← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 111

Sashe 43

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushin yaqe yayi mata yana cewa
"Yes miss, da dai sauqi za'ace" inji sadeeq yana Satan kallon Ashraf

"What happened?" Inji saudart

Zai bude baki yayi magana Ashraf ya katseshi da.

"Look keep quiet my friend! Me zaka gayamata Wanda batasaniba? A matsayinta na secretary na ita wannan labarin zai fara riska kafin kowa, so meye na pretending? Kifito fili ki nuna Farincikin dakike aciki mallama, dama abinda kikeso kenan, my downfall, now kinsani, go and celebrate"

"Ashraf..."

"Kaga kyaleni mallam, don't Ashraf me ok? Ba gaskiya bane? Eh! Ki gayamin baki tsaneni ba? Da bakin ki kika fada, kullum kina cikin addu'ar taggayyarata kuma gashi Allah ya amsa, sai kiyita murna, keda kwaddayayyen babbanki, now leave! Kibarmin office dina! Get out of my life!" Yafada cikin qaraji.

Daskarewa saudart tayi inda take zaune.
Tarasa inda maganar shi ta dosa, sosai kanta ya kulle.

"Haba Ashraf? This is wrong..."

"Look mallam ban kasa dakai ba ok? Kacemata tafita before I do something stupid, taje ta gayawa Shamsu tau burinshi yacika!, kufita dukanku!!" Yafada kamar wani sabon kamu.

Saurin miqewa tayi ta dufi hanyar waje cikin sassarfa.

"Damn you!" Sadeeq ya fadawa Ashraf cikin fushi sannan ya maramata baya.

A office ya taddata ta juyama kofa baya.

Shigowa yayi da sallama Wanda hakan yasata saurin goge hawayenta da bayan hannu.

"Miss saudart dan Allah kiyi hqr..."

"It ok" tafada tana juyowa ta kalleshi da idanunta dasuka farayin ja

"Miss saudart wlh baya cikin hankalinshi ne, he's in shock, dazu takarda yazo mana cewa..."

"Jirgin gwalagwalai yayi collapsing ko?" Ta katseshi da hakan

Kallon mammaki yayimata sannan yace

"Kinji labari kenan?"

Jan hanci tayi ahankali sannan tace

"Eh nasani, tun kafin mubaro Spain, nasan jirgin zaiyi collapsing" tafada tana kallon yadda ya Waro idanu cikin kidima.

"W...what! Tayaya? Kardai dasa hannunki aciki?" Ya tambaya bakinshi na 6ari

Murmushi saudart tayi sannan ta fiddo wayarta ta kunna wani video ta miqamashi

Amsa yayi yafara kallo .

Da farko magana kawai yakeji be ganin mutanen sannan daga baya fuskarsu ta bayyana.

Wadannan mutanen ne uku dasukayi meeting dasu a Spain tsaye suna magana akan yadda zasu tsara yadda jirgin zai kife a ruwan shi yadda baza'a zargi wani Abu ba Wanda a zahiri jirgin dauke yake da gwalagwalai na bogi.

Sannan suka tsara yadda zasuyi kason abinda suka samu idan komai yatafi daidai, duk wannan abin da turanci suke magana.

Zufa sadeeq keyi takoina har saida yagama kallon video din sannan ya dago yana kallon saudart totally speechless.

Itama shi take kallo, ganin kallon dayake mata Yama kasa magana yasata cewa

"Ni nayi video din.... Ranar bayan meeting din mun fito muna tafiya sai igiyoyin takalmi na suka since, shine na aza purse dina a wani dakali da duqa na daure... Cikin ikon Allah saina manta da purse din nafita saida zan shiga mota natuna nadawo domin dauka.
Harna dauka zan wuce naji maganar su saikuma naji ya danganci meeting din damuke saina kasa kunne.

