← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 111

Sashe 38

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"My pleasure sir(s)" tafada cikin girmamawa

"Shall we?" Inji baqin cikin mutanen yana nuna hanyar ciki.

"Sure" duk sukace gabadaya suka dunguma suka shiga ciki suna tafiya suna fira jefi jefi...✍

Insha Allah idan nasamu lokaci zakuga next page ko zuwa dare ne amma idan kukaji shiru kuyimin uzuri🙏

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

048

Restaurant din hotel din sukayi reserving don gudanar da meeting din.

Zauna suka kan kujerun dake zagayeda wani round table, kowanne da robar swan a gabanshi da glass cup duk sunyi shiru suna sauraron bayyañin da daga daga cikin mutanen mai suna *Hussain* keyi.

Meeting ne akan wani contract na ordern gwalagwalai dazasuyi, kasancewar companyn A.A companine na dealer gwalagwalai da zinarai, yana daya daga cikin companyn dayayi fice a Nigeria dama Africa gabadaya, yana ordering din gwalagwalai a qasashe daban daban.

To anan ma hakan take, zuwa yayi don yin ordern wasu latest design na gwalagwalan masu tsadan gaske don sabbin design ne don ba'a gama saninsu a duniya ba.

Wani qaramin akwatin glass ne a tsakiyar table din Wanda ke dauke da sample din gold din.

Saida Hussain yagama 6a66atunshi sannan ya buqaci su duba suga ingancinshi.

Budewa baqin cikinsu yayi ya fiddo ya miqama saudart dake gefen Ashraf, ta amsa sannan ta miqama Ashraf.

Sundan Dade suna dubawa (Ashraf & saudart) suna jujjuyawa suna dan qus qus tsakaninsu da alamun shawara suke yankewa.

Sudai mutanen kallonsu suke har suka gama sannan Ashraf ya maidama saudart Itakuma ta miqama Wanda yabata.

Cikin inganttaciyar turancinta tace

"Yayi kyau sosai, amma kunzo mana da kala kalan designs dinsu ne, munason mu za6a" tafada tana kallonsu, Ashraf dake gefenta na kada kai alamun abinda tafada gaskiya ne

Baqin Wanda yakira kanshi da *zahid* yace

" sosaima, gashi Ku za6a" yafada yana bude musu laptop ya shiga hotunansu sannan ya turomusu Gabansu.

Nan suka shiga dubawa suna za6an choice dinsu suna qus qus, idan ka gansu a lokacin baka ta6a tunanin tom & jerry dinnan ne don dukansu sunci serious sosai.

Saida suka za6i iya Wanda sukeso sannan aka maida musu laptop din.

Nan sukayi cinikin iya adadin dazasu saya Wanda za'a turomusu ta jirgin ruwa bisa yarjejeniyar zasu fara bada Rabin kudin anan, Rabin kuma sai kaya sun isa.

Anan aka yanke shawarar zasu sake haduwa a companyn su Hussain din ranar Monday don biyan Rabin kudin kamar yadda suka tsara sannan suyi abun a rubuce kowa yasa hannu saboda yazama shaida.

Awa daya meeting din ya dauke su sannan su saudart suka miqe don tafiya kowanne fuskarshi fall fara'a.

Har mota suka rakasu, dayake makullan motar na hannun saudart sai kawai tashiga mazaunin driver ta zauna tana jiran Ashraf dahar yanzu suke magana da mutanen.
Can sukayi musabaha sannan shima yashiga motar suka bar hotel din.

Tunda suka hau hanya babu Wanda yacewa kowa uffan gar suka qarasa gida.

Lokacin da suka iso har anfara kiraye kirayen sallar la'asar don haka bema shiga gidanba yawuce masjid din estate din Itakuma ta shigewarta ciki don gabatarda tata.

Bayan tagama sallar ne taciro wayarta tafara kiran yan Niger.

Da daddy tafara, sosai suka sha fira dashi Wanda Rabi shagwa6a ce take zuba mashi yana biyemata sannan takira mamy nan Suma suka gaisa da kowa na gidan kowanne nabata sabtun tsarabar dazatayi mashi sai dariya take musu.

