← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 111

Sashe 76

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau thursday, suna zaune a falo dukkansu mamy na waya, saudart kuma da abdul da habeeb na baje qasa suna buga game, su aminu kau basu gidan suna gidan granny (mamansu Abba)

Dan ihu habeeb yayi ahankali gudun kar mamy dake waya taji yayiwa saudart gwalo yana maida fuskarshi puppy face.

Kallon juna saudart da abdul sukayi suka 6ata fuska tare.

Dauke papern game din abdul yayi ya cikwikwiyeta yana cewa
"Dama don kaga kai kadai ka iya shiyasa ka nace ayi to munfasa mu buga ludo"

Dariya habeeb yafashe daita yace
"Nadaiyi winning dinku, taar! Imagine ku biyu akan ni daya amma naciku 5:0 shame!!"

"Don dai bamu iya bane yaro da shi kadai ya isheka" inji saudart tana harararshi

"Me wannan ajebon ya iya banda shirme?" Inji habeeb yana fashewa da dariya don ya qule abdul

6ata fuska abdul yayi ya kalli saudart kamar zaiyi kuka.

"Habeeb banson wulaqanci, mind yourself" tayi warning din habeeb tana gallamashi harara.

Sunkuyar dakai yayi yana dariya qasa qasa ganin yadda abdul din keta rau rau da idanu hawaye harsun taru a idanun.

Sallamar megadi ne ya katsesu.

Duk kallon kofar sukayi harda mamy da tagama wayar sai danne danne datakeyi.

"Habeeb get the door" inji mamy tana maida kallonta akan wayarta.

Tashi yayi yawuce yayinda saudart ta ciro wayarta zata shiganma abdul game din ludo kamar yadda yace.

Adan jima kadan saiga habeeb yadawo dakin.

"Mamy baqine" inji habeeb

"Who?"

"Don't know sundaice inzo ince zasu shigo gaidaki"

Kallon juna saudart da mamy sukayi sannan mamy tace "ok saudart jeki daukomin mayafi na, abdul tattara rubbish takardun nan kayi sama"

Tashi saudart tayi tanufi upstairs dakin mamy while abdul ya tattara takardun games din hannunshi riqeda wayar saudart dayake game daita.

Can saiga saudart da mayafin mamy ta bata tajuya takoma sama abinta.

Kallon habeeb tayi dake tsaye tundazu bayan tagama yafa mayafin tace
"Jeka shigo dasu"

"Tou" yafada yajuya don shigowa dasu din.

Ajikin motarsu ya taddasu tsaitsaye, qarasowa yayi yana murmushi yace
"Mamy tace kushigo"

Shafa kanshi sadeeq yayi yace "alright good boy muje"

Habeeb yayi gaba sadeeq yabishi.

Saurin kamo hannunshi A.A yayi yana wiqi wiqi da idanu kamar marar gaskiya.

"What" inji sadeeq daya juyo yana kallonshi cikin takaici.

"Please sadeeq, am shy" yafada cikin marairaicewa

Tsaki sadeeq yaja cikin takaici yace
"You know what? Idan najuya nabar gidannan natafi kenan wlh, wannan wane irin wulaqancine, ka tilastamani rakoka kuma kazo kana behaving annoyingly? Haka kabani kunya wajen daddy agidanshi dazu, kasan bazaka iya zuwaba ka jiji6oni?" Yafada yana harararshi

"Mtcheew yanzu am sorry muje, wai maimakon ya kwantar ma mutum hankali saiya rufe mutum dafada"

"Hankalin ya dade be tashiba, yafi rocket tashi" inji sadeeq.

Wuceshi ashraf yayi cikin fushi yanufi habeeb da harya kai bakin kofa.

Binshi shima sadeeq din yayi yana harararshi yana gunguni qasa qasa.

Koda yakai bakin kofar kasa shiga yayi saida yajira sadeeq ya iso sannan.

Harara sadeeq ya gallamashi sannan yasa hannu yatura kofar ahankali yana sallama.

Shima ashraf daduk yake very nervous ya maramashi baya shima yana sallamar.

Akan kujera suka tadda mamy zaune fuskarta asake tana amsa sallamarsu tareda yimusu sannu dazuwa.

Ahankali suka qaraso cikin falon kansu a sunkuye suka zauna kan carpet suna fuskantar mamy.

