← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 111

Sashe 14

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"To yanzu nizanje in tunamashi abinda yakamata yayi? Yafini sani ai"

"To ai shima kai yake jira, jai zaka tura asa rana ko?"

"Babu inda zan tura"

"Mtcheew, wani sa'in idan kayi wani abun kamar aita dukanka"

"Go ahead ai kana iya dukan nawan ma"

"Yanzu dai tell Ummy kasamu wanda kakeso atura Ayi magana aure kakeso"

Wani mugun kallo ya watsa mashi

"Are you kidding me?"

Dariya Sadeeq yayi yana cewa

"Allah ya yayema wannan dabi'ar, Harara kamar tsohuwar faruwa"

Bugu Ashraf yakai mashi yayi saurin kaucewa yana dariya

"Get out"

"Naji Amma wlh kayi yadda nace"

"Bazanyiba idan kai bakada kunya ni inada"

"To kunyatu, ya za'ayi kenan?"

"Ta inda aka hau tanan za'a sauka"

"Meaning?"

"Bansaniba"

"To nima ban ganeba"

"Kar Allah yasa kagane"

"Amin Amma.."

"Out!"

Yabude baki zai sake magana ya katseshi ta hanyar Jifanshi da pen

"Out!!"

Da dariya yafice office din.
Shima murmushi yayi yana girgiza kai, Sadeeq? Ciwon kai.

Shiru yayi yana tunanin maganar da Sadeeq yafada mashi yanzu

'Eh auren nan kawai zaisa Suzy tabar liqemashi, dolene Ayi auren kusa kusa don yaji dadin fara daukar fansa akan babban maqiyinshi.

******************************************

Su baby ankoma gida an Tisa Ummy gaba sai zubamata surutu suke suna bata labarin Saudart da kirkinta, nan suka shiga nunamata hotunan dasukayi, Masha Allah kawai Ummy ke fadi saboda ba qaramin shiga ranta yarinyar tayiba, kallo daya zakayimata kasan tanada nutsuwa.

Nan suka fiddo snacks din sunaci suna santi harda Ummy, sosai ta qagara itama ta ganta.

Da daddare fa group din CLASSIC LADIES ya qara hargitsewa saboda pics din da baby ta tura Wanda sukayi a bakery dazu Kowanne da caption dinshi, nanfa akayi caaa kowa na fadin albarkacin bakinshi.
Masu yabawa na yabawa Masu kushewa na kushewa, yan a la6e gefe asha dariya nayi.

Duk abinda ake Suzy Nagani, baqinciki kamar tayi bindiga.

Haka taita zooming din hotunan Saudart tana bin kowane lungu da saqonta da kallo, takaici fall zuciyarta.

*****************************************

Kwance take kan gadonta ruff da ciki ta tada kai da tafikan hannayenta tazubama wani littafi idanu tana karantawa.

Sanye take cikin pink din Kayan barci Riga da Wanda iya gwiwa, sai hular net dake kanta itama pink.

Kallo daya zakayi mata kasan littafin yayi mugun tafiya da hankalinta don sai murmushi take saki, tana jinjina kai alamun dramar da ake ciki na qayyatar daita.

Ringing din wayarta ya dawo daita Daga duniyar karatu.

Jawo wayar tayi taduba mai kiran.
SWEET MUMMY taga na yawo a screen din wayar.

Dagawa tayi ta kara a kunne tana mirginawa tsakiyar gadon.

"Mamyna"

"Na'am Angel"

"Ina wuni mamyna?"

"Lfy lau, ya aiki?"

"Alhamdulilah mamyna, yaya wajensu Abdul baseet?"

"Hmm Abdul baseet ko rigimmame? Sunanan dawowa jibi insha Allah"

"Dagaske? Kai Amma naji dadi dama nayi missing dinsu"

Tafada cikin murna

"Aikau sunkusa dawowa yazo ya Dora Daga inda ya tsaya"

"Kai mamy Abdul fa Beda rigima"

"Ke daice bemawa"

"Hhhh atoh Yamayi din in mashi Rowa"

Dariya mamy itama tayi sannan tace

"Daughter Wai dagaske ne abubuwan danake ji?"

Gaban Saudart ne yafadi

"M..me kenan?"

"Wai anganki tareda A.A Wai ke budurwarshi ce"

Kunya ce tadan kama Saudart sai tayi shiru

"Kinyi shiru?"

"Mamy.."

Saikuma tayi shiru don batasan abinda zatace ba

"Ba damuwa, gobe ki biyo tanan zamuyi magana"

"Ok mamy" tafada a kasalance.

"Saida safe to"

"To mamy Allah yabamu alhairi"

Kitt suka katse wayar tare.

