← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 111

Sashe 57

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shima babu laifi ansha shagalluluka kala kala, Ashraf kau saboda farinjini fatima har rasa hannun wa yake don beda qiwuya ko kadan da yaga saiya 6angale mashi baki yana miqo hannu alamun yanason adaukeshi, hakan yasa Fatima bata ganinshi sai ya buqaci abinci sannan za'a kawoshi ta shayar dashi akoma dashi.

Saida sukayi sati sannan suka juyo kano wanda tun washegarin biki Alhaji Auwal dama yayi gaba sukuma saida suka zagaye dangi sannan suka taho.

Haka rayuwa tacigaba da kasancewa.
Ashraf ya taso cikin gata da soyyaya tako wane 6angare saidai duk gatan dayake samun hakan be hanashi samun inganttaciyar tarbiya ba don duk yadda suke dashi idan yayi ba daidai ba suna tsawatar mashi kuma suyimashi nasiha.

A 6angaren arziqin Alhaji Auwal kuwa sai abinda yayi gaba don yanzu yabar tuqi yakoma harkar shinkafa kawai, mottocinshi basu qilguwa kullum cikin busy yake yazama babban dan kasuwa.

Tun bayan haihuwar Ashraf *Ummy* kamar yadda Ashraf ke kiranta bata qara haihuwa ba sai 6arin datakeyi akai akai wanda sunyi maganin amma a banza.

Da farko Alhaji Auwal (Abbu) yaso ajuya mahaifarta saboda wahalar dayaga tanasha amma saita qiya acewarta abarta ahaka haka allah ta tsara mata.

Ashraf nada shekara biyar Abbu tabiyama inna, inna Raliya, ummy, inna jamila da zainab matar Nura hajji suka dunguma sukaje suka sauke faralli.

Bayan dawowarsu da yan wattanni akasama Alhaji shamsu biki dawata shuwa Arab ta garin borno.

Acikin wannan lokacin ciwon zuciyar Inna yatashi sosai babu wata wata Auwal ya daukota takawota asibitin kano aka cigaba da bata kulawa saidai dayake lokacinta na kusa kwana biyar tayi tana jinya ta rasu.

Sosai mutuwar ta girgizasu don sunyi kuka marar iyaka.

Haka suka dauki gawar suka juya wudil don Inna tabar wassiya idan tamutu koma inane a maidota wudil arufe don tafison arufeta a mahaifarta.

Bayan sati biyu suka dawo kano rayuwa tacigaba da tafiya.

Izuwa yanzu ansaka Ashraf makarantar primary ta private kuma allah yayimashi qwalwa da basirar daukar abu don shike ciwo nadaya a ajin duk qarshen term

Ba'a dadeba bikin Alhaji shamsu ya matso nanfa sukaita shirye shirye babu kama hannun yaro.

Duk tare suke komai da Alhaji Auwal don bawani dangi ke gareshiba sosai sai tarin abokan arziqi da abokan kasuwanci.

Gaggarumin biki akayi nagani na fada inda babu laifi ansha shagulgula sosai sannan aka kawo amarya khadija dakin mijinta.

Haka rayuwa tacigaba da tafiya Ashraf sai qara girma yake da wayau, arziqin Abbu sai qara hauhawa yake allah nasa mashi albarka hakan yasa yakeda maqiya da mahassada masu hassada dashi a6oye batareda yasaniba.

Bayan shekara daya da aurensu Alhaji Shamsu sai Allah ya azurtasu da samun diya mace kyakyawa sak uwarta.

Alhaji shamsu baki yaqi rufuwa don murna, ranar suna na zagayowa aka radamata sunan *SAUDATU*

bayan haihuwar da 'yan wattani su Alhaji shamsu da matarshi khadija suka fara samun matsala atsakaninsu sanaddiyar sata dayayi acire mata mahaifarta wai diya daya ta ishesu acewarshi 'ya'ya talauci suke jawowa.

Firr khadija taqi yarda acewarta bazai sata ta kashe kanta da rai ba, tun suna abin a tsakaninsu har yakai kunnen Abbu kasancewar Khadija tagayamashi ko zata samu yanunama Alhaji shamsu daidai.

