← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 111

Sashe 33

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

5. Kar ashigo office harsai anbada izini duk jimawarka kana knocking.

6. Another coffee 3:00pm

7. Closing time 6:30pm"

Dago kai tayi daga takardar bayan tagama karantawa.

Ahankali yabude bakinshi kamar beso yawani yi balancing a kujera yana dan jujjuyawa yace

"Nakine.. Fatan za'a kiyaye"

"Ok" tafada a ataqaice

"Ok..what?" Yafada yana tsareta da idanu

Banza tayi dashi don batajin tana iya kiranshi da sir din dayakeso, Kai ina? Bekaiba.

"Magana Nike"

Nanma tsit don ko gefenshi bata kallaba

Murmushi mai dan sauti yasaki sannan yajawo wasu takardun cikin wadanda yabata jiya ya Diba da yawa Suma batareda yasan adadinsu ba ya tura a gabanta yace
"Same thing da kikayi jiya" ya koma ya jingina da kujerar yana kallonta.

Babu musu ta kwasa har gyara zamansu take kamar bata damuba sannan tajuya tafice.

Binta da kallo yayi harta fice sannan yayi qwafa yana jinjina kai.

Komawa tayi office dinta ta Dora takardun saman desk ta zauna kan kujera ta kifa kan akan desk din tana sauraron yadda zuciyarta ke bugawa kamar zata fado Gawani suya na musanmman datakeyi.

So take tayi kuka ko zataji sauqi amma kwata kwata kukan yaqi zuwa, ambaton sunan Allah tafarayi tana dan jujjuya kanta saman desk din.

Ta jima ahakan sannan tafarajin sauqi acikin zuciyarta.

Tashi tayi ta jawo papers din Suma tahau copy dinsu.

11:55am ta dakatar da aikin datake ta miqe tanufi office din A.A don 12 dot za'ayi meeting din.

Kwankwasawa tayi taji shiru tasake nanma shiru, tasake nanma tsit.

Murmushin takaici tasaki, wato don ya wulaqanta ta yasashi kafa dokar idan ba iziniba aka badaba kar a shiga.

Komawa tayi office din ta share shi, ayi cancelling din meeting din for all she care.

12 daidai sadeeq yafito daga office dinshi da niyyar wucewa shima meeting din.

Mammaki yayi ganin saudart a office tana aikin ta ta dode kunne da earphones irin Wanda ake dorawa akai dinnan.

To ko batasan da ita za'ayi meeting din ba ne?
Tambayar dayayiwa kanshi kenan.

Qarasowa office din yayi yayi knocking.

Dagowa tayi ta kalleshi batareda tace komai ba.

Shigowa yayi ya tsaya daga bakin kofa yace

"Are you not supposed to be in the meeting Hall?"

Dan zame earphones din kunnenta tayi tana cewa "Perdon?"

Ajiyar zuciya yayi yace "nace meyasa baki fito meeting din ba?"

"Boss dinne ke barci" tafada tana maida earphones dinta

Shiru yayi cikin mammaki.

"Barci?"

Bata ko dagoba bare yasamu amsa.

Fita yayi ya nufi office din A.A din ya bude batareda ya kwankwasa ba.

A.A daya cika faam saboda tafiyarta datayi daga tayi knocking uku be amsaba kuma gashi har sha biyun ta gota bata dawoba ya dago Kai don ganin wane isashen ke shigowa batareda knocking ba.

Ganin sadeeq ne yasashi kauda kai.

Shima sadeeq qara tamke fuska yayi don haryanzu be huceba ya qaraso ciki.

"Yadai? The meeting is 12 gashi yanzu past 12"

"Cancel it" yafada batareda ya kalleshi ba.

"What?" Inji sadeeq cikin Waro idanu

"Am not speaking Chinese" inji Ashraf yana wullamashi mugun kallo

"Wai for goodness sake Ashraf lafiyarka qalau kuwa? Meeting din da kusan wata daya kenan da arranging dinshi zakace ayi cancel? What exactly is your problem?" Inji sadeeq ciki quluwa jiyake kamar ya rufeshi da bugu.

