← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 70 OF 111

Sashe 70

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka dai suka shigo gidan suna hira cikin raha da dariya shikau ashraf kanshi a qasa yake biye dasu sadeeq abayanshi sai faman danne dariyarshi.

Wannan karon saida duk suka dan ta6a abin motsa baki ana fira cikin raha da dariya idan ka cire ashraf da saudart da suka kasa dago kansu sai sadeeq dake gefen ashraf shima yanna tsokanar ashraf qasa qasa.

Sau biyu idanun saudart na hadewa dana ashraf duk dagowarta hakan yasa bata qara dagowaba.

Saida komai ya lafa sannan suka fara gabatar da abinda ya tarasu tun farko, anan kawu ibrahim yafara bada labarin asalin aurensu A.A da dalilinshi na qirqirar auren duk don ya dau fansa akan abinda yake zargin daddy dashi be 6oyemasu komaiba har zuwa yanzu dasuke zaune.

Shiru falon ya dauka, mammaki ne sosai yacika saudart don ko da wasa bata ta6a kawowa ranta Ashraf nada wata manufa gameda aurensu ba, she thought kawai irin mutanen nan ne da basu yarda suyi taimako batareda wani abu in exchange ba don ko rashin mutuncin dayakema daddy gani take kawai saboda giyar kudi dake dibanshi ne don tasan wasu mutanen kudi na maidasu rude brats. Ashe shi revenge yake taking.

Ahankali tad'an dago idanu ta saci kallonshi taga kanshi na akasa don tunda akafara maganar yakasa kwakwarar motsi, jiyake kamar ya 6ace ya huta.

Sauke idanunta tayi ahankali abinda takeji gamedashi naqara hauhawa yayinda kwakwalwarta tashiga tariyomata cin mutunci dayaimata ita da daddy.

Daddy kau a 6angarenshi shima yayi mammaki amma daga baya kuma saiya saki murmushi yana kallon ashraf daya wani raku6e waje daya kamar wanda ruwa ya cinye.

"Allah sarki son, ba laifinka bane, rashin sanine kuma rashin sani yafi dare duhu, konine a matsayinka idan banyi fin hakaba to iya abinda zanyi kenan, besides nima da nawa laifin da banda kwadayi da bazan yarda da hakanba da na hango wani abu makamancin haka amma lokaxin idanuwana sun rufe nakasa hango komai, Am sorry for putting you through pain son"

Qara yin qasa ashraf yayi dakai yana jin wani matsanancin kunya jiyake kamar ya ruga aguje yabar gidan gabadaya.

"Muhammad?" Daddy yakirashi da ainahin sunanshi

Kasa dagowa ashraf yayi

"Look at me son, ko baka yafemin bane?"

Girgiza kai yayi ahankali still be dagoba.

"Come closer son"

Shiru yayi yakasa motsawa, kowa na falon shi yake kallo harda saudart dake kallonshi ta qasan ido tanajin wani daci daci a maqoshinta.

Ahankali ya rarrafo gefen daddy ya zauna kanshi sunkuye

"Ashraf?"

"Am...sorry daddy, please forgive...me" yafada ahankali still kanshi qasa.

"Ni bakamin komai ba,if am in your shoe i'll behave exactly the way you did, am sorry too, forgive me too"

Shiru dai kawai yayi still kanshi qasa.

Ganin babu mai niyyar sake magana acikinsu yasa kawu ibrahim gyaran murya ahankali sannan yace

"To alhamdullilah, godiya ga allah subhanahu wata'ala daya sa muka fuskanci juna sosai ayau wanda idan kukayi duba ga wannan abu zakuga tsararrene wanda ubangiji ya tsara domin koyarda kowanne cikinmu darasi.

Nafarko da Alhaji shamsu be nemi taimako a kamfanin A.A ba da haryanzu muna cikin duhu gameda abinda muke zarginshi akai na sanadin margayi.

Nabiyu da Ashraf be dage akan daukar fansaba da bamuyi wannan zaman ba na yau

Da alhaji bai aminta da aurennan ba da haryanzu muna acikin duhu

Saigashi abun kamar a film, abinda yafaru shekara da shekaru anzo an warwareshi yanzu bayan babu wanda yata6a kawowa ko a mafarki zamu sake haduwa a duniyarnan.