Ahaka suka fito daga office din suna maganar cikin turanci don da alama baqin cikinsu bejin Spanish, jin abinda suke fada yasani shiga firgici, narasa yadda zanyi saina la6e ina sauraron su, anan idea ta fadomin na dayi recording, da voice naso nayi sainaga Gwara video tunda fuskarsu is showing clearly, hannuna na 6ari nafiddo wayata na dauke su har suka gama tattaunawarsu suka shige dayan office din"

Dagowa tayi tana kallon sadeeq daya tsuramata idanu kamar T.v

"Haka nafito rai a jagule, naso nafadama A.A saikuma nakasa, firstly at that time ya 6atamin rai ina fushi dashi, secondly dukda wannan ya isa hujja gani nake be cika hujjaba Gwara nabi a sannu inta bibbiyarsu insamu enough evidence"

"Muna cikin mota yafadamin jibi zamu koma Nigeria, hakan yasani cikin rudani sosai don sonike in bincikesu sosai, haka na kwana ranar ina tunanin mafita"

"Washegari mukaje shopping din tafiya dawasu qawayena biyu, daya mai suna Loveth masanar computer ce sosai, kamar wasa na tambayeta ta iya hacking din account din mutum tace eh, nace ta koyamin tace zata koyamin amma saina fadamata dalilin hakan, dafarko naqiya saikuma daga baya na gayamata, jin hakan yasata taimakamani nayi hacking din account din zahid, ya kasance duk abinda suka turamashi duk ina gani.... Gasunan"

Tafada tana Ciro wasu takardu a Jakarta ta miqa mashi.

Hannu na 6ari ya amsa yana dubawa.

Waro idanu yayi don komai na ciki, yadda suka hada komai.

Koda takardun kadai sukayi amfani saisun dauresu bare uwa uba ga video.

Dagowa yayi yana kallon saudart dake kallonshi itama, sai 6ari bakinshi yake yakasa magana

Murmushi tasaki sannan tace

"Wannan ya isheku Ku dauresu, aciki idan ka duba sosai zakuga ba akanku suka faraba, sun yaudari mutane da Dana ta wannan hanyar, go ahead a sue them, best of luck" tafada tana fita daga office din tabarshi nan tsaye yakasa ko motsi...✍

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

Gaskiya naji dadin comments dinku na page daya gabata, sai jiya nasan AUREN KWANGILA Nada masoya dayawa.

Jinjina gareku members din
*AUREN KWANGILA NOVEL GROUP*

*OFFICIAL MARCY NOVEL FANS*

*HOME OF HAUSA NOVELS*

*MATAR BAHAUSHE NOVEL FANS*

*FAUZZIYA D SULEIMAN NOVEL GROUP*

*KANO NOVELS*

duk naga comments dinku da fatan alhairi da addu'o'inku gareni, ina godiya sisters🙏 Allah yabar zumunci🤝

Masu qorafin short page suyi haquri, yanzu ban zama sosai, dakyar nakesamu nayi muku wannan dasafe kafin na fita, nima na qagara Nagama littafin, dama aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, please bear with me, mutafi ahakan har insamu kaina, ngd da qaunar Ku agareni💝💝💝

054

Saida yaji Qarar rufewar kofa sannan yadawo hayyacinshi.

A tamanin shima yafito office din amma sai gani yayi elevator din na rufewa daita aciki

"Miss saudart!" Yafada da qarfi yana nufarta amma har yagama rufewa.

"Shit!" Yafada yana nufan private elevator din Ashraf don cimmata.

Hannu na rawa ya Danna last floor yashiga.

Jiyayi kamar elevator din baya Gudu don jiyake kamar yafita yabi ta mattatakalai.

Finally elevator din yatsaya a last floor, tun kafin yagama budewa ya ra6a ta gefe yafita yayi waje dagudu.

Tayaya zaibari ta tafi bayan wannan abun datayi musu Wanda bazasu iya sakamata da komaiba.

Fitowa yayi a harabar company din yana wurge wurgen idanu don ganinta.

Can parking space yaganta tana qoqarin bude motarta.

A sittin ya nufi wajen yana kiran sunanta, tana jinshi tayi banza dashi ta bude motar tashiga, ta ziro hannu don maido kofar motar taji an riqe kofar gamm.

Dagowa tayi tana kallonshi da alamun tambaya batareda tayi magana ba.

