← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 111

Sashe 54

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Tell me, waye yazo jiya? Waye yazo yasami ummy jiya yabata wannan takardun" yafada yana kafeta da idanu.

Shiru baby tayi tana sadda kai qasa cikin tsoro.

"Tell me ok? Don't get scared" yasake fada ahankali

"Suzy.."

Dan ware idanunshi yayi

"Wanene?" Yasake tambaya cikin mammaki

Hawaye taji suna taranmata a idanu

"Suzy ce yaya"

Shiru yayi yana kallonta don harga allah inba yanzu data kira sunanta ba harya mance da wanzuwarta a duniyarnan.

"Suzy? How?"

Sniffing tayi ahankali sannan tace

"Muna zaune bayan mungama lunch mukaji doorbell na ringing, Asabe taje ta bude sai gashi sun shigo tareda ita tayi shigarnan nata na rashin dacewa.

Nayi mammaki dana ganta har cikin falonmu amma sai banyi maganaba muka bita dakallo nida ummy hartazo tanemi wuri tazauna ta dora qafa daya bisa daya tana taunar chewing gum.

Nice nace 'mallama lfy zaki shigo gidan mutane babu ko sallama and ki zauna vatareda an baki iziniba?'

Kallon banza ta watsamani sannam tace
'Save it, ba wajenki nazoba wajen kakar da ko diyata nazo, so mind your damn business'

Shiru mukayi muna kallonta cikin mammaki don babu wanda ya fuskanci inda ta dosa.

Kallon ummy tayi tace 'barka da warhaka hajiya, fatan kina lfy?'

Karfin hali ummy tayi tace 'lfy lau, wacece ke?'

"Surukarki nan gaba insha allah kuma uwar jikanki nan bada dadewa ba"

Kallon juna mukayi nida ummy sannan na miqe a fusace ina cewa
'Look mallama tashi kifita! Rashin ajin naki haryakai kibiyo mijin wata har gidansu don rashin zuciya..'

Ummy ce ta katseni ta hanyar dagamani hannu sannan ta kalli suzy da ko ajikinta saima kallonmu sheqeqe datake.

'Baiwar allah, vamu fahimci bayananki ba'

'Ok ina nufin ni karuwar danki ce Ashraf mai dauke da danshi ko diyarshi a marata, yanzu kin gane?'

Abin ya dakemu sosai dagani har ummy.

Bansan sadda nakai wajenta ba sai gani nayi ummy na kiciniyar rabani daita.

Dakyar ta banbareni jikinta tanamin fadan meye haka nakeyi.

'Ummy qarya takeyi, tana daya daga cikin yan iskan dakebin yayane tun kafin yayi aure, ganin be aureta ba shine zata yimashi sharri, nasanta ummy nasanta farin sani' nafada ina huci

'Kin sanni amma bakisan yayanki ba, idan ni yar iskace to yayanki dan guguwa ne don shi ya koyamin iskanci yafake da auren bogi don azaci kamili ne a zahiri bayan yana tsula tsiyarshi a 6oye'

Kalamanta sunyi mugun 6atamin rai hakan yasa na nufeta again ummy tayi saurin kamo hannuna sannan takalli suzy

'Kinsan dawa kike magana? Kinsan kan wa kike magana? Kinsan abinda zaki iya jama kanki akan wannan qazafin?' Inji ummy da alamun itama ranta yafara 6aci.

'Ba qazafi bane hajiya ban taho nanba saida sheduna, ashraf auren bogi yayi, tsararren aure yayi da wannan yarinyar don wanda itama tayishi ne don tarufama kanta asiri...'

Cakumota nayi wanda hakan yayi sanadiyar katsewar maganarta nafara bugunta takoina hakan ya fusata ummy ta juyoni da qarfi ta daukeni da mari wanda yasani dawowa hayyacina, nan taita man fada inda take shiga batanan take fitaba sannan tajuya kan suzy tace ta zauna ta gayamata komai dalla dalla.

Zama suzy tayi sannan tacigaba dacewa
'Nida Ashraf masoyane tun a school, shine saurayina na farko kuma shine yafara kawarmin da virginity na' saita fashe da kuka.