Abin yaba Abbu haushi sosai saiyaje yasamu Alhaji shamsu har company dinshi yayimashi magana shikuma sai abin ta hassalashi sosai ganin wai khadija takai qararshi wajenshi kamar wani ubanshi.

Nanfa Alhaji shamsu yafara zazzaga bala'i ta inda yake shiga batanan yake fitaba, aranar dakyar Abbu yafito company din rai 6ace abinda beta6a faruwaba a tsakaninsu.

Shikuma Alhaji shamsu yana komawa gida yarufe khadija da fada ta inda yake shiga batanan yake fitaba yace kuma cire mahaifa dole ayi muddin tanason cigaba da zama dashi.

In taqaice muku dai saidai auren yamutu da abu yaqi dadi wanda hakan ba qaramin 6ata ran Abbu ba yayi.

Wannan karon har gida Alhaji Auwal ya tadda Alhaji shamsu sukayi tatass inda daganan abotarsu ta shekara da shekaru ta watse.

Ummy sam bataji dadin hakanba amma ya suka iya?

Kan kace me? Har labarin 6atawarsu ya zagaye koina da aka sansu, mutane sai jimamin abun suke yayinda wasu suke farinciki akan haka.

Shekara daya da faruwar wannan al'amari Ummy tasake samun juna biyu lokacin shekarar Ashraf takwas kenan.

Sosai cikin yabata wahala sannan tasamu ta haifeshi bayan tasha baqar wahala tasamu diya mace sak Ashraf saidai bata ida kamoshi a haskeba.

Zokaga murna wajen Ashraf don sosai yake sha'awar qane ko qanwa dama.

Ranar suna na zagayowa akasamata sunan margayiya Inna wato AMINATU amma ana kiranta da *Baby*

Ana haka bikin zaharadini yataso inda ya auri yar kano suka tare a gidanshi da shima yagina a unguwar.

Kwanci tashi ba wuya, baby anfara girma don harta shekara biyu wanda yayi daidai da shekarun ashraf goma da wattanni.

Har a lokacin Abbu basa ga maciji da Daddy, sun watsar da zumuncinsu don ko labarin juna basaji.

Ana haka watarana Abbu na zaune cikin iyalanshi zaharadini ya bugo mashi waya kome yacemishi oho? Saiga Abbu ya zabura zaune har yana qwarewa da abinci

Cikin sauri ummy ta bashi ruwa suna jeramashi sannu ita da yaran.
Saida tarin ta lafa sannan ta tambayeshi lafiya? Yace ba lafiya bari yaje yadawo.

Haka ya fice be ida qarasa abincinba wanda itama ummy kasa ci tayi sai barosu ashraf datayi a dining tadawo falo tazauna tana addu'ar allah ya jiyardasu alhairi.

Acan kau Abbu yashiga tashin hankali marar misaltuwa don duka mottocinshi jami'an custom suka kame da abinda suka dauko.

Babu yadda beyiba wajen ganin an sakarmashi su amma abu yaci tura kai daga baya ma har gidanshi jami'an sukazo suka watsamashi komai suka 6alle store dinshi suka kwashe shinkafa ko taci basu bariba.

Wannan cin zarrafin baqaramin qonama Abbu rai yayiba don gani yake wannan cin fuskane babba.

Be ida shiga tashin hankaliba saida yaji cewa tsohon abokinshi kuma amininshine ummul aba'isan faruwan wannan lamarin.

Sosai abun ya dakeshi wanda har saida yakwanta ciwo.

Alokacin zaharadini ne yake taimakonsu dana magani don yadda kasan daukewar ruwa hakan komai na arziqin Abbu ya qare.

Magani akema Abbu amma kamar qaramashi ciwon ake.

Kullum cikin ambaton sunan Shamsu qolo yake yana hawaye.

Sosai su ummy dama kingin danginshi suka shiga tashin hankali akoda yaushe ummy da ashraf dashima yafara sanin komai cikin kuka suke saiya kasance Ashraf yakasa mance sunan da abbu ke yawan maimaitawa yana hawaye. Abinka da yaro saiya riqe sunan gamm a kwakwalwarshi yayinda yakema mammalakin sunan tsana wacce bata misaltuwa.

Saida Abbu yayi sati biyu sannan Allah ya dauki ranshi, mutuwar da ta girgiza jama'a da dama kar ummy ma taji labari.