Kasa cigaba da karatun tayi takoma ta kwanta tana kallon ceiling zuciyarta fall da saqe saqe...✍

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ya yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

022

Washegari kamar yadda mamynta ta buqata, biyawa tayi gidanta.

Kamar ranan bata iske kowaba sai mamy kadai, yaran basu dawoba shikuma mijinta yana banki (dayake bank manager ne).

Hira suka dan ta6a kafin mamyn ta dauko maganar jiya.

"Angel, jiya munfara magana bamu idaba"

"Eh mamy" Saudart tafada tana sinne kai.

"Tell me Angel, dama A.A saurayinkine? Wace cinema naji yace kun hadu? Dama kina zuwa cinema ne? Me kuma yakaiki binshi wannan taron?"

Shiru Saudart tayi don tama rasa da wacce tambaya zata fara, gashi bawani karya ta iya shiryawaba.

"Saudart kinyi shiru, kinkau san waye A.A? Kinsan matsayinshi kuwa? How come kika fara soyayya da wanda ni dake Munsan kwata kwata baya cikin tsarin mazajen dakike so, Saudart are you hiding something from me?"

Qaqaro murmushi tayi tana cewa
"N..no mamy, Allah babu abunda nake boye miki, kawai hadi ne na Allah"

"Naji, me yakaiki cinema at first place har kuka hadu?"

'Woo yau na banu' inji Saudart cikin zuciya.

"M..mamy tareda daddy fa mukaje, w..wani film ake haskawa shine mukaje kallo"
Tafada sai raba idanu take alamun rashin gaskiya.

"Saudart, karya kikemin?"

"A'a mamy, mezaisa inmiki qarya? I swear kallo mukaje da daddy muka hade"

Ajiyar zuciya mamy tasauke dukda haryanzu bata ida yarda daitaba.

"To meyasa kika bishi taron?"

'Ohh mamy pleease' tafada a zuciyarta

"Ina jinki" inji mamy data tsareta da idanu.

"Mamy cewa yayi nabishi"

"Kuma sai kika bishi?!" Inji mamy ahasale

"Mamy am sor..."

"Dalla rufemin baki! Har namiji yazo yace kibishi kema kibishin? Ina tarbiyyarda nabaki? Kuma shi baban naki da saninshi yabarki kikaje? Ina hankalinki yatafi? Ehh?"

"Am sorry mamy, bazan sake ba"

"Kima sake din sakaran banza, yaje yawani nunaki wa mutane, idan be aureki bafa? Wannan ai sakarcine..."

Nan taita fada ta inda take shiga batanan take fitaba, itadai Saudart haquri kawai take bata, nan Daga baya fadan yakoma nasiha, nasiha mai ratsa jiki tayi mata har saida zuciyar Saudart ta karye tafara hawaye.

Sai wajajen 12:pm ta var gidan Tawuce bakery.

A bakery ma ranan ranta a dagule yake, anya tayima kanta adalci data yarda da wannan auren, ga kuma sa6ama ubangijinta datayi.

Haka tawuni ranan zuciya a cunkushe sai istigfari take akan Allah ya yafemata da ita da daddynta.

Suna zaune falo suna kallo sukaji sukaji qarar doorbell.

Ganin baby batada niyyar motsawa yasa Ummy cewa
"Bakiji ana danna bell ne?"

"Wayyo Ummy dan Allah kiyi hqr idan natashi wuceni za'ayi kuma ba damar tariyowa, please kiyi hqr"

"Zaki tashi ne ko saina sa6amiki"

Baki a cinne ta tashi tanufi kofar tanayi tana waigen tvn

Qara danna doorbell da'akayi yasa ta qarasa wajen kofar a afusace tana cewa
"Ana zuwa, haan?"

Tana budewa sukayi four eyes da Ashraf sai Sadeeq bayanshi.

Saurin ja dabaya tadan yi tana yaqe

"Laa! Ashe kune? S..sannunku Ku shigo"

Wata uwar Harara ya gallamata sannan yashigo zaiwuce tayi saurin ra6ewa ya wuce, Sadeeq na shima yashigo yana dariya ganin yadda baby ta bude azafafe tana ganin Ashraf Duk ta daburce.

Harara ya wanka mashi.

"Meye abin dariyar?"

Sake dariyar yayi cikin tsokana yafara waqa

"Taji tsoro abata ruwan mad'aci ta kuskure..."

Kwa6e fuska tayi cikin shagwa6a tareda juyawa zata tafi tana cewa

"Wlh yaya Sadeeq mun 6ata kuma baxamu shiryaba nan kusa"

Wari idanu yayi ya biyota ganin tasa gudu.