'Shi ya lallatani nikuma saboda soyyayar danake mashi yasani biyemashi, bayan yagama karatunshi yadawo nigeria yafara aiki nikuma yabarni can ina kammala karatuna, lokacin kuka takuramashi kan batun aure shikuma ni yakeson aura nikuma family na sunce bazasu aurar daniba saina kammala karatu na.
Hakan ya tada hankalina sosai..dafarko harnaso bijirewa akan saina kammala karatun don inasonshi sosai don hakanma yabashi damar yin amfani da son danake masan ya lallatani.

Ana hakan yazo qasar wanda dama al'adarshine daya fita qasar waje da sunan business trip wajena yake gangarowa muyita masha'ar mu.

Nan yaita rarrashina ganin yadda duk nadamu yacemin yasamo mana mafita wai akwai wata yarinyar dazasuyi auren kwangila daita.

Cikin mammaki na tambayeshi Auren kwangila kamar yaya?

Sai yace wai itama yar hannuce wato tasha mu'amala da maza to shine takeson yin aure amma tana tsoron kar asirinta ya tonu don a zahiri tana pretending ita kamilace kuma nitsatsiya wanda a badini kuma karuwace, shine tazo mashi da tayin ya aureta na yan wattani saisu rabu yadda zatayi aurenta a matsayin jawara babu wanda zai zargi komai, suka yanke wannan shawarar akan babu abinda zai shiga tsakaninsu har su rabu wanda lokacinda zasu rabu kuma zaiyi daidai da nagama karatu sai muyi aurenmu'"

Shiru baby tayi tana sheshekan kukan da tundazu tafarashi, shikau ashraf kamar statue yakoma sai binta da kallo yake babu ko kyaftawa.

"Yaya wlh bakaji yadda najiba alokacin, zuciyata kamar ta tarwatse, nasan karya take yaya, sharri take qulamaku kaida anty hakan yasa natashi nasake nufarta ina bugunta ina kuka ina cewa karya take wlh sharri take muku.
Itadai ummy batace konaiba, she's shocked to death don tama kasa motsawa.

Dakyar suzy ta kwaci kanta ta tureni nafadi sannan ta watsamana wasu takardu tana magana cikin qaraji wai muduba idan qarya take don harda shaidu gasunan.

Duqawa ummy tayi ta tattara takardun tana dubawa nan mukaga takardar comtract ne na auren kamar yadda tafada ga sa hannunka 6aro 6aro gana aunty ga kuma na sadeeq na hudun kuma tace natane.

Mun shiga rudani sosai don sosai hankalinmu yatashi.

Dayar takardar kuma na gwajin juna biyu ne nata na wata biyu sai hotuna dakuke tare.

Ahankali ummy ta dago ta kalleta sannan ta sake kallon hotunan taga eh ita dince tareda kai.

'Juna biyu gareki?' Ummy ta tambaya

'Eh ummy kuma nashine wlh' ta amsa tana matsar hawaye

'To meyasa kika tonaku bayan ba haka kukayi dashi ba?' Ummy tasake tambaya

'Saboda yanason tilastamin zubarwa ne kuma ni ina tsoron aikata kisan kai, dana gayamashi yace to ku in zubar ko intafi can nida cikin kar in alaqantashi dashi don ba shirya zubewar mutuncinshi ba, nikuma naji haushi nafara masifar be isaba don tun farko shiya lallatani ba wani ba, shine yayiman mugun bugu yakuma ce yafasa auren kuma karna sake nanuna nasanshi.

Ganin ban iya facing din family dina da wannan abin kunyar yasani tahowa nan don a warware komai asamamin mafita'

Tashi nasakeyi ina qaryata cikin kuka
'Ummy qarya take wlh, son yaya take da aure shikuma yaqi saurarenta shine tabiyo ta wannan hanyar tayaya za'ace anty saudart karuwa ce? Tayaya yaya zaiyi zina? Wannan sherrin editing ne'

Dagaman hannu ummy tayi sannan tace ma suzy ta tafi zata nemeta saita tashi ta tafi.

Zuwa nayi kusada ummy nayita mata rantse rantse cewa qaryane, sharri ne

Batace mani komai ba sai shirun datayi na wani lokaci sannan ta umarceni na kira aunty saudart.

Kira biyar nayimata lafiyayye amma bata dagaba hakan yasa ta kiraka tace kuzo.

