zata tashi yayi saurin kama hannunta yana Dariya yace
"It ok, it ok na daina" yafada yana dan toshe baki da dayan hannun fuskarshi dauke da murmushi

Dan kawar da kai tayi tana dan murmushi, aabin mammaki jitayi zuciyarta wasai babu digon damuwa ko kadan saima farincikin daya maye gurbinshi

Tankwashe kaffafu yayi ya buga tagumi da hannu bibbiyu yace
"Now tell me, wadannan hawayen na menene?"

Harara taqara gallamashi tana saka bayan hannu tana goge fuskar

Wani white handkerchief yafiddo daga aljihunshi yabata

Saida tadago ta kalleshi sannan ta amsa ta ida goge fuskar tanayi tana shaqar qamshin handkerchief din

"Inaji, why those tears?" Yasake tambaya yana kallonta

Qin dagowa tayi bare tabashi amsa

"Oho? Nagane, saboda Karna tambayi coffee Dina ko? Hard luck👎🏻 don wannan bazai ceceki ba"

Qara dagowa tayi ta dan harareshi

"That also won't save you miss emoji, I'll make sure you learn a lesson"

Sinne kai tayi tana Dariya marar sauti jin yace mata miss emoji

Qara kusanto da fuskarshi yayi da nata yace
"Yanzu gayamin, did you miss me?"

Dagowa tayi ta kalleshi tadan yamutse fuska tace
"No?" Kamar a sigar tambaya

Wara idanu yayi harda dan bude baki yace
"Really?"

"Ni kau kinga you're sticked to my brain, ina aiki amma ke nake hange, because of you saida nayi mistakes dayawa wanda saboda cancelling da retyping kalli yadda yatsuna sukayi swelling ga wancan annoying fringe daya tasani gaba da ban haushi, Abu ya hademin goma da ishirin kamar inyi hauka shine zaki ce bakiyi missing dinaba nima? Kai amma kin gama dani" yaqarashe zancen yana dafe Kai🤦🏻‍♂️

Dariya yabata sosai hakan yasata sadda kai tanayi ahankali ga wani farinciki dake sake lullu6e zuciyarta

Zai sake magana yaji gyaran murya a bayanshi hakan yasasu juyowa gabadaya

Baby ce tsaye tadan Sosa qeya tace
"Erm... Dama ummy tace na gayamuku Ku tashi kuyi sallah"

Waro idanu saudart tayi tayi saurin miqewa tsaye don ita tama manta inda suke saboda shagala

Shima miqewa yayi yana kallon wristwatch din hannunshi yaga bakwai da kusan rabi, tuni aka gama magrib sai batun isha'i kuma

Saurin bin bayan baby da tuni tayi gaba Dariya fall cikinta tayi yayinda shikuma yabita da kallo

Saida takai bakin stairs zata taka saikuma tajuyo

Hada idanu sukayi ya kashe mata ido daya, saurin juyawa tayi ta haurawarta tana smiling itama

Saida ta 6acema ganinshi sannan ya kauda kai yana murmushi hadi da shafa kanshi

Zira takalminshi yayi yafice shima yanufi part dinshi dauke da murmushi a fuska...✍️

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖

098

Koda saudart ta haye saman kasa shiga dakin ummy tayi, tayaya zata iya facing din ummy? Wataqila ma ta gansu

Ta dade a bakin kofar tana shawarar shiga, ganin dai bata iyawa din yasata chanza akalarta zuwa dakin baby

Jin an bude kofa yasa baby dagowa tana kallon kofar

Tana ganin itace ta fashe da Dariya tana toshe baki

Ko gefenta saudart bata Kalla ba tanufi toilet

Alwala ta dauro tadawo ta zari hijab cikin wardrobe tahau sallayar da baby ta shimfida mata ta kabbara sallah

Koda ta ida har wasu massallatan sun fara isha'i don haka itama tashi tayi ta jona da ita

*DINNER*

zaune suke su uku suna cin abincin dare in silent

Tun saudart na dari dari da ummy harta dan saki jiki ganin ummy bata wani nunamata komai ba

Abincin takeci saidai rabin hankalinta naga kofar shigowa, she's wondering why haryanzu be shigo yin dinner ba

Haka kawai saita samu kanta da damuwa da hakan tanajin abincin ma na fita kanta

Sunyi nisa acin abincin taji screeching din handle din kofa hakan yasata saurin dagowa tana kallon saitin

Bayyanarshi yasata jin wani sanyi na ratsa zuciyarta yana maye gurbin damuwarta

Janye idanunta tayi cikin jin kunyar kamata dayayi tana kallonshi ta maida kan abincin ta tana tsakura

Da sallama yashigo dining area din ya chanza shiga zuwa blue three quarter da farar T-shirt

Duk amsa mashi sallamarshi sukayi yaja kujerar dake facing din saudart ya zauna yana kallonta ta qasan ido

Baby ce ta gaidashi ya amsa yana janye idanunshi daga kanta sannan ya dago ya kalli ummy yana gaidata

Amsawa itama tayi agajarce tana cigaba da cin abincinta

Dago idanu tayi da niyyar Satan kallonshi sai kawai suka fada cikin nashi kasancewar dama ita yake kallo

Kashe Mata ido yayi kamar yadda yasaba idan suka hada ido

Janye idanunta tayi dan murmushi na su6uce mata itama ta gaidashi asanyaye

Amsawa yayi in joy sannan yasa hannu ya janye plate din abincinta ya maido gabanshi yahau ci batareda ya damu da kallon reaction dinta ba

Dagowa tayi ta kalleshi tana 6ata fuska ganin beko dagoba bare yasan tanayi ba yasa tadan saci kallon ummy taga ita abincinta ma takeci da alama ma batasan abinda sukeba

Hakan yasata satar kallon baby itama, kashe mata ido baby tayi tana sunkuyar dakai don 6oye dariyarta

Janye idanunta tayi daga kanta ta zari wani plate din taqara serving kanta wani abincin

Gamawarta keda wiya taga anqara janye plate din an turomata wancan na dazu wanda yanzu babu komai ciki don dama abincin ciki bawani mai yawa bane

Sagale tayi tana kallon plate din leftover din sannan ta dago ta kalleshi
Chapter 95 · 0% Book details