← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 111

Sashe 74

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai ashraf yayi kawai yana murmushi sannan yakoma wajen desk dinshi yana kaikaye stuff dinshi don lokacin tashin nasu yayi cikin zuciyarshi kuma yana wondering ina sadeeq ke zuwa yan kwanakinnan da rana don abin yafara damunshi, mutum kamar tsinke saidai ka nemeshi ka rasa?

Haka ya ida kammala kayanshi ya fito daga office din yanajin wani nishadi a zuciyarshi duk sadda yatuno muryar saudart dayaji dazu acikin kwanyarshi.

Shigewa yayi cikin motarshi ya tada yafice daga company din feeling very lively...✍

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)

082

Washegari jumua't babbar rana.

Ashraf ne da sadeeq cikin mota suna kan hanyarsu ta dawowa daga sallar jumu'a.

Sadeeq ne ke tuqi while ashraf na danne danne a waya.

Sosai ya shagala da abinda yake a wayar don bema lura da sadeeq ya dauki wata hanyar ba saida sukayi nisa sosai sannan ya ankara.

Kallon waje yayi yana yatsine fuska sannan yajuyo ga sadeeq yace
"And where are you taking us to?"

Ta6e baki yayi yace "sai yanzu ka lura"

"That's not the answer to my question" ashraf ya ansamashi yana harararshi

"Inda kake complaining ina zuwa zan kaika kaima" sadeeq ya amsa mashi yana shan wata corner

"Ina kenan?" Inji ashraf

"Gani ya kori ji" inji sadeeq batareda ya kalleshi ba.

Be sake cemashi komaiba sai maida hankalinshi dayayi kan wayarshi yana scrolling information on *how to make a girl fall for you* dayayi browsing.

Jin tsayuwar motarsu ya dawo dashi daga duniyar karatun daya lula, ajiyar zuciya ya sauke sannan ya dago idanunshi daga kan phone din yashiga bin inda suke da kallo cikin mammaki.

"Ina ne nan?" Yafada still yana bin harabar da kallo cikin mammaki

"Idanunka sun fara ciwone halan?" Inji sadeeq yana bude murfin kofar sannan yafita.

Shima fitowa yayi yana qara bin environment din da kallo.

"Waye be lafiya?" Inji ashraf yana kallon sadeeq

"Kaidai muje" inji sadeeq yana yin gaba.

Maida wayarshi a aljihu yayi sannan shima ya maramashi baya yana wondering waye be lafiya aka kwantar dashi asibiti.

Saida suka biya office din wani Dr sannan suka fito gabadaya da Dr din suka nufi wani ward, shidai ashraf binsu kawai yake batareda yasan wazasu je ganowaba.

A bakin wani ward suka tsaya Dr din yabude kofar yashiga sadeeq yabishi sai lastly ashraf da shima ya maramasu baya very eager to know what's happening.

Daga farko be dago wacece ba saida yakusan kaiwa bakin gadon sannan ya ganeta wanda hakan yasashi tsayawa cak daga tafiyar dayakeyi yana kallonta.

Itama kallonshi take agalabaice da alamu dai tana jin jiki ga wasu hawaye dasukayi forming a idanunta dasuka fada ciki.

Juyawa yayi batareda 6ata lokaciba ya nufi hanyar fita don baxai juri ganintaba don zuciyarshi wani irin suya take.

"My.... my please don't leave...please" tafada cikin muryar kuka.

Beko saurareta ba ya cigaba da tafiya harya isa bakin kofa yakama handle zai bude yaji tace
"Please don't leave without forgiving me, nasan mutuwa zanyi, please forgive me" tafada cikin kuka sosai.

Tsayawa yayi hannunshi kan handle din kofar batareda yajuyo ba.

Ganin hakan yasata cigaba dacewa

"Am so sorry my... na cuci kaina, beebah ta cuceni, nabiyewa son zuciya da hudubar muguwar qawa nafada hallaka, please forgive me"

Shiru yayi yana sauraronta zuciyarshi na zafi, duk ya tuna kazafin dataje tayimusu wajen ummy saiyaji kamar yaje ya shakureta a inda take.

