← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 111

Sashe 41

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Saurin Kamo hannunta Reyna tayi tana cewa
"Oh saudart! Ki shigo, am soo sorry, wlh tun washegari naso nazo amma tsoron shi nake, ina tsoron naje na taddashi ko ya taddani gidan, we're soo sorry!" Tafada tana jawota cikin dakin cikin kulawa.

"Mtcheew, wannan sorry din duk na menene to?" Inji saudart tana kwace hannunta ta nemi kujera ta zauna

Dawowa Reyna tayi kusada ita ta zauna tana cewa
"Wlh tun ranar muka shiga tashin hankali musanmman Amir, gani muke dukanki zaiyi, babu yadda beyi daniba nazo gidanku kona gayamashi block dinku amma tsoro ya hanani don gani nake a yanayinshi dinnan yana iya hadawa damu ya make, am so sorry, hope beyimiki komai ba?" Tafada tana dafa kafadarta.

Tsaki tasake ja tace "ni babu abinda yayimin dalla, ni Abu daban yakawoni kinzo kin isheni da surutu" inji saudart don kwata kwata batason ayi maganar

"Ayyah ai dole na damu ai, haryanzu amir bebar damuna ba, wai inbaki hqr besan ke Matar aure bace"

Dagowa tayi da sauri ta kalleta
"Waya fada miki ni Matar aurece?" Ta tambaya a mammakince

"Amir mana, sun hade da mijin naki yana bashi hqr anan ya fadamashi, ai wlh yanada gaskiya dole ne yayi kishi, imagine wata tazo tace maki tana sonshi kuma the next minute ki gansu tare dole kiji haushi" inji Reyna

Banza saudart tayi ta kyaleta don ita har mancewa take dawani aure dake kanta, jinta take soo free kamar ba Matar aureba.

Ganin zata sake magana tayi saurin katse ta da

"Look Reyna komai yawuce, ninan Abu daban yakawoni, idan kuma bazaki saurareni ba fine"

Saurin riqo hannunta Reyna tayi ganin zata tashi tana cewa
"Ok ok ina jinki, am sorry"

Saida ta murguda mata baki cikin wasa sannan tace
"Gobe zamu koma Nigeria"

Dafe qirji Reyna tayi da sauri kamar Wanda akayima mugun Abu.

"What? Please wasa kike? Nasan wasa kike ko?" Inji Reyna unbelieving

"Hmm wlh dagaske nake, meye abun wasa aciki?"

"Oh My good Lord saudart, akan wannan Abun zaku tafi? Please karku tafi zan kira amir yazo har gida yabaku hqr"

Tsaki saudart taja cikin takaici
"Look nifa nagayamiki nama manta da wannan babin, dama Abu yakawomu kuma mungama shiyasa zamu tafi" tafada tana kallon yadda duk Reyna tabi ta susuce

"No, nasan duk saboda abinda yafaru ne, please don't leave, wlh besan ke Matar aure bace" tafada cikin marairaicewa.

Tsaki saudart taja ta miqe tana cewa
"Bari kiga intafi tunda bakida ganewa"

Saurin shan gabanta Reyna tayi tana cewa
"Ok ki rantse please, ki rantse ba saboda hakan zaku bar nan ba"

Tsaki saudart taja tace
"Wai nata6a yimiki qarya ne?"

"Nidai please ki rantse"

"To na rantse, mungama abinda yakawomu shiyasa zamu tafi, ke ke tunawa da abinda yafaru ni harna manta, yanzu haka zuwa nayi naji babu inda zaki anjima Ku rakani shopping ke da Loveth?"

Sai a sannan hankalin Reyna ya kwanta har wani sauke ajiyar zuciya tayi

"Better, nazaci sbd haka zaku tafi and maganar shopping? It's capital YES! ko da inda zani bazan bari wannan damar kasancewa dake na qarshe ta su6ucemin ba, waya sani ko bazamu sake ganin junaba?" Tafada tana langwa6a kai gefe

"Insha Allah zamu sake hadewa ok? Koba yanzu ba" tafada itama tana langa6e kai

"I'll miss you" tafada tana rungumeta

"I'll miss you much" inji saudart tana murmushi

Ganin batada niyyar sakinta yasata yimata chakulkuli Wanda hakan yasata saurin sakinta suna dariya tare

"Ok now tafiyar nanan? Loveth zata samu zuwa?"

"Yes, yaushe zamu?"

"4:00pm dot zanzo nan, idan Baku shiryaba zan tafiya ta" tafada cikin kashedi

"Yes ma'am" inji Reyna tana sarawa sukayi dariya gabadaya sannan suka fito tare tayi mata rakiya harta kusan kaiwa gida sannan ta koma

*****************************************

*4:33pm*

"Mtcheew zanyi tafiya ta fa!" Inji saudart dake kofar gidansu Loveth fuskarnan a hade.

Reyna dake gefenta sanye da wando da shirt sai purple jacket ita gwiwa akai gashinta awaje ta kama hannun saudart tana cewa

"Kinga zomu tafi, she's not serious"

Saudart sanye take cikin lace jaa Riga da zani ta yafa gyale baqi stylishly, kallo daya zakamata kasan cikkakiyar bahausa ce.

"Mtcheew mutafi" inji saudart din tana bin Reyna.

Dagudu Loveth tafito daga cikin gidan takalmi a hannu tana cewa

"Kujirani please!"

Saida ta iso motar sannan ta ajiye takalmin tasaka tana numfarfashi wai don tayi Gudu.

Sanye take cikin baqar English gown mai tsaga a baya kanta kuma daukeda hula fara sai qatuwar handbag hannunta.

Haka suka shiga motar Reyna din sunama juna tsiya.