Dama ance kana naka Allah na nashi gashi sanaddiyar auren nan na contract tsohon zumuncinmu zai cigaba daga inda ya tsaya insha allah.

Don koda auren nan ko babu auren nan bazamu ta6a watsar da zumuncinmu ba a karo na biyu kuma muna fatan insha allah zumuncinmu yacigaba da dorewa har qarshen rayuwarmu har izuwa cikin aljanna insha allah"

Juyowa yayi yakalli saudart da kanta ke qasa yace
"Haqiqa 'yata kin kasance diya abar alfahari ga kowa'anne iyaye, abun kwatance ga alumma, ki kasance mai biyyaya da tarbiya ga girmama na gaba dake.

Da watace taga yadda Ashraf ke wulaqanta mata iyaye da ko kallo nashi iyayen bazasu ishetaba amma ke kin kauda kai kin rungumi iyayenshi da danginshi kamar naki, kin kawo haske a rayuwarsu gabadaya kin ajiye komai kin taimakeshi a lokacin da yake buqatar taimako kuma ke kadaice keda ikon yin haka alokacin batareda kinyi la'akari da abubbuwan dayaimiki kuma yake kan yimaki alokacin, gaskiya you have a good heart kuma allah ne kadai zai iya saka maki, kin jure abubuwa dayawa saboda farantama mahaifinki rai haqiqa ke yar aljanna ce insha allah"

Dan dakatawa yayi yana kallonta kafin kuma ya cigaba dacewa
"Saudart you've endure enough, kin juri abubuwa dadama akan wannan auren bazamu tilastaki da cigaba da zaman cutuwa ba.

You have a choice, aurennan zai dorene bisa ga kalar amsar da kika bada, karki cuci kanki daughter, ada kin amince ne saboda daddynki yanzu kuma nobody is forcing you, your fate is in your hand kuma munaso ki sane ko da aurennan ko babushi babu abinda zai canza alaqarmu daku don haka choose wisely daughter"

Shiru dakin ya dauka all eyes on Saudart while ashraf kanshi a sunkuye zuciyarshi na bugu abnormally.

"Daughter? Ni mahaifiyar ashraf ce amma dana ji abinda yafaru the first thing dayazo bakina shine yabani takardarki don nasan you've suffered enough, ba don su kawu ibrahim sunsa bakiba akan abari aji ta bakinki da wlh bazamuzo nan ba saida takardarki, ni na haifi ashraf kuma nasan halinshi idan ya tsani abu don haka karki cuci kanki don farantawa kowa saudart, ki tuna this is your life bana kowaba, idan kin cigaba da zama dashi don wani to kanki kika cuta, just pour what's in your heart daughter, fear nothing"

Shiru dakin yasake dauka saudart ko motsawa batayiba shima ashraf haka saidai kowanne bugun zuciyarshi ya chanza sosai.

"Saudart?" Kawu ibrahim ya kira sunanta ahankali.

Ahankali ta dago kanta ta kalleshi saikuma ta maida kanta qasa

"Zaki cigaba da zama da Ashraf a matsayinshi na mijinki daga auren contract zuwa auren gaske na har abada koko ya sawwaqe maki Allah ya hada kowa da abinda yafimishi alhairi? Remember your fate is in your hand" yaqarashe a tausashe.

Tsit falon ya dauka kowa idanunshi akanta, zuciyoyin kowa na qara bugu musanmman na goganku😄 sadeeq kau harda share zufar daya tsatsafo mashi a goshi😆

Motsi tafara yi da baki amma maganar taki fitowa kallo daya zakamata kasan bata cikin nutsuwa.

Dafa kafadarta ummy tayi ahankali tace "keep calm daughter, just pour your mind"

Lumshe idanu tayi tana sauke ajiyar zuciya yayinda komai daya faru daga haduwarsu da ashraf har kawo yanzu yashiga yawo a kwanyarta.