"A'a? Ku zauna kan kujera mana"

Duk murmushi sukayi kansu a sunkuye suka shiga gaidata batareda sunyi yadda tace dinba.

Amsa musu tashigayi tana kallonsu most especially ashraf don kallo daya tayimusu tagane kosu waye.

"Ya mutanen gida? Ya aiki?" Inji mamy

"Alhamdulillah, yasu Abba" inji sadeeq yana murmushi shikau ashraf kunya ta hanashi cewa komai sai sunkuye kai dayayi kawai yana sauraronsu.

Amsamasu tayi da yana wajen aiki be dawoba.

Saida suka gama gaishe gaishen sannan mamy ta tashi tsaye ta kalli habeeb dake zaune can gefe yana qoqarin chanza channel ta 6allamashi harara a fakaice tace
"Zoka kaisu falon baqi"

Tasowa yayi yazo wajensu ya tsaya, tashi duk sukayi suna yimata sallama tana amsawa cikin fara'a tanacewa su gaidamata Hajiya fateema idan sun koma sannan itama tajuya tahau sama bayan sunfita.

Wani gauron ajiyar zuciya ashraf ya sauke bayan sun fito yana dafa chest.

Harararshi sadeeq yayi yace "matsoraci kawai"

Shima hararar ya rama batareda yace komaiba sukabi habeeb dake gaba don kaisu falon baqin.

Kwankwasa kofarta da akayi yasa tadago daga linkin kayan datake, kafin tace komai har mamy ta bude kofar tashigo.

Murmushi saudart tayi mata tace
"Har baqin sun tafi?" Tafada tana ajiye zanen data linke.

Fuska ba yabo ba fallasa mamy tace
"A'a kije suna falon baqi and kitafi da refreshment"

Dan waro idanu saudart tayi tace
"Nikuma mamy?" Tana nuna kanta da yatsa.

Wata harara mamy ta gallamata tace "no ni, zakiyi abinda nacene ko kuwa? And change into something more decent kuma karkiyi wasting dib time" tana kaiwa nan tafice tabarta sake da baki.

Asanyaye ta maida kayan data linke cikin sip dinta sannan taciro wata dark blue din hijab doguwa ta dora kan kayan jikinta tadan gyara fuskarta ta fesa cool turare sannan tafita.

Bata tadda kowaba falo hakan yasa tanufi kitchen tadauki tray ta bude fridge tafiddo drinks uku ta daura akai da cups ma uku don batasan adadin baqinba ta debi snacks ma sannan tafito kitchen din tanufi falon baqi.

Tafiya take tana tunani nason gano su wanene, haka kawai taji beating din zuciyarta na chanzawa. She feels very nervous and uncomfortable.

Koda takai bakin kofar saida tadanyi jimm na yan daqiqu sannan ta daga hannu ahankali tayi knocking sannan ta tura kofar bakinta dauke da sallama.

Sadeeq kadai ya amsa sallamar while ashraf da muryarta ta saukar mashu da wata iriyar kasala ya kafe kofar da idanu cikin son ganin ta inda zata 6illo.

Anitse tashigo dakin kanta qasa tana sake maimaita sallamar datayi hannunta riqeda tray.

Lumshe idanu ashraf yayi akanta ya bude jin wani sanyi na ratsa zuciyarshi by the mere sight of her...✍

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️
[9/1, 11:13 PM] Hayat: 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)

084

Wannan karon ma sadeeq yasake amsa mata sallamar cikin fara'a.

Dumm.. gabanta yafadi jin muryar sadeeq wanda hakan yasata dago idanunta don ganin ko kunnenta ke decieving dinta.

Caraff suka hada idanu dashi wanda dama tunda tashigo idanunshi ke kafe daita.

Saurin janye idanunta tayi gabanta beating sosai don ba qaramin kashemata idanu idanunshi sukayi ba, there is something about his eyes dake sata jin takasa kallonsu na lokaci mai tsayi.

Ahankali tashiga takowa falon kamar mai kirgan steps making extra sure bata harde ba don sosai take jinta a takure jin piercing idanunshi akanta.

Saida tafara ajiye tray din hannunta akan centre table din dakin sannan takoma can kujerar dake fuskantarsu ta zauna ta sauke kai qasa tana wasa da zira ziran yatsun hannunta.

