← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 111

Sashe 77

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sallama sadeeq yashigo riqeda bottle din drink dinshi dayasha rabi.

Dan ware idanu sadeeq yayi ganin ashraf yayi changing din wurin zama sannan yadan saki murmushi ya ida qarasowa.

"To love birds, time up. Naga alamar idan aka biyemuku kuna iya kwana anan" yafada cikin barkwanci.

Dan ta6e baki saudart tayi batareda ta dagoba don dama a qagare take sutafi ko tajita normal.

"To ai saika tashi mallam, ranki ya dade zamu ruga kauyenmu"

Dan dagowa tayi ta kalleshi sannan ta sadda kai tana cewa "allah ya tsare"

Amsawa yayi da amin ya kalli ashraf dashima daidai ya kalleshi ya daga mashi gira alamun yatashi su tafi ko?

Harara ya gallamashi sannan ya miqe daga xaunen dayake hakan yasa sadeeq ficewa daga dakin.

Takowa yayi har gabanta yana kallonta.

Bugun zuciyarta yaqarayin saman jin tsayuwarshi akanta ga kaffafuwanshi datake gani agabanta kasancewa qasa take kallo.

Ahankali ya duqa gabanta yana kallonta, saurin ja da baya tayi ta shige ma kujerar tana ware manyan idanunta akan fuskarshi a mammakince don kusancin nasu yayi yawa don har tanajin saukar numfashinshi.

Daga glass cup din hannunshi yayi ya miqomata yana murmushi.

Kasa ko motsi tayi sai kallonshi datake cikin mammaki tana tunanin anya lafiyarshi lau?

Kamo hannunta yayi ya sakamata cup din aciki ya hada yariqe tenderly yana mata wani irin kallo mai tsayawa a zuciya.

Saurin sauke idanunta tayi qasa tana qoqarin zame hannunta acikin nashi amma takasa hakan yasata lumshe idanu don wani iri takeji har cikin 6argonta

"Thank you" yafada cikin rada yana kallon yadda ta limshe idanu taqi budesu ga zara zara lashes dinta dasuka hade waje daya kamar na fixing

Matso da hannun yayi saitin bakinta wanda hakan yasata saurin bude idanu tana kallonshi kamar zuciyarta xata fado tana qoqarin janye hannun.

Ahankali yayi placing din light kiss kan yatsunta dake riqeda cup din batareda ya janye idanunshi daga fuskarta ba wanda hakan yasata saurin maida idanun ta rufe gabanta na faduwa sosai.

"I love you" yayi wishpering cikin wata iriyar cool voice.

Sake tamke idanunta tayi zuciyarta na bugu sosai tanajin kanta na juyamata ahankali.

Ganin kamar hannunta nadan 6ari yasashi zare glass cup din hannun nata ya ajiye sannan ya saki hannun nata tayi saurin maida hannun cikin hijab still idanunta arufe.

"Take care of yourself... for me" yafada cikin rada in an extra cool voice wanda saida taji tasirin hakan har cikin kwanyarta.

Miqewa yayi ahankali yafara tafiya da baya baya yana kallonta.

Jiyake beson tafiya, jiyake kamar yatafi daita, jiyake be gaji da ganinta ba amma he have no choice, dolene yabi komai ahankali if he really want her, zai jira, zai jure harzuwa lokacinda zayayi nasarar mallakar zuciyarta, zai cigaba da hqr har lokacinda zata koyi sonshi, so mai tsanani irin wanda yake mata.

"Bye" yafada ahankali daidai yakai kofa sannan yajuya yafita.

Ta dade ahalin datake ciki, takasa koda bude idanunta ne bare tayi wani kwakwarrar motsi.

Jitake kamar haryanzu yana gabanta, jitake kamar haryanzu yana riqeda hannunta, jitake kamar haryanzu watery lips dinshi na kan hannunta. Jikinta haryanzu yakasa dawowa daidai, abinda yafaru yakasa barin brain dinta.

Jin an dafa kafadarta yasata saurin bude idanu a zabure.

Ganin habeeb ne yasata sauke ajiyar xuciya tana dan waige waige.