Ahankali ta rufe idanunta ta bude bakinta dakyar tace...✍

Kusani a prayers fans👏

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)

079

Ahankali ta rufe idanunta ta bude bakinta dakyar tace
"Allah yasa hakan shiyafi alkhairi" tafada cikin sanyi sosai

Tsiit falon ya dauka na wucin gadi don kasa gane inda maganarta ta dosa sukayi.

Kawu ibrahim ne yayi karfin halin cewa
"Me hakan ke nufi daughter?"

Shiru tayi kanta aqasa takasa cewa komai.

"Kinga saudart ki bude baki kiyi magana, this is something serious" inji Abba

Shiru tayi har lokacin kanta aqasa sai idanunta dake forming din hawaye.

"Saudart kin yarda xaki cigaba da zama da Ashraf a matsayin matarshi ta sunna na har abada?" Inji daddy yana kallonta keenly trying very hard to read her mind

Gyada kai tayi ahankali batareda ta dagoba.

"Ba maganar kurame zakiyi ba, open your mouth" inji abba

Ahankali ta bude bakinta trying very hard to control her emotion

"Eh abba, na....amince"

Shiru falon yadauka kowa na kallonta unbelievable

Babu wanda amsarta beyi shocking ba don basu ta6a tsammanin wannan amsarba.

Ashraf kau kasa gasgata kunnuwanshi yayi, amsarta kawai ke eoching a kunnuwanshi jiyake kamar amafarki.

"Karya kike saudart! This is not coming direct from your heart" inji ummy cikin dan daga murya

Kasa dagowa saudart tayi bare ta lalubo amsarda zata bata.

Yes, amsarnan is not directly from her heart don babu abinda zuciyarta ke muradi kamar rabuwa da ashraf, she hate him and today she hate him more, jin cewa duk abubuwan dayake musu fansa ne yaqara dagula mata lissafi yasata jin bazata ta6a yafemashi ba, yasata jin qara tsanarshi a zuciyarta.

Ta tsaneshi ta tsaneshi saidai wannan kalmar saidai ta tsaya a cikin zuciyarta, jitake inama tana iya furtawa, tasan furtawan kawai zai rabata dashi har abada amma kash! Bazata iyaba.

Ada babu abinda take buqata irin wannan damar, damarda xata rabata dashi na har abada, kullum cikin addu'a take allah ya kawo rabuwarsu, yarabata da wannan mutumin da babu digon sonshi ko diss a zuciyarta, saigashi damar tazo amma wani abu yayimata katanga da samun cikar burinta, tana ji tana gani zata amince da abinda xuciyarta bataso, xata zauna zanan cutuwa, xata za6i rayuwar qunci da baqinciki.

"Saudart look at me!" Ummy ta umarceta.

Saida tayi iyakar qoqarinta na ganin ta maida hawayen dake maqale a idanunta tundaxu taqi basu damar sauka don tasan sune zasu fallasa asirin zuciyarta sannan ta dago tana kallon ummin

"Tell me, wake tilastaki yanzu? Ni da ke munsan ba gaskiya kike fadi ba"

Ahankali tashiga girgiza kanta trying so hard to control herself

"Ummy babu mai tilastani, this is coming directly from my heart.."

"Karya kike" ummy ta katseta

"Saudart kinsan abinda kike shirin yi kuwa? You are depriving yourself your right" tafada wholeheartedly

"No ummy, inayin abinda kuka sanine, kunce infadi ra'ayina batareda nayi considering din komai ba and that's exactly what am doing, it's my choice ummy" tafada calmly yayinda zuciyarta ke fadin akasin haka

Shiru ummy tayi tana kallonta kawai, kallo ne na mammaki chakude da tausayi, tasan karya take, gashinan tana hango hakan acikin idanunta, meyasa zata za6i quntatawa kanta, meyasa xata za6i zaman cutuwa? Zaman da babu digon so aciki?

Shidai ashraf haryanzu yakasa dagowa kuma haryanzu jinshi yake kamar a mafarki, kai mafarki ma ne, yarinyar da ta tsaneshi, batada wani buri daya wuce rabuwa dashi zata amincewa cigaba da zama dashi na har abada? This is a dream, mafarkin da bazaiso ya farkaba yanzu.
Chapter 70 · 0% Book details