← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 111

Sashe 32

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya akayi kuma yanzu? Abin mammaki yau the proud peacock ce a gabana amatsayin secretary na...you shouldn't have stooped so low, basai kin qasqantar da kanki ba wajen cin kudina, you have the right.
Da kin tambayeni ko nawa kikeso zan baki kodan darajar wannan tsararren auren namu, amma it's a shame, an extreme shame ace diyar shamsu, the mighty Saudart herself tayi stooping low wajen zama secretary na... *koba hakaba?*" yaqarashe maganar cikin rad'a yana kafeta da hazal eyes dinshi kasancewar ya zagayo gabanta suna kallon juna.

Wani siririn murmushi tasaki ta kalleshi taga shima fuskarshi dauke take da murmushin gefen baki Wanda yafi kama da na mugunta.

"Isn't that obvious Mr A.A?" Tafada still murmushi a fuskarta.

"Ba qasqantar dakai bane, it's called *BUSINESS*"

Daga gira daya yayi still yana kallonta murmushin kuma bebar fuskarshi ba.

"A tunanina a matsayinka na dan kasuwa yakamata kasan the full meaning of *BUSINESS*, wannan ba qasqantar dakai bane, *BUSINESS* ne, *HALAQ* dinane, my sweat.
Me kake tunani? A matsayina na yar kasuwa, diyar yan kasuwa, babana shahararren dan kasuwa ne, mamana shahararriyar yar dealer ce, duk abinda nasan zai kawomin samu muddin halaq ne zan yishi.
Am a real hustler, I hustle day and night so far it's halaq, bana depending akan wani, bana jiran abun wani, bana kwadayin abun wani saboda be dameni ba, inacin guminane, haqqina, same goes with this, aiki zanyi kuma a biyani, I don't care" tafada tana daga kafadu🤷‍♀

"Batun aure kuma Kai kema tunawa dashi har kake ganin zanci darajarshi, as far as am concerned ni ba Matar kowa bace, karka manta it's all contract, signed contract.

So am here for business ne kawai, bansanka ba, baka sanniba, babu wani alaqa tsakaninmu saina boss da employee dinshi, bayan wannan kuma babu wani dangantakar... *koba hakaba?*" itama ta qarshe maganar cikin rad'a.

Murmushin da beyi niyyar yi bane ya subucemashi yadan kawar dakai yanayi.

Lallai wannan yarinyar, her courage, her pride da confidence dinta yayi yawa.
Da watace dauko dago kai ta kalleshi bazata iyaba, da watace da yanzu tananan tanaji kamar ta nitse don kunya amma banda ita, banda shugabbar yan girman kai din duk duniya.
This is an opportunity, damarshice na koyamata hankali, na koyamata yadda ake girmama na gaba.

"Nice one miss Saudart, business ne ya kawoki right? Babu wani dangantaka tsakaninmu saina boss damai aikin shi, good and so be it, let the business start"

Saikuma ya matso dab daita har suna shaqar numfashin juna, idanunshi cikin nata.

"But are you sure you can cope with a boss like me?"

Dukda yadda takeji na yanayin kusancinsu ta danne tace "is this a challenge?"

Cikin rad'a yace "yes"

Murmushi ta qaqaro Wanda bekai zuciba tace
"Challenge.. Accepted"itama cikin rad'ar.

Murmushin gefen baki yayi yana kallonta, itama samun kanta tayi da d'an rausayar da kanta gefe itama dauke da irin murmushin shi.

Jada baya yadanyi still idanunsu cikin juna sannan yajuya yanufi desk dinshi.

Wasu takardu dogaye ya kwaso batareda yasan adadinsu ba yadawo gabanta ya dorasu saman table kusada ita.

Batace komaiba sai kallon takardun datayi sannan ta maida kallonta akanshi alamun qarin bayani.

" kiyi copy dinsu, kiyi printing sannan kowane guda daya ayi photocopy dinshi waje goma...Good luck " ya qarshe zancen yana komawa mazauninshi ya zauna yayi balancing Yana binta da wani irin kallo.

"With pleasure" tafada da murmushi sannan ta tattare takardun tafice.