"Good afternoon ranki shi dade" inji sadeeq cikin barkwanci.

Dan murmushi tayi na kunya don sosai takejin kunyar sadeeq yanzu musanmman idan ta tuna abinda yafaru haduwarsu ta qarshe

"Ina wuni?" Tafada ahankali batareda ta dagoba.

"Lfy lau, ya gida ya hutu?" Yafada yana satar kallon ashraf daya maidata mirror tsabar kallo

"Alhamdullilah" ta amsa a taqaice

Dan shiru falon ya dauka ganin hakan yasa sadeeq miqewa ya nufi centre table din yana cewa
"Bari kuga"

Dan daga idanu tayi qasa qasa tana kallonshi taga ya dauki drink daya ya debi snacks din kadan a wani dan plate sannan ya miqe.

"Tohm ni nayi nan" yafada yana nufan kofar fita ya fice.

Dakin ne yadauki wani deadly silent, bakajin ko kwakwaran motsi aciki.

Kanta haryanzu na aqasa tana fidgeting din yatsunta duk jinta take atakure kamar tasa kuka takeji.

Shikau maidata t.v yayi yana kallo, Allah knows yayi missing dinta, jiyake kamar yayi shekaru be gantaba, jiyake kamar su dawwama ahakan tana gabanshi yana kallonta, yarasa dalili kawai shidai yanajin wani irin farinciki ne idan yana kallonta.

Everything about her is different, fuskarta, shigarta, qamshinta, muryarya, everything! He's in love with everything about her.

Muskutawa tayi ahankali tadan gyara xama uncomfortably, allah ma yasan a mugun takure take, jitake kamar ta tashi ta fita, me yake nufi da yazo ya tusata gaba kamar mirror yana kallo? Meya kawoshi ma at the first place?

Ahankali ta dago idanunta da niyyar satan kallonshi

Gaurayewa idanunsu suka sakeyi a karo nabiyu ya sakarmata one of the coolest smile dinshi.

Saurin sauke idanunta tayi qasa tana dan runtsesu cikin kunyar hada idanun dasukayi.

Ita dayasan yadda takeji idan yana kallonta da wannan idanun da ya bari, kwata kwata bata sonsu, suna sata jin wani iri.

Wannan zaman nasu ya tina mata da zuwan dayayi gab da bikinsu, exactly kamar irin wannan saidai wancan bemata irin wannan kallon hasalima hankalinshi nakan waya while yanzu yawani tsareta da idanu kamar tsohon maye.

"Good afternoon" yafada cikin wani irin cool voice wanda hakan yasata dan dagowa da nufin satan kallonshi.

Hada idanu sukayi again tayi saurin janyesu ta kalli gefe sannan ahankali almost in rada tace
"Same"

Murmushi yayi sannan ya miqe yafara takowa wajenta.

Bugun zuciyarta ne yafara qaruwa jin kamar takunshi na kusantota.

Daidai centre table din ya tsaya ya dora hannu akan drink daya yana kallonta, sannan ahankali yace
"Should I?"

Qin dago kanta tayi ta kalleshi don batason qara hada idanu dashi ta daga kai ahankali tanajinta duk a takure.

Murmushi yayi ya bude drink din idanunshi a kanta ta tsiyaya kadan a glass cup din sannan yamaida ya rufe ya dauki glass cup din.

Maimakon yakoma mazauninshi saiya dawo kujerar dake gefenta ya zauna irin zaman balancing dinnan daya riga ya bi jikinshi ya kai cup din abaki yana kur6a idanunshi akanta.

Ji saudart tayi kamar ta dora hannu aka taita ihu, jitayi tafi dazu takura dukda akwai dan tazara tsakanin kujerun nashi.

Wani haushi takeji na kafeta da idanun dayakeyi, wannan kallon ko maye albarka, why zai tisata gaba kamar t.v ya takurata da wadannan mayun idanun nashi?

Dan kawar da kai tayi dayan gefen fuskarta a hade tanajin kamar ta tashi tabar dakin.

Haka suka qaraci zaman nasu in silent kowa da saqe saqen dayake a zuciya. Basu san iya lokacin dasuka daukaba ahakan sai jisukayi anyi knocking din kofa wanda hakan yayi sanadiyyar dawowar dukansu daga dogon tunanin dasuka lula.
Chapter 76 · 0% Book details