Banza Ashraf yayi ya kyalleshi

"Look Ashraf idan saboda saudart ne fine, ka sallameta din, atleast kasan badakai ta dogaraba kuma itama Kanta bada son ranta take aikinnanba ni shaidane, zanje inyi firing dinta kowama ya huta" yafada afusace yanufi kofa.

"Don't dare me! Ban sakaba"

"Saika sani?"

"Sadeeq don't!"

Hakan yasashi juyowa yana kallonshi

"Menene to? Bakai kace kayi firing dinta ba?"

"That was then, amma yanzu dolene tayi aikin, dolene!"

"Kai ka isa kasata dolene?"

"Namayi yawa so shut the hell up!"

"Mtcheew yanzu zaka meeting din ne koko?"

"Dole saina jera dakai?"

Tsaki sadeeq yaja yafice yana fadin "kanka yakeji"

Koda yafita bega saudart a office din ba hakan yasashi wucewa Hall fin meeting din inda a can yaganta sunadan tattaunawa da baqin cikin Sakin fuska.

Saida ya mula yasha iska sannan yashigo Hall din fuskarshi a tamke.

Saida ya zauna sannan meeting din yafara.

Saudart ce ta miqe tafara gabatar da dalilin taruwar meeting din.

Sosai ta burge mutane da yanayin yadda take gabatar da abin cikin nutsuwa da turancinta lafiyayye ga fuskarta a sake very friendly, hakan yasa kowa ya maida hankalinshi kacokan akanta.

Bayan tagama takoma ta zauna nan P.A wato sadeeq ta Dora daga inda ta tsaya yana yimusu bayani dalla dalla akan abinda ya tarasu sannan shima boss ya Dora da nashi shima cikin bi daki daki da ganin cewa ya warware musu komai.

Ataqaice dai saida sukayi awa daya a office din sannan aka gama meeting din kuma alhamdullilah ansamu abinda akeso Gawani farijinin da saudart tayi nan take don sai yabonta ake kan qwarewarta da fara'arta.

Koda suka fito direct office dinta takoma tayi azahar sannan takoma kan aikinta dukda tasan shima qarshen shi basket za'a sakasu.

Uku dot ta dakata ta tashi tana gyara gyalenta sannan tafito ta nufi office dinshi don hadamashi coffee din.

Bugu daya, biyu, uku amma yanzu ma tsit ba'ada niyyar amsawa hakan yasata Jan tsaki ta murda kofar tashiga da sallama...✍

Manage please🙏

Ummin fasihu ce

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Wayyo fans naga cigiyarku, am sorry😢 wlh WhatsApp dina yayi expire, dama na fadamaku yakusa sai yau naturo wani, but I missed you too, soo much😘😘

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

043

Yanzuma dagowa yayi yana kallonta, batareda tabari sun hada idanu ba ta nufi coffee maker din office din tafara hadawa.

Dauke Kai yayi ya maida kan rubutun dayake acikin zuciyarshi kuma yana ayyana yadda zai koyamata hankali.

Wato simple instruction bazata biba, kenan she's too big tajira yabata izinin shigowa?

Kwafa yayi cikin zuciyarshi, he wonder why she's so proud of herself, jin kanta yayi yawa, me take dashi? Metake taqama dashi?

Idan kyau ne akwai wadanda suka dameta suka shanye a kyau suna binshi, akwai classic ladies dirarri wadanda saita raina kanta agabansu masu so ko kallo daya ne yayimasu amma basu isheshi kalloba.

Mace bata ta6a rainashi ba yadda ta rainashi, mace bata ta6a nuna halin ko-in-kula dashiba kamar yadda takeyi, wasu ma dying suke dan suji ya furta koda kalma dayace garesu amma this one is as if ko ganinshi batason yi.

Beta6a sanin akwai mata masu girman kai da jida kai sai akanta, yasaka shi akebi yana wulaqanci son ganshi hakan yasa yakejin wani iri yanzu idan tanuna she didn't care about his existence, gani yake it's an insult to him ace kamar wannan yarinyar na nuna batamasan da wanzuwarshi ba.

Ajiye mug din coffee daketa faman tururi agabanshi ya katsemashi tunani.
Dagowa yayi yana kallonta qasa qasa.