"Miss saudart... Please karki tafi... Kizo mu warware komai tare please" yafada yana maida numfashin gudun dayayi

Murmushin nan nata tasakeyi sannan tace
"Warware me? I've done my part, ko babu ni zaku iya warware komai"

"Please saudart, kizo mu gwadawa A.A, yaga abinda kikayi please, don't leave just like that"

Guntun murmushin takaici tayi sannan tace
"Ni ba don wani nayiba, idan da danshi zanyi to believe me ya Dade be fada chakwakiyar datafi wannan ba, ni don Allah nayi, kuma wannan abun ina iya yiwa koma wanene, muddin na tsinci kaina a position na taimaka wa wani zan taimaka mashi badon komaiba saidan samun lada, duniyarnan yar qanqanuwa ce, batada tabbas bansaniba wataqila wannan shine aikina na qarshe a duniya, ina iya fita yanzu inyi clashing dawata motar in mutu, yanzu haka ina iya kai Kalmar nan tazamo itace ta qarshe a duniya, idan mutane zasu dinga tuna mutuwa dakuma nazari akan duniya da sun zage, sun nemi hanyar lada at any possible time or little opportunity, kana iyayin Abu Allah yabaka lada daya bazaka San muhinmmancin wannan ladar ba sai ranarda kake Neman ladar ruwa a jallo, lada daya yana iya hana mutum shiga aljanna yafada wuta, lada daya na iya hanaka shiga wuta kashiga aljanna, shiyasa duk abinda kasan zaka aikata kasamu lada komin qanqantarshi karka bari damar ya wuceka

Ni nayi saboda Allah ne da qwadayin lada, so basai ka kaini wajen shi ba don bayada abinda zai iya biyani asalima da saboda shi zanyi da ba zanyi ba, saidai a matsayinka na aboki kuma dan uwanshi zan baka shawara, ka fahimtar dashi meye duniya, dukiya ba itace komaiba, dan Adam daraja gareshi, musanmman mahaifa, yau mahaifinka ko mashayi ne yasha yayi tatul yazo yana Marisa tsakar hanya dole nakane, dole kaji zafi idan aka sokeshi koda yana yin abinda aka sokeshi akai muddin kasan darajarshi, mahaifa ba abin wasa bane saboda bakada tamkarsu kuma bazaka samu tamkarsu ba, duk wannan zai iya zagin mahaifan wani ko yayi maganar Rashin da'a gamedasu to ka bincika, besan darajar nashi bane, ko kisan kai mahaifina yayi hakan bazai sani gudunshi ba ko w sokeshi inkasa nuna jin haushina ba, saboda bayan Allah da manzonsa wadannan hallitun biyu sune mafi daraja acikin hallitu.... Nabarka lfy". Tana kaiwa nan ta rufo kofarta ta tada motar tabata wuta.

Ja yayi da baya cikin mutuwar jiki yabata hanya tayi reverse yabita da kallo harta fice daga kamfanin.

Ya Dade nan tsaye yana saqawa da kwance wa sannan dakyar yasamu yajuya jiki a sanyaye yashige company din.

Direct office dinta yakoma inda ya ajiye takardun da wayarta Wanda bata tsaya amsaba.

"Wane irin zuciya saudart ke dashi? Gaskiya samun irin saudart acikin al'umma zaiyi wuya a irin wannan zamanin"

Kwasan kayan yayi ya nufi kofar Ashraf ya bude yashiga batareda knocking ko Neman iziniba.

Jin anshigo yasashi dagowa a masifance don ya balbale koma wanene.

Ganin sadeeq da yanayin dayake ciki yasashi fasawa ya tsaya yana kallonshi.

Qarasowa sadeeq yayi ya ajiye abubuwan gabanshi yana kallonshi.

Shima kallonshi yayi sannan ya kalli takardu da wayar kan table din.

"Wannan fa?"

"Ka duba mana, amsarka na aciki, na barka lfy" yajuya yafita batareda yajira single word from him ba.

Saida ya rakashi da kallo harya fice sannan ya dauki takardun yafara dubawa.

He was in shock sai zare idanu yake yana bin takardun da kallo, kanshi ya qulle ruff yakasa gane komai.

Wayar ya jawo ya kunna power dinta nan yaga ba password sai sliding din daza'ayi kawai.

Sliding yayi ta bude sai yaga video ne akan screen din.

Kunnawa yayi yafara ganin the shock of his life.
Chapter 43 · 0% Book details