← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 111

Sashe 72

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ganin irin kallon dayake mata yasata sakin murmushi cikin basarwa tace
"Daddy na" tafada a shagwa6e tana matsowa kusadashi tayi pillor da kafadarshi

"Shalele ta" yafada yana dan rungumo kafadarta

Lumshe idanu tayi tana jin qaunar daddyn nata sosai acikin zuciyarta

"Shalele, meyasa kika yarda da abinda zuciyarki bataso? Meyasa kika za6i zama da abinda zuciyarki bata muradi? Hmm?" Ya tambaya softly.

Tasan 6ata lokaci ne kawai jayaya dashi akan ba haka bane don tasan idan tana iya yiwa kowa basaja to banda daddy don yasanta ciki da bai, kallo daya zaiyi mata yagano gaskiyarta ko akasin haka.

"Daddy ka tayani da addu'a kawai, Allah yakawomin komai da sauqi"

"Baki amsa tambaya ta ba"

"Daddy, na amsa tambayoyinka tun agaban su ummy, am giving him another chance don wancan lokacin komai yafarune abisa rashin sani, shiyasa nayi mashi uzuri kuma atunanina allah kadai yasan dalilin hadamu tun farko kuma bamuda wata qwaqwarar hujjar rabuwa"

Ajiyar zuciya daddy ya sauke sannan yace
"To shalele allah yasa hakan shiyafi alhairi, shalele am so happy today na hadu da wadanda na shafe shekaru aru aru ina nema dukda narasa wanda nafi muradin sanyawa a idanu shekara da shekaru" yafada in mixed feeling

"Allah ya jiqansa daddy yakuma yimashi rahma ka kuma yawaita sakashi a addu'a don yanxu babu abinda yafi buqata sama da ita, allah kuma ya dorar da zumuncinmu" inji saudart

"Amin amin shalele, Allah yayimiki albarka, yasa kigama da duniya lfy yabaki 'ya'ya masu biyyaya kamar yadda kikemana, Allah ya qara daukakaki ya tsareki daga sharrin masu sharri" inji daddy

Qara qanqameshi tayi tana murmushin jindadi don sosau taji dadin addu'o'in

"Amin sweet daddy na, i love you" tafada cikin murna

Dariya daddy yayi cikin farinciki shima yace
"Love you more my jewel"

"Daddy?" Takira sunanshi a shagwa6e

"Na'am shalelen daddy"

"Alfarma nakeson kamin daddy, please don't say no" taqarashe maganar kamar zatayi kuka tana qara lafewa a kafadarshi

Murmushi daddy yayi sannan yace
"I won't, ki fadamin"

"Daddy sonike nakoma gidan mamy for a while please" tafada ahankali

Shiru yadanyi sannan ya dago fuskarta cikin taffukan hannayenshi yana kallonta yace
"Why?"

"Hakanan, ba dadewaba zanyi sosai ba, just a week or two" tafada asanyaye

Shiru yayi yana kallonta bece komaiba.

"Pleeeeease" tafada kamar zatayi kuka.

"Ok, anything for you" yafada yana mata murmushi.

Qanqameshi tayi cikin jindadi

"Yeah! That's my sweet dad!" Tafada cikin murna

Shima dariyar farinciki yake, ganin shalelenshi cikin farinciki shima ba qaramin sashi cikin farinciki hakan yayi ba.

Haka sukaita fira cikin raha da jindadi wanda rabon da suyi irinshi har mantuwar ta mance, haka sukaita firarsu cikin tsananin so da shaquwa yayinda hakan ya gusarmata kaso 60 na 6acin rai da kuncin datake aciki.

Qarshe ma tare suka hau hada yan kayyayakinta dazata dasu gidan mamyn, daddy na mitar zata tafi ta barshi shi kadai, zaiyi missing dinta sosai. Itadai sai dariya take mashi tana fadin abinda duka yan kwansji zatayi tadawo kuma itama ai zatayi missing dinshi.

Haka dai suka qarashe yinin cikin farinciki da jindadi.

A bangaren ashraf kau tunda yashiga daki be saukoba sai wajajen magrub yafito suka hadu da kawu ibrahim da shima gobe insha allah zai koma suka wuce massalaci.