Cikin sheshekar kukan dabai fita tacigaba dacewa

"Ashe beebah ba masoyiyata bace? Ta kaini ta baro, A.A nasan bani cikin mata masu kyawun hali, nasan bana cikin masu isashiyar tarbiyya.

Ashraf nasan kasoni ada, kasha yunkurin nunamini hanyar gaskiya amma nayi wasa da damata na 6ata wayauna na biyewa rudin qawaye da rayuwar turai na lallata alaqar dake tsakaninmu.

Ashraf tunda nafara ganinka a uk nakamu da matsanancin sonka wanda hakan yasa naji idan ba kaiba babu wanda zan iya rayuwa dashi amatsayin mijina.

Hakan yasani tattalin kaina da mutuncina don kai ganin kai kamili ne.

Duk iskancina ban ta6a wuce romance don nasa a raina kai kadai zanba kaina saboda na samama kaina mutunci awajenka bayan aurenmu.

Ranar daka ganni da chris muna kissing har hakan yayi sanadin rabuwarmu, aranar nashiga tashin hankali sosai kuma nadama tashigeni amma na nade tabarmar kunyata da hauka don ganin zan wulaqanta a idanun jama'a.

Daga lokacin natuba daga romance life saidai kaqi kabani wani damar.

Nabi duk hanyar danasan zanbi inshawo kanka amma kaqi saurarata.

Alokacin da labarin aurenka ya riskeni na shiga tashin hankali sosai.

Tun a lokacin naso tada bori amma beebah ta hanani acewarta asannu zamu warware komai.

Na biyemata nakuma yarda daita saboda duk duniya banida qawa kuma aminiya data fita.
Ita tayi convincing dina takaini wajen wani boka da nufin shiga tsakaninku kai da matarka yakuma cusa maka tsananin sona yadda zakaji bazaka iya rayuwaba batareda niba"

Shiru tayi sakamakon kukan dayaci qarfinta.

Izuwa yanzu ashraf yajuyo yana kallonta ya jingina da kofa hannayenshi harde da qirji shima sadeeq ita yake kallo shima jingine da bango.

Babu wanda yacemata uffan har taci kukanta mai isarta sannan ta tsagaita don kanta sannan tacigaba dacewa

"Bansan wannan ne hanyar lallacewar rayuwata ba, bansan kaini zatayi ta baro ba.

Ataqaice dai the man demand for my virginity domin samun biyan buqata ta.

Dafarko naqi yarda don banga amfanin auren ba bayan nayi loosing din abinda zai kankaromin mutunci awajenka ba amma sai sukayi convincing dina dashi da beebah cewa aikin da za'ayimaka bazai baka damar tantance am virgin or not ba, kawai dai burinka a lokacin ka mallakenine kuma bazaka ta6a barinaba har abada.

Ina sonka kuma banida burin daya wuce in mallakeka na har abada hakan yasa magangannunsu sukayi tasiri azuciyata nabada kai"

Sniffing tayi ahankali sannan tacigaba

"ranar nayi loosing pride dina ga dirty tsohon nan, nayi kukan takaici sosai saidai beebah na kwantarmin da hankali cewa yanzu you're mine forever.

Shiru shiru har aka kwashe wata banji alamun nasaraba saima canjin danakeji ajikina cos am always sick.

Hakan yasa na tsare beebah da qorafi nan ta kwantarmin da hankali tareda cemin akwaima hanya mafi sauqi dazamu warware aurenku batareda munjira bokanmu ba.

Nan tagayamin tasamu information awajen helen cewa aurenku is based on contract.

I was shocked alokacin don abin yazomun a bazata, nan na buqaci evidence tace tasa helen tasamo mana akan yarjejeniyar huge amount of money.

Hakan yasa nadanji dama dama saidai me? Bayan kwana biyu jikina yayi worsening.

Dakyar na iya kai kaina hospital inda aka gwadani aka bani result din daya giggita rayuwata.

Result ne na juna biyu wanda ya nuna inada jaririn ciki sai kuma cutar nan mai karya garkuwar jiki wato HIV/AIDS.

Ina gama karantawa na yanke jiki nafadi saidai nasake bude idanuna naganni akan gadon hospital.

Nayi kuka sosai nayi baqinciki marar misaltuwa.