Sai bayan sunyi sallama sannan ta bugama Ummy.

Sosai Ummy taji dadin kiran nata, sunsha fira sosai kafin takaima baby wayar

As usual ihun nan nata na hauka taitayi da sunan murna, nan sukasha fira kamar ba gobe sai tsokanarta baby take wai ya? An samu tsarabar nata koko da saura? Itakuma tana amsa mata da zata gane kuranta ne saita gayamashi.

Haka sukaita firarsu, dakyar suka ajiye wayar kowanne najin qaunar dan uwanshi har cikin zuciyarshi.

***********************************

Tana cikin shirin kwanciya kasancewar har Tara tayi taji ana bubbuga kofarta.

Dan jimm tayi daga gyaran zanen gadon datake ta kalli kofar.

Jin ansake bugowa yasata Sakin bedsheet din ta zura hijabin sallarta akan doguwar rigar barcinta sannan tanufi kofar.

Tana budewa taga shine, gyara tsayuwarta tayi tana kallonshi da alamar tambaya.

"Coffee.. Kikawomin a study room" yafada yana wucewa.

Galala tabishi da kallo harya shige.

Mene? Coffee cikin Daren nan? Wannan wane irin wahalarwa ne?
Mutum na shirin barci awani tsiromashi aikin hada coffee?

Sosai ranta ya 6aci don barci ke idanunta burinta kawai ta kwanta.

Babu yadda ta iya haka tawuce kitchen din ranta a jagule, tsaki kau tafishi yafi cikin kwando kafin tagama hadawa.

A study room din tasameshi zaune gaban laptop sai danne danne yakeyi.

Ciki ciki tayi sallama sannan ta qaraso gabanshi kamar bataso sannan ta dungure mashi mug din coffeen a kan table din gabanshi tajuya da niyyar komawa.

"Come back here" yafada batareda ya dago daga kan laptop din ba.

Saida tayi jimm kaman bazata juyoba sannan tajuyo tadawo gabanshi ta tsaya.

Dagowa yayi yana kallon yadda taketa faman kumburi tawani tsaya mashi akai.

"Da ina zaki?" Ya tambayeta

"Ina bayan dakina?" Tafada cikin son danne fushinta

"Na sallameki ne?" Ya fada cikin son qular daita

"Ba na hada cofeen ba? Ni Am sleepy wlh" tafada tana turo baki.

"Barci? Dama barci ya kawoki nan?"

"Bashi ya kawoni ba, amma ai yanzu na hadamaka coffee din ko? Zan iya tafiya ko?" Tafada cikin tsiwa tsiwa

Daukar mug din cofeen yayi ya kafa Kai ya shanye sannan ya diremata

"Make another one"

Wani Abu taji ta taso ya toshe mata maqoshi, Kutt...

"Bakijiba? Nace ki hado wani" tafada yana kallon yadda fuskarta ke yin ja ja ja ja alamun tana cikin tsananin 6acin rai.

Batace komai ba ta figi mug din ta fice tana bugomashi kofa har yana toshe kunne.
Binta yayi da kallo sannan ya jinjina Kai yana murmushi

"Shima wannan you'll pay for it" yafada yana maida hankalinshi kan laptop din.

Can saigata ta dawo ta qara dungure mashi mug din har coffee din badan zubewa.

Dagowa yayi yana kallonta da mammaki

"Wai kwakwalki qalau kuwa?"

'Kai ka cancanci tambayar' tafada a zuciyarta

Banza tayi dashi ta juyamashi qeya.

Qwafa yayi ya cigaba da danne dannenshi sannan ya dauki mug din yakai baki da niyyar kur6a.

Kur6a daya yayi yayi saurin furzoshi ko maqoshi be kaiba saboda wani zau dayaji a harshenshi.

Kauda Kai tayi saurin yi tana son hadiye dariyarta

"Kutt... Uban me kika samun a coffee? Kasheni zakiyi?" Ya tambaya yana kallonta cikin mammaki

"Ni me nasa?" Ta tambaya tana dan matsawa baya.

"Me kika sa ko? To wlh saikin shanyeshi yafada yana daukar mug din ya nufota.