Binta yayi da kallo harta fita, wani irin haushi yakeji azuciyarshi, wai me yarinyar nan ke taqama dashi ne? Me ta dauki kanta ne? Soyayi yayimata wankin babban bargo yau amma daga qarshe shi ta cusama haushin.

Qwafa yayi yana jinjina kai, zan koyamiki hankali ne.

Itakau tana shiga office dinta ta ajiye takardun saman desk dinta ta shige toilet dake cikin office din.

Ahankali ta qarasa gaban sink din toilet din ta bude fanfon wajen ta Tara tattausan tafin hannayenta ruwan na zuba cikinsu tana kallo.
Biji biji tafara gani sanadiyar hawayen dasuka tararmata acikin idanu.

Barinsu tayi suka gangaro batareda tayi yunqurin tsaidasu ba.

Tun tana hawaye harta fara shesheka ahankali.

Zafi takeji acikin zuciyarta kamar ana ruramata wuta, ga wata wutar Qin Ashraf dake ruruwa a zuciyarta, ga takaicin abinda daddy yayimata dazu, Abu dai yazaman mata goma da ashirin.

Saida taci kukanta ta qoshi sannan ta wanke fuskarta da ruwan fanfon ta tsane fuskarta da hand towel.

Dagowa tayi ta kalli kanta ta cikin mirror dake jikin sink din taga idanunta dama fuskarta sunyi jajur.
Murmushin takaici tayi sannan ta daura alwala tafito.

Dayake tazo da spare hijab a Jakarta dama, veil dinta ta warware ta samu qusurwa ta shinfida, dayake Allah yamata baiwar gane gabbas duk inda ta tsinci kanta, down haka shimfidawa tayi ta zura hijabi ta gabatar da sallar zuhr, tayi addu'o'inta sannan ta miqe tacire hijabin ta yafa veilbdinta qaraso gaban desk dinta.

Takardun daya bata ta dauka tafara dubawa.

Gabanta ne yafadi ganin uban aikinda yasata.
Takardun qwara shabiyar dogaye kowanne an rubuceshi gaba da baya, tasan intayi gudun tsiya tayi copy din biyu cikin awa daya, kafin a kaiga printing ga kuma photocopy.

Jitayi wasu sabbin hawaye na zuwamata, saurin maidasu tayi tana girgiza ksi
'No saudart, ba yanzu ba, you're strong, be strong'

Jan kujerar gaban desk din tayi ta zauna ta zari paper daya tafara aikin.

Aiki take tuquru batareda shiriritaba, babu abinda ke tadata sai sallah, tama manta dawani Abu waishi abinci, kodama ta tuna batajin tana iya sama cikinta wani Abu.

Qarfe shidda saura kofar office din Ashraf ta bude ya fito hannunshi daya riqeda briefcase dayan kuma sa6e da jacket din suit dinshi.

Taji fitowarshi kuma tasan shine amma ko dago kanta batayiba bare ta nuna tasan da wanzuwarshi.

Shima ko gefenta be kallaba yawuce private elevator dinshi da shi kadai ke ya Danna floor din qarshe kofar ta bude yashige.

Sai bakwai saudart tafito daga company din, shima bawai tagama aikin bane.
Tadaiyi copy din duka tayi printing dinsu, photocopy kawai yarage Wanda ta aje da niyyar shine Abu na farko dazatayi gobe idan Allah ya kaimu.

Agajiye tashiga motarta tarufe tafice daga company din, saida ta tsaya restaurant tayi takeaway taje pharmacy ta siya maganin ciwon jiki sannan tanufi gida.

Agajiye ta qarasa gida, sallar magrib da isha'i tayi tadanci abinci sannan tasha magani tabi lfyar gado.
Kasancewar a agajiye take bata wani Dade a kwance ba barci ya sadado ya dauke ta...✍

Ummin fasihu ce🧚‍♀

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

042

Washegari tunda tayi sallar asuba bata koma barciba.

Laptop dinta taja tadanyi yan dube dube da gyare gyare akan abinda yashafi bakery dinta da ice cream joint.

Ciwon jikin yarage sosai saidai haryanzu yatsunta na zugi saboda typing datayi.

Qarfe bakwai da Rabi ta rufe laptop din, ta tashi ta jona ruwa a electric kettle sannan tashiga wanka.