Qarshe dai na lalla6a dakyar nakai kaina gidan beebah.

Sosai na burkuce mata don gani nake tawa tazo qarshe kawai.

Dakyar ta rarrasheni ta nuna haryanzu is not too late wajen mallakarka, ta fiddomin takardun datasamu wajen helen na yarjejeniyar aurenku takuma kitsamin yadda zan maku makirci wanda dolene umminka tasa ka aureni

Banida za6i, a lokacin banida kingin burin daya wuce in mallakeka kafin inmutu hakan yasa nazo har gidanku nayi maka kazafin danayimaka.

Bayan wannan ranar kuma zazzafan zazza6i yakuma lullu6eni ga laulayi daga qarshe beebah tabani shawarar terminating din cikin.

I dont have choice don alokacin inajin jiki sosai haka takawoni wannan asibitin don zubda cikin.

Wanda garin zubda ciki akasamu matsala mahaifata ta ta6u.

Tunda takawoni hospital yau kwana goma kenan ban sake ganinta ba, ina cikin matsanancin hali gashi tagudu tabarni, banida kowa, bansan ta ina zanfara contacting din yan uwana ba.

Beebah ta cuceni A.A, taci amana ta, tasani tafka kuskuren da bazan ta6a iya gyarawa ba.

Please forgive me ashraf, ka yafemin kona dan ji sauqin abinda ke damuna, ka yafemin ko allah zai sassautamin halin danake ciki" ta qarashe maganar cikin kuka sosai.

Shiru dakin yayi sai sheshekar kukanta kadai da akeji qasa qasa.

Sosai magangganunta suka ta6a ashraf, sosai tabashi tausayi kuma yaji har aranshi ya yafemata don bega amfanin rashin yafemata dinba.

Allah yasani ada yasota kuma yaso ya taimakamata wajen ganin ta gyara hallayenta amma the deed is done and it can never be undone.

Kallon Dr dake tsaye shima tundazu yayi sannan yace "A minute please"
Sannan yajuya yafita Dr din ya maramashi baya.

Hada kai da gwiwa tayi taqara fashewa da kuka mai cikeda danasani.

"Ehrm... please kibar kukan haka it's not good for your health, everything will be alright ok?" Inji sadeeq ahankali.

Saida yayi making sure tabar kukan sannan shima yafita waje yarufo kofar.

A corridor ya tadda ashraf tsaye hannayenshi zube a aljihu yana fuskantar Dr dake mashi bayyanin status din suzy.

Qarasowa yayi shima yana cigaba da sauraranshi har yakai aya.

Furzar da iska A.A yayi ahankali sannan yace
"So sad.. yanzu i think the best option here shine a sanar da familyn ta, koko?" Ya maida akalar tambayar ga sadeeq daya rungume hannaye a qirji.

"Yes abinda yakamata kenan" inji Dr

"Yanzu ya maganar bill?"

"Sir yayi settling din komai" dr yafada yana nuna sadeeq da beyi mgn ba haryanzu

"Alright please take good care of her, zamuyi qoqarin contacting din family dinta as soon as possible" yafada yana gyara tsayuwarshi

"Ok insha allah" inji dr din.

Nan sukayi sallama suka fita daga hospital din batareda sun sake komawa dakintaba.

Shiru motar ta dauka tunda suka baro asibitin.

"Tayaya kasan tana asibitin" ashraf ya jefoma sadeeq dake tuqin tambayar.

Dan kallonshi sadeeq yayi sannan ya ta6e baki yace
"I've been looking for her tun bayan faruwar abinnan don koyamata hankali, dakyar naganota nan din da taimakon wani neighbour dinta"

"And ina beeba ko mema take kiran friend din nata?"

"Babu inda ban nemeta ba, yanzu hakama nasa anaimomin ita duk fadin garinnan itakuma helen ta dade da barin garinma takoma qauyensu" sadeeq ya amsa idanunshi akan titi.

Ajiyar zuciya ashraf ya sauke yace
"To allah ya kyauta, yanzu ina zamu nemi familyn nata?"

"Suna jos, phone dinta ta 6atane kuma she doesnt wanna give any of her family number, guess tanajin kunyar suganta a wannan halin ne"
Chapter 74 · 0% Book details