Koda aka gama sallar basu dawoba can suka xauna jiran isha'i inda a dan wannan lokacin kawu ibrahim yaita yimashi nasiha da shawarwaru masu amfani wanda sosai ashraf yaji dadinsu don sun taimaka mashi wajen dan ragemashi abinda yakeji a zuciya.

Saida suka gama isha'i sannan suka shigo gida inda direct dining suka nufa.

Saida yaci ya qoshi sannan ya miqe yaima kowa saida safe sannan yayi hayewarshi sama.

Koda yakoma dakinshi cigaba yayi da tunanin daya katse dazun yana nazarin shawarwarun da sadeeq da kawu ibrahim suka bashi ayau.

*Ashraf nasan saudart bawai ta yarda zata zauna dakai bane don son ranta, ta yarda ne don batada za6i, ashraf wannan damace allah ya aramaka don ba kowanne mutum allah ke sake bashi damaba, ashraf take your time, don't play with your opportunity, yanzu damarkace na koyawa saudart sonka, ta mato akanka, ka tsundumata tsundum acikin kogin sonka, don't play with your chance, opportunity come but once*

Maganar da sadeeq yafadamashi daxun kafin yatafi ya dawo mashi a qwanya.

*Babana Allah ya azurtaka da mace tagari mai tarbiyya, kayi kokarin riqeta dakyau, karka bari tasake kufcemaka a karo na biyu don ba lallai bane allah yabaka irin wannan damar ma, ita zuciya tana muradin mai kyautata mata ne, ka kasance mai kyautatawa iyalinka zakasha mammaki* maganar kawu ibrahim yadawomashi.

Ya dauki lokaci mai tsawo yana tunani wanda kuma ke qaramashi qarfin gwiwar samun saudart.

Tabbas dafarko yayi kuskure ya bari girman kanshi yakusan kaishi yabaro amma ayanzu ya shirya damarar yaqo zuciyar saudart, saiya koyamata sonshi yadda duk numfashinta saita shaqa da sonshi ne, zai ajiye komai ya gyara abinda ya 6ata da kanshi.

Fatanshi dai allah ya tallafamashi yakawomashi komai cikin sauqi.

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

Washegari wajajen 12:00pm saudart ta isa gidan mamy.

Saida ta tsaya suka gaisa da maigadi kamar yadda suka saba sannan ta shige ciki janye da dan qaramin trolley dinta.

Gidan shiru kuma tasan hakan be rasa nasaba da saboda yaran na makaranta ne, tasan mamy kadai ke gida, koyaya zata tarbeta? Tambayarda taiwa kanta kenan.

Danna doorbell tayi tana jinginar da trolley din gefenta.

Saida ta danna sau uku sannan taji muryar mamy na amsawa daga ciki sannan tajiyo takunta na nufo kofar wanda hakan yaqara mata fargaba.

Budewa akayi fuskar mamy ta bayyana.

Turus mamy tayi tana kallonta daita da trolley dinta da ayar tambaya a fuskarta.

"Mamy barka da rana" inji saudart tana dan murmushi

Kaucewa mamy tayi tana bata hanya don tashigo tana amsa gaisuwarta.

Kama trolley din tayi tashigo tana jaye dashi mamy tarufe kofar tabiyota tana kallonta still da ayar tambaya.

Zama saudart tayi kan daya daga cikin kujerun falon feeling uncomfortable da kallon da mamy ke binta dashi.

Itama mamy zama tayi dan nesa daita tana kallonta.

Zamowa tayi tashiga gaidata cikin girmamawa.

Amsawa mamy tayi babu yabo ba fallasa.

"Su abdul basu dawo makaranta ba?" Injita trying to sound free

"Eh basu dawoba" inji mamy a taqaice.

"Ayyah shiyasa gidan yai wani shiru" tafada tana murmushi.

Shiru yadan ratsa falon can sai mamy tace
"Ya naganki da trolley?"

Dan murmushi tayi shyly sannan tace
"Zan dan tayaku zamane mamy"

Dan ta6e baki mamy tayi tace "ok saiki kai kayan sama ki huta, bari nakoma kitchen" daga haka ta miqe tai wucewarta kitchen din.

Tashi tayi itama ta haura sama kamar yadda mamyn tace ta ajiye kayanta a dakin datake sauka anytime idan taxo kwana gidan sannan ta warware nadin gyalen jallabiyarta tabar hula kawai akanta ta sauko qasa ta wuce kitchen itama.