Haka dole akamashi sutura jama'a takoina ancika unguwar danqam suka rakashi aka kaishi gidanshi na gaskiya.

Su ummy basu tashi gane kurensu ba saida duk aka watse nan fa talauci ya kunnomasu kai.

Gashi dama zaharadini yake dan taimakawa to shima yanzu babu mota hannunshi kuma kamar hadin baki kowa yaqi bashi dukda kau mutuncin da mutanen keyi da margayi Auwal dayake raye.

Hakan yasa yakoma kasuwa yana tsaron shago wanda abinda yake samu bewani taka kara ya karya ba.

Ganin haka yasa ummy ta tuntu6i zaharadini akan asiyarda gidan dasuke ciki su siya qarami kingin kudin saisu jujjuya.

Saida zaharadini ya tuntu6i yayyanshi na wudil saboda hadin kai irin tasu suka kauyi maraba da hakan don suma basujin dadin halin da iyalan dan uwan nasu yake ciki kawai don basuda halin taimakawa ne.

Kan kace me? Har an saka gidan kasuwa aka kau siyeshi da daraja, zaharadini ya samarmasu dan qaramin gida a unguwarsu suka zauna ya miqamata kingin kudin inda taqi amsa tace yaje yaita jujjuyawa kawai.

Shima qin yarda yayi har saida magana taje gasu Kawu ibrahim nan shima kawu ibrahim yayi na'am da shawarar Ummy kan zaharadini ya juyasu tunda shima kusan beda sana'a yanzu tsayyaya albashi sai aba ummy wani kaso acikin kudin itama tafara business.

Hakan kau akayi, zaharadini yaje ya sari kayan kitchen da kudaden yayi hayar shago acikin kasuwa itakuma ummy tafara sana'ar saida kayan humra da turrarukan wuta wanda Allah ya dubi maraicinsu yasamasu albarka aciki.

Ashraf da tuni ancireshi daga makarantar kudi don yanzu tafi qarfinsu aka maidashi ta gomnati yazana common entrance dinshi yakau fito da result mai kyau yasamu admission awata makarantar gomnati ta secondary.

Ashraf yanada hazaqa sosai kasancewar yasamu good background a makarantar primary dinsu kasancewar private ce.

Ahankali yafara suna don ashraf akwai qoqari da saurin fahimta don shike topping din class dinsu duk term.

Bayan haka ga baiwar kyau da Allah yabashi don kallo daya zakamashi kasan ya hada jini da fulani.

Ganin yadda ake sonshi ake kuma lilliqemashi yaja ashraf tsirowa da halin jinkai da miskillanci.

Yaga daman kana mashi magana saiya mula yasha iska sannan ya amsa a dage.

Haka yan aji ke fama dashi musanmman masu liqemashi ya koyamasu karatu, bazaiqi koyamusu ba amma saiya wanasu son rai ya shamusu qamshi sannan ya koyamasu hakan kuma be 6atamasu rai don su shan qamshinshi ma burgesu yake don komai yake kyau yake musu.

A ss1 suka hadu da *SADEEQ UMAR* the mathematician kamar yadda aka samashi suna a school din.

Duk aji daya aka sasu kuma ga lokacin basusan junaba don sadeeq transfer akayi mashi yayi junior waec a school din, sai ya kasance dukkansu sun hadu a commercial class.

Da farko gaba da kishi suka farayi dajuna kasancewar kowa na taqama shi genius ne.

Ashraf yafishi qoqari a sauran subjects din irinsu biology, english, business studies da dai sauran subjects din da babu calculation saidai sadeeq ya dokeshi a calculation don yadda kasan aljani haka ya iya lissafi hakan baqaramin 6ata ran ashraf yakeba don yasaba shine agaba a komai.

Hakan yasashi yin kishi da sadeeq musanmman idan yaga students naxuwa wajenshi solving din lissafi.

Shima sadeeq lura dayayi da yadda ashraf kemashi wani gani gani yasashi kama kanshi yanuna besan da wanzuwarshi ba.

Haka fa akacigaba da competition tsakaninsu kowa nason gwadawa dan uwanshi iyakarshi.

Saida suka shiga ss2 suka shirya shima sadeeq ne yanemi suyi abota don harga allah ashraf na burgeshi.
Chapter 57 · 0% Book details