Saigashi kuna zuwa kuka gasgata abin"

Ta qarashe tana kifa kanta a dining table din.

Tsitt wurin ya dauka bakajin komai sai kadawar a.c dake wajen

Idanunshi sun kada sosai kamar gauta yayinda numfashinshi ke fita da nauyi har kana iya hango yadda qirjinshi ke sama da qasa.

Motsin dataji yasata dagowa daga kifa kan datayi taga shine ya miqe.

Sosai yanayinshi ya tsoratata hakan yaqara bugun zuciyarta.

Juyawa yayi batareda yace komaiba ya fice daga dining din dama falon gabadaya yanufi parking space cikin wani irin taku nashi wanda ban ta6a ganiba saiyau.

Wayarshi yaciro yana dailing din number yana bude motar.

Ba'a dagaba harta tsinke hakan yasa yasake bugawa lokacin harya shiga motar ya tadata.

Sai a kira na uku aka daga, lokacin harya fara reverse

"Fuck you! Ina kake!" Yafada cikin wani irin murya

Bansan kome aka fadamashi ba saiya sake cewa
"Damn you! Nace where the hell are you before I straggled you to death!" Yafada tsakankanin haqora, qirjinshi sai sama da qasa yake alamun zuciya

Bansan kome akace ba sai gani nayi yayi tilli da wayar seat din baya sannan ya bama motar wuta yafice daga gidan kamar zai tashi sama...✍️

Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)

064

Tsit dakin yayi bakajin komai sai qarar a.c dake aiki.

"Kutt... amma anyi tsinnaniyar yarinya, ciki? How and when?" Inji sadeeq cikin tsananin 6acin rai

Cize le6enshi na qasa Ashraf yayi yana kalkada kafa daga inda yake zaune, shikadai yasan abinda yakeji acikin zuciyarshi.

"Lallai dolene akoyama yarinyarnan lesson, ni wlh nama manta da ita ashe tananan tana bibbiyarku, abu mafi daure kai anan shine ina tasan cewa auren contract kukayi? There is something fishy here" yafada yana zagaye dakin

"I can't believe ummy kallon mazinaci takemin a jiyan nan, kallon me lallata yanmata, ni... ni Ashraf" yafada cikin wani yanayi

"Dolene mu nunamata kuskurenta Ashraf wanda nan gaba ko wuqa akasamata a maqoshi bazata qara gigin yima wani qaxafi ba, qazafin zina ba qaramin abu bane musanmman ma akan Saudart kamilar mace... baiwar Allah, allah kadai yasan yadda zataji idan labarin nan ya risketa"

Shiru dakin yasake dauka kowa da kalar tunanin dayake.

Ringing din wayar sadeeq ne ta katse musu tunaninsu.

Zaro wayar yayi ya duba sannan ya dago ta kalli Ashraf daya lumshe idanunshi.

"Ashraf.. ummy ce" yafada yana maida kallon ga wayar kuma

Bude idanunshi yayi yazuba mashi kawai batareda yace komaiba.

Ganin kiran zai tsinke yasashi saurin dagawa yakara a kunne.

Sallama yafara yimata sannan ya gaisheta a ladabce.

Bansan kome tacemishi ba saiya dago ya kalli Ashraf da shima kallonshi yake yace

"Eh gashinan ummy"

Magana aka sakeyi tacan 6angaren sannan yace
"Insha allah ummy"

Katse wayar yayi ya maido kallonshi ga ashraf dake kallonshi haryanzu.

"Ka tashi mutafi"

"Ina?" Ya tambayeshi ahankali

"Ummy ke nemanmu tace takira wayarka ba'a dagawa" inji sadeeq yana nufan closet dinshi don zaro rigar dazai daura bisa singlet din jikinshi.

"Ban iyawa, bazan iya fuskantar ummy ba ahalin yanzu" yafada yana dafe kan dake saramashi

"Meyasa? Yanzu ne the right time dazamu fahimtar da ita komai tun kafin abu ya girmama, yau zatasan komai so stand up dalla" inji sadeeq yana dora shirt saman singlet din.

"Allah kadai yasan kallon datakemin yanzu, i swear sai suzy tayi nadamar zuwanta duniya" yaqarashe yana huci
Chapter 54 · 0% Book details