"Sugar or honey?" Ta tambayeshi batareda ta kalleshi ba.

Banza yayi da ita tareda cigaba da rubutunshi.

Bata sake tambayarshiba ta dauki sugar cube biyu tasaka mashi ta jujjuya sannan ta maida sugarn da zuman ma'ajinsu tayi hanyar fita.

"Stop!" Ta dakatar daita da hakan.

Cak ta tsaya batareda ta juyoba.

"Come back here" yafada still hankalinshi nakan rubutunshi

Babu musu tadawo ta tsaya gabanshi not saying anything

"Throw the coffee away" yafada batareda ya dagoba.

Jimm tadanyi sannan ta dauki mug din tawuce toilet ta juye a sink ta dauraye mug din tadawo ta kifa, harta kusan kaiwa kofa taji yace

"Make another one"

Wani Abu taji ya zo daidai maqoshinta ya tsaya yaqi wucewa.

Me wannan gayen ke nufi da itane? Ta hadamashi yasata zubarwa kuma yace ta hada wani? Me yakeso daita ne?

'He want you angry'_wata zuciyar ta rada mata.

'Then he should hug transformer' tafadawa zuciyar

Juyowa tayi batareda nuna dumuwar komaiba a zahiri amma a badini tafasa take, kai tama fara kamu, jitake kamar ta Dora hannu aka taita ihu.

Haka takoma tasake hado wani coffee din, wannan karon honey tasa teaspoon daya takawo mashi.

Yanzunma be tashi yimata magana ba saida takusan kofa sannan yace ta zubar.

Gani yake abin nata gaba gaba yakeci, wato she can't ask twice? Lallai

Sake sata hada wani yayi, tahada again this time around sugar tasa saida ta ajiye yasake sata zubarwa.

He want to show her ya isa and she must follow his instructions a matsayinshi na boss dinta.

Itakuma a 6angarenta she know exactly abinda yake nufi amma ta nuna batasaniba, her ego won't let her ask again.

Haka taita zaryar hadawa tana zubarwa, sosai zuciyarta ke suya kawai daurewa take ga maqoshinta har wani yaji yaji yakeyi amma taurin kai ya hanata surrender

Ahakan sadeeq yashigo don ajiye wani file sannan ya wuce masjid.

"Throw it away" yasake cewa batareda ya dagoba

Itama bata kalleshi ba tashiga toilet tadawo da empty mug.

Da mammaki sadeeq yatsaya yana kallonsu cikin son fahimtar meke faruwa.

"Make another one" yasake umartarta.

Babu musu tasake hada wani takawo ta ajiye.

"Throw it away"

"What?" Inji sadeeq cikin tsananin mammaki

Wani kallo Ashraf ya wurgamashi yana kauda kai.

Itakau saudart bata tsaya sauraron su ba tawuce toilet din.

"Ashraf meye haka?"

Banza yayi dashi.

"Look Ashraf, da baban wannan yarinyar kake da case bada itaba, why zaka dinga wahalar daita? Plus almubazzarancin dakake, kasan wani nacan ba Neman Rabin wannan vesamuba amma kai kesawa a zubar?"

Nanma banza yayi dashi, zai sake magana tafito riqeda mug din

"Ermm.. You can go please" inji sadeeq yana kallonta.

Batace komaiba ta kifa mug din tawuce zuciyarta kamar tayi bindiga.

Saida tafita sannan sadeeq yasake cewa

"A.A kaji tsoron Allah, sbd kaga mutum na qarqashinka zaka dinga zaluntarshi"

"Dakata mallam! I have the right din sakata ko hanata, am her boss ok?! Inada right to do anything ok?! Don haka karka sake questioning dina, muddin zata cigaba dayimin girman kai to bataga komaiba ma, mtcheew!"

Ya tashi yanufi toilet kamar zai tashi sama.

Binshi da kallo yayi harya shige sannan ya ta6e baki yad'an daga murya yace

"To zuciyatu, karka manta munada meeting bayan asr, idan kuma kaga dama cancel it, ruwanka" ya fice

Tsaki yaja cikin toilet din yanufi sink din, abinda yagani yasashi tsayawa yana kallo cikin mammaki.
Chapter 33 · 0% Book details