"Haba autas, tsaya mana"

Amma harta haye.

Dariya yayi sannan yajuyo suka hada ido da Ashraf daketa yimashi antayen Harara tundazu.

Shima antayamashi nashi yayi sannan ya qaraso falon a kunyace ya zauna gefen Ashraf.

Zamowa yayi Daga kujera ya tsugunna yana gaida Ummy.

Amsawa tayi cikin fara'a tana tambayar Yasu mamanshi.

Komawa yayi kan kujerar yana amsamata suna lfy.

Nan fira ta 6arke don dama Sadeeq dan gidan Ummy ne, kusan Duk weekend dama yana zuwa gidan ya yini kamar yadda shima Ashraf ke zuwa gidansu, idan suka yini gidansu Ashraf ranar Saturday to gidansu Sadeeq zasu yini ran Sunday, idan kuma ran Saturday sun yini gidansu Sadeeq to ran Sunday gidansu Ashraf zasu yini.

Wannan abota nasu na burge mutane musanmman su Ummy, don da wuya kaji Kansu, idanma sun 6ata saikiga babu mai sukuni acikinsu har saisun shirya.

Hira suketayi gwanin sha'awa dama Sadeeq qaqa lafiyar giwa? Ashraf kau takaici ya rufeshi sai zungurin Sadeeq yake kan yafadi abinda yakawosu Amma yayi banza dashi kamar bejin zungurin, dariya fall ranshi.

Dadai Ashraf yaga abin nashi rainin hankali ne saiyayi Fushi ya tashi yana cewa Ummy zai shigo, a fito lafiya tayimashi sannan yayi gaba kamar zai tashi sama.

Dariya Sadeeq yayi yana girgiza kai saida ya sake 6ata kusan mintuna talatin sannan yacema Ummy bari shima ya haura.

Izuwa yanzu saura kadan Ashraf yayi bindiga.

Da sallama Sadeeq yashiga yana qumshe dariya.

Ashraf dake rigingine kan gado kafaffunshi zube qasa yayi saurin tashi kamar Wanda aka tsikara,

"Get out dan ubanka!"

Waro idanu Sadeeq yayi sannan ya dan dafe kai

"Ohni wannan uban nawa na shan zafi wajenka"

"Nace out!"

"Sai kazo ka fiddani din, ba'a fita yafada yana riqe qugu yana girgiza kamar dan daudu.

Tasowa Ashraf yayi yana nad'e hannun Riga yana cewa

" wlh koka fita ko in fiddaka"

Cikin girgiza Sadeeq yace

"Fiddani din"

Nan suka hau kokowa, sai Ashraf takaishi bakin kofa dakyar sai yakuma zille yadawo ciki dagudu, shikuma bazai haqura ba, yana nishi yana komai zai sake maidoshi bakin kofa saikuma yasake zillewa yadawo yana kyakyatamashi dariya.

Babu abinda ke tashi dakin sai nishi da dariyar Sadeeq.

Ganin babu sarki sai Allah yasa Ashraf haqura yawani laftashi kan kujera yamike yana haqi

"Shege.. Rusheshen banza"

Dariya Sadeeq keyi sosai

"Naji raggo ajeebo kawai, d'an ni dinne bazaka iya fiddawaba? Shame!!"

Tsaki yaja yawuce bedroom dinshi yana gunguni.

Shidai Sadeeq saida yagama dariyarshi sannan ya tashi ya shiga bedroom din yaga Ashe wanka yashiga.

"Woo yaji maza dole yaje ya watsa koko juye akeyi oho?"

Ashraf dake jinshi yaja tsaki kawai.

Sai Bayan kusan 20mins Ashraf yafito yana tsane jiki fuska a tamke.

Ganin Sadeeq na lasta mashi laptop yasa yaje ya kwace yana mashi mugun kallo

"Bi sannu kar towel din ya kunce inshiga uku, ca6! Dakau Saudart saita daure ni"

Tsaki yaja yana ajiye laptop din kan mirror.

"Get out zan shirya"

"Yo ai hikenan" inji Sadeeq shima yana Fadawa bandakin.

Koda yafito Ashraf harya bar bedroom din.

Bude closet din Ashraf yayi yaza6i wasu qananun kaya yasaka sannan yafito ya iske Ashraf falo yana kur6ar coffee.

Shima hada coffeen yayi yazo ya zauna kusadashi yana kur6a.

"Wai dude Duk hade haden rannan Duk na menene?"

Banza yayi dashi

"Kaji?"

"Please ka kyaleni Sadeeq, please"
Chapter 14 · 0% Book details