Ai a sittin tayi wani turning tana fasa qara ta bude kofar tayi waje tana tsuwa.

Binta shima yayi dagudu saidai kafin ya taddota harta shige daki ta Danna sakata sama da qasa tana numfashi sama sama.

Bubbuga kofar yashiga yi da karfi yana cewa tazo ta bude amma tayi banza dashi saima antayama kofar harara datake

" to wlh ki tabbatar nan zaki cigaba da zama har abada don ido na idonki..." Sai yayi Kwafa yana jinjina kai sannan yayi tafiyarshi

"Idan na fito karka barni da rai, mugu kawai mummuna" tafada tana murguda baki sannan ta haye gado tashige cikin bargo...✍

Kuyi manage🙏

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

Sorry for the late post🙏

Yanzu bazaku dinga ganin post ba akai akai, munada hidima, please bear with me🙏

Washegari Friday, bata yarda tafito daga dakinta ba saida ta tabbatar yabar gidan gabadaya.

Sai a sannan tasamu kwanciyar hankalin fitowa don yin aikace aikacen datasaba.

Saida ta share koina, ta goge, tabi da freshener sannan tashiga kitchen don samarma kanta abin ci.

Tana cikin suyar kwai taji ana bubbuga kofa.

Gabanta ne yafadi jin bubbugar kofar abinka da marar gaskiya don duk a tunaninta Ashraf ne.

Kwan ta kashe batareda ya ida soyuwaba ta saka a plate ta jidi kayan breakfast din tayi daki dasu sannan ta dawo cikin sanda ta qaraso kofar tana leqen wajen ta wurin nan na kofa don ganin waye.

Ganin wasu yanmata biyu tsaye yasata Sakin ajiyar zuciya sannan tabude.

Yanmata biyu tagani tsaye fararen fata kowacce tasha kayan sanyinta sai washe mata baki suke.

Itama washe masu nata bakin tayi Tanadan matsawa don basu wuri sy shiga tana cewa
"Please come in"

Babu musu suka shigo suna bin falon da kallo suna murmushi.

Maida kofar tayi ta rufe sannan ta qaraso ciki tana musu tayin zama cikin fara'a

Babu musu duk suka zauna

"Bari nakawo muku ruwa" tafada cikin turanci

Dakatar daita daya tayi dacewa

"A'a yar uwa, murda ga gidanmu nan kusada ku, bawani tafiya mai tsawo mukayi ba kuma ma sanyi ake ba'a cika shan ruwa ba"

Murmushi saudart tayi sannan ta koma ta zauna tana cewa
"Kenan Ku maqobtanmu ne?"

"Eh mana, fa gidanmu nan No 35 Itakuma wannan No 37" inji Wanda tayi magana dazu

"Wow, nice to meet you" tafada cikin Sakin fuska.

"Thank you, sunana Loveth wannan kuma Reyna" inji mai maganar

"Wow nice name, ni sunana saudart" tafada tana murmushi

"Wow nice name too, amma Ku baqi ne ko?" Inji Wanda aka kira da Reyna

"Eh kwananmu biyu yau" saudart tabasu amsa

"Ayyah ai naganku jiya dazaku fita, banma San akwai mutane saida naganku jiya" inji Loveth

"Ai saboda bamu Dade bane shiyasa" saudart ta amsa

"Ok, dama zuwa mukayi muji zaki samu zuwa wajen hada kayan Good Friday?"

"Good Friday?* inji saudart cikin Rashin fahimta

"Eh, good Friday wani taro ne haka mukeyi duk ranar Friday, duka yan yankinan zasu hadu don zumunci, anan muke sanin baqin dasuka shigo kuma mu qulla zumunci" inji Loveth

Reyna ta Dora dacewa
"Akwai wata mata a block 39, doctor ce kuma duk ta fimu shekaru, a gidan ta duk muke taruwa mu hada kayan da za'a dan ta6a a gathering din, muna zuwane da marece mukama aikin ayi agama da wuri, idan zaki samu damar zuwa saiki leqo ayi dake"

"Wow yayi kyau sosai, insha Allah zan leqo idan nasamu dama" inji saudart tana murmushi
Chapter 38 · 0% Book details