Sau daya mamy ta waigo ta kalleta takuma juya ta cigaba da abinda take.

Qarasowa saudart tayi ta amshi wuqar hannun mamyn, ba musu ta sakarmata ta koma wajen tukunyar dake saman gas cooker tana budewa itakuma saudart tacigaba da chopping din carbbage din a chopping board.

Haka dai sukai aikin kamar kurame babu mai magaba cikinsu gwara gwara saudart tana dan tambayar wani abin idan zatayi itakuma ta amsa a taqaice da alamu dai bata huce ba.

Cikin qanqanin lokaci suka gama saudart taita kawosu dining area itakuma mamy ta haye sama.

Saida saudart ta gyare kitchen din kamar ba'ayi girkiba ciki sannan itama ta haye sama don watsawa.

Wajajen biyu tana zaune kan sallaya bata dade da ida sallah ba taji hayaniyarsu abdul alamun sun dawo kenan.

Shafa addu'o'inta tayi sannan tamiqe ta linke sallayarta ta ajiye samsn bedside locker ta cire hijabinta ta adanata sannan tayi hanyar waje.

Su abdul nata gwadama mamy sums dinsu dasukayi a school sukaji tafiyarta.

Duk dagowa sukayi suna kaĺlonta a mammakince don basusan tana gidanba.

Dagudu sukayo wajenta har suna rige rige.

Fasa yar qara tayi tana dan qanqame jiki ganin yadda suka nufota don yadda suka taho dinnan tsab su zibe dukkansu.

Illai kuwa saigashi suna qanqameta suka tafi gabadaya suka zube.

Su aminullah da kamal me zasuyi banda dariya don kamal harda riqe ciki.

Mamy ma saida ta murmusa sannan ta dauke kai.

Tashi saudart tayi tana turo baki tana dungurinsu ganin sun kadata kuma suna mata dariya.

Haka suka taho suka w
qaraso falon suna ta dariyar.

Nan suka shiga gaidata tana amsawa tana tambayarsu ya school.

Tuni abdul yaje ya amshe littafinshi daga hannun mamy yakawoma saudart sai washe baki yake yau yace duka sums dinshi

Yabonshi saudart tashigayi tana fasa mashi kai shikau kan sai kumbura yake yana washe baki.

Ganin hakan yasa su kamal fara tsokanarshi saudart na kareshi.

Ganin abin nasu bana qarewa bane yasa mamy umartarsu suje su chanza su sauko suci abinci.

Babu musu duk suka haye sama harda saudart dake goye da jakkar abdul da habeeb.

Ita ta taimakawa qanannun suka chanza sannan suka sauko qasa suka wuce dining.

Saudart ce tayi serving dinsu suka zauna suka faraci silently bayan kowa yayi basmalah...✍

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

081

Da suka gama cin abincin duk sama suka haye don shirin islamiyya while saudart ta tsaya gyara inda suka 6ata ta tattara abinda suka 6ata tayi kitchen dasu don wankewa.

Tana gamawa itama tabisu saman don taimaka masu wajen shiryawa, anan ne suke tambayarta yaushe zata koma tace musu tananan sai tayimusu sattitika.

Zo kuga murna wajensu don sosai suke qaunar yar uwar tasu, haka dai suka kammala shirinsu suka fito gabadaya har wajen motarsu.

Shiga duk sukayi driver ma yashiga maxauninshi ya tada motar yaja su Abdul na dagama saudart hannu.

Saida suka fice sannan ta sauke ajiyar zuciya murmushi a fuskarta, dan lokacin nan datayi dasu ba qaramin tasiri yayi ba wajen gusar da damuwarta, sosai take jinta cikin nishadi.

Juyawa tayi takoma ciki, bata iske kowa falo ba hakan yasata hayewa sama don gabatarda sallar asr don wasu massalatan ma harsun gama.

Tana zaune kan sallayarta taji knocking din kofa, shafa addu'ar tayi sannan ta miqe ta dauke sallayar ta dora saman bedside locker sannan tanufi kofar.

Tana budewa taga mamy tsaye bakin kofar tana kallonta.

Murmushi tasaki sannan ta matsa don bata damar shigowa.

Shigowa mamy tayi dakin itakuma ta maida kofar tarufe sannan itama ta shigo.
Chapter 72 · 0% Book details