Bata jimaba sosai tafito ta shirya cikin atamfa Riga da skirt ta Dora baqar after dress ta yane kanta da gyalen after dress din.

Yauma bawani kwalliya tayiba tadai dan bursuna powder da kajal ta taje lashes din idanunta da mascara.

Hada kakkauran shayi tayi ta zauna tasha sannan ta feshe jikinta da turare tasaka takalmi tadau Jakarta tafice.

Direct parking space tanufa nan taga duka motocinshi nanan alamun be fitoba.

Shigewa motarta tayi tabata wuta sannan tafice daga gidan.

Qarfe 8:25am ta isa company din.

Parking tayi a space din sannan tafito cikin unique shigarta ta wuce cikin company din cikin takunta mai cikeda nutsuwa.

A gyare ta tarda office dinta sai tashin qamshi yake da alama ma ba'a jima da gyarashi ba.

Babu 6ata lokaci ta jawo aikin da bata idaba jiya tahauyi.

Cikin qanqanin lokaci tagama sannan tadawo ta zauna gaban system dinta ta bude.

Sai qarfe goma Ashraf ya iso company din.

Ta gaban office dinta yazo yawuce amma ko daga kai ta kalleshi batayiba hasalima nunawa tayi batama lura dashiba.

Saida tagama abinda tajeyi tsaff sannan ta kwashi dukan takardun tafito daidai shima sadeeq yafito daga office dinshi.

Ganin tana niyyar yin fuska tawuce yasashi saurin cewa

"Good morning ma'am"

Tsayawa tayi batareda ta juyoba, tasan ita yakamata ta gaidashi sbd yafita matsayi a company din amma batajin tana iya gaidashi, a halin yanzu ta tsani duk Wanda keda alaqa da A.A idan aka cire Ummy da baby.

"Hyy" kawai tace zata wuce.

"Yau za'ayi meeting dinnan ko?" Yaqara fada

Batareda ta tsaya daga tafiyar datakeba tace
"Nasani"

Tayi knocking sau daya tabude kofar tashige tabarshi anan.

Jin anbude kofar anshigo yasashi dago kai yana kallonta.

Qarasowa tayi gabanshi batareda tabari sun hada idanu ba ta ajiye takardun kan desk din.

"Good morning" tafada ciki ciki

Be amsaba kuma bebar kallonta ba

"Ga papers dinnan, kuma yau munada meeting biyu, daya qarfe 12:00pm dayan kuma bayan asr"

Bece mata komai ba sai jawo takardun data ajiye yayi yafara dubawa.

Yayi mammaki sosai na ganin ta gama aikin duka kamar yanzu, shi bemayi tunanin zata gamashi yau ba, a tunaninshi saikuma batun gobe.

Be bari mammakin ya bayyana a fuskarshi ba ya cigaba da dubawa ko zaiga mistake ko dayane amma komai daidai yake kuma cikin tsari.

"Ok, amshi" yafada yana miqamata takardun.

Babu musu ta amsa

"Ki chikwikwiyesu duka"

Dum gabanta yafadi tayi saurin dagowa ta kalleshi.

Dagamata gira daya yayi yace
"Yes, squeeze it"

Wani Abu ta hadiye a maqoshinta dakyar sannan ta ajiyesu kan table din ta fara dauka da daya daya tana chukwikwiyewa tana ajiyewa gefe.

Tasan yayi hakanne don ya 6atamata rai yaganta cikin bakinciki saidai bazata bashi abinda yakeso ba don haka ko afuska bata nuna ta damuba, fuskarta nanan dai yadda take babu yabo babu fallasa amma karka bincika zuciyar.

Haka taita chukwikwiyewa harta gama.

"Sasu a waste basket"

Babu musu ta kwashesu ta zubasu a wani emptyn kwadon shara dake daga can gefe.

"Good ga wannan ki karanta" yafada yana miqamata wata paper

Amsa tayi tana dubawa

"Ba aciki zaki karanta ba, a bayyane"

Daidaita muryarta tayi sannan tafara karantawa.

" 1. Lokacin zuwa office 8:00am

2. Hada coffee 8:55am

3. Gabatarda aikin da aka kwana dasu 9:10am

4. Girmama na gaba dakai ta hanyar kiranshi sir ko ma'am
Chapter 32 · 0% Book details