"Mamy tace what are you still doing here" inji habeeb yana kallonta.

Sauke numfashi tayi sannan ta miqe trying to be normal again

"Muje" tafada tana kama hannunshi

Haka suka fito suna tafe yana bata labarin chocolates dasu sadeeq suka bashi, itadai jinshi kawai take amma haryanzu bata ida dawowa daidai ba.

Koda suka shiga falon wucewa upstairs tayi batareda ta tsayaba.

Binta da kallo mamy tayi ta ta6e baki sannan tacigaba da kallonta.

Tunda suka kamo hanya yaketa sakin murmushi akai akai, allah kadai yasan farincikin dayakeji azuciyarshi a wannan lokaci.

"Uhmm am i really safe? Karfa inji saukar bugu, wannan dariyar dakake kai kadai anya lafiya?" Inji sadeeq daketa satan kallonshi tun dazu.

Komawa ashraf yayi ya jingina da kujerar dayake xaune yasake sakin wani broad smile kamar wanda akawa babban albishir

Murmushi shima sadeeq yayi ya maida hankalinshi kan tuqin dayake yana fadin "ba sabon ba"

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

Zaune take adaki sanye cikin kayan barci idanunta a lumshe.

Duk yadda su abdul suka so ta tsaya suyi firar dasuka saba da daddare qiyawa tayi tace kanta ke ciwo don har lokacin bata gama dawowa daidai ba kuma babu abinda tafi buqata alokacin kamar kadaici.

Tayi nisa sosai cikin tunaninta taji ringing din wayarta alamun shigowar text.

Sauke ajiyar zuciya tayi ahankali sannan ta bude idanunta ta kalli wayar dake gefenta sannan ta dauka ta bude.

Wannan special number dince, bude message din tayi a sanyaye don jinta take too weak tarasa meke mata dadi.

Gani tayi an rubuta

*the best kind of friend is the one you sit with, not saying a word and leave feeling it's the best conversation you've ever had*

*being with you today made my day and i know the smile you left on my face won't fade even in my sleep... sleep without worries JHAN*

Shiru tayi tana kallon message din, qara karantawa tayi for the second time trying to figure out something.

*Being with you today* kenan the special number is Ashraf's? Shine mai turomata all these messages dama?

Goge message din tayi tana cilli da wayar gefen gado tana jan tsaki.

"Hakan bazai chanza komaiba, nothing can change my hatred towards you, bazan ta6a bama wanda besan darajar mutane dama ba, you're wasting your time ne kawai wlh" tafada ita kadai cikin jin haushi.

So wannan sabon salon duk don ta soshi yakeyi kome? Lallai iska na wahalar da mai kayan kara.

Idan ma mafarki yake to yadaina, dadin bakinshi bazai amfaneshi da komaiba, wama yasani ko kawai lust yakeji gameda ita, the first time yayi stolen kiss from her yanzu ma daga zuwa yayi wani grabbing din hannunta yayi kissing. Me hakan ke nufi?

Haka ta kusan raba dare cikin takaici da haushin abinda yaimata don gani take this is not love, it's lust, pure lust.

Ashraf kau a 6angarenshi ranar kwanan farinciki yayi, sosai ganinta dayayi yayi tasiri a zuciyarshi, he can't just take away her picture from his thoughts. Kosu ummy saida suka lura da sauyin yanayinshi.

Washegari ma haka ya tashi da ragowar farincikin jiya, last night was filled with her dreams, mafarkan dayayi daita basu qirguwa jiya, jinshi yake so un top...✍

Sorry for the short chappy.

Aski yazo gaban goshi.

Masu complaining saudart ta riqe wuta dayawa kuyi hqr, everything will be alright insha allah, lokaci guda ake jima mutum ciwo a zuciya, warkewarshi sai ahankali. Banason rushing din komai ne, hope zaku fahimceni🙏

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

085

Tun daga wannan zuwan ashraf yasamu ticket din zarya gidan mamy.

Every two days saiya biya gidan duk don ya ganta yaji sanyi, wani lokacin ma daga office zai biya gidan yaganta sannan yawuce gida.

Shaquwa sosai tashiga tsakaninshi da qannen saudart musanmman abdul don mafi yawancin lokuta dashi take zuwa falon baqin tasameshi susha firarsu itakau daga gaisuwa bata qara uhm bare uhm uhm.

Zaryar da ashraf keyi gidan ba qaramin haushi yakebata ba don gani take duk salon takura ce, babu abinda yafi bata haushi kamar maidata t.v dayakeyi tsabar kallo shiyasa daga baya ta tsiri fita da abdul don taji sauqin kallon ko yaya ne.

Messages kau tun yana turowa tana gogewa har ta haqura ta share don wasu bata ma budesu, bataga amfaninsu ba don basa qarar daita da komai, shikau a 6angarenshi be ta6a sarewa ba ya maida abun dialy route dinshi dukda be ta6a samun reply ko sau daya ba.

***

Yau saturday, tunda ta tashi ta yanke shawarar yau saitaje saloon ayimata retouch daga nan tawuce supermarket tadanyi sayayya.

Tunda tadawo gidan mamy bata qara fitaba sosai takeson fitan nayau koba komai zata dan motsa kafa.

Fitowa tayi daga bathroom qirjinta daure da farin towel iya gwiwa kanta sanye da net cap.

Kallo daya zaka mata kasan wanka tafito duba da yadda glowing jikinta ke jiqe da ruwa. Gashin hannunta gaban goshinta duk sun kwanta luff sanadiyyar ruwan daya jiqasu.

Gaban mirror ta nufa tana gyara daurin towel din qirjinta.

Tsayawa tayi tana kallon kanta a mirror ganin yadda skin dinta ya chanza sai glowing yake.

Murmushi tadanyi sannan ta dauki man shafanta ta shafa tadanyi simple makeup sannan ta saka riga da skirt na atamfa ta yafa veil tafita.

Direct dakin mamy tanufa don tasan tana ciki, su abdul kau ana islamiyya kasancewar weekend idan suka tafi tun safe sai shidda na marece suke dawowa.

Tadda mamy tayi tana gyara gadonta hakan yasa ta ida shigowa tana sallama.

Amsawa mamy tayi batareda ta dagoba har tagama gyaran gadon sannan ta juyo ta zauna tana kallonta.

Zama itama saudart tayi kan bedside locker tana shagwa6e fuska.

"Menene?" Inji mamy tana kallonta

"Mamy my hair, yayi dirty dayawa" tafada tana dan turo baki.

"Ehen? Ni mezan miki?" Inji mamy tana dan harararta

"Zanje saloon please" tafada a marairaice

"Yaushe?"

"Yanzu, this is five, i promised kafinma su habeeb sudawo nadawo kawai wanki kai ne" tafada a marairaice.

"Ok kin gayawa mijinki?" Inji mamy.

Jimm saudart tayi tana kallonta batareda tace komaiba

"I said kin gayawa mijinki?" Inji mamy tana dan waremata idanu.

Kauda kai saudart tayi tana dan turo baki.

"kinzo wajena wai zaki saloon, ni ke aurenki? Ko kin manta ke matar aurece? Duk abinda kike ina sane samaki idanu kawai nake don ganin gudun ruwanki, yanzu duk nasihohin danake miki shiga suke a kunnen dama su fita ta haggu ko? Gaki kamar kinsan abinda yake maki ciwo amma ba haka bane, cigaba to allah yabada sa'a and if you really want to go to saloon ki nemi izinin mijinki ni ba ruwana, duk laifinsu abbanki ne dasuka wani zubamaki ido ahakan, i wonder why za'a kyaleki anan da igiyoyinki uku akai, wannan bayi bane is better ki tarkata ki koma gidanki inhuta da kayan haushi" inji mamy cikin fada don sosai zamanta ahakan ke damunta tayima abba magana yace zata koma lokaci suke jira tarasa wane lokaci suke jira.

Shiru saudart tayi tana kallon mamy tun sadda tafara fadan nata.
Chapter 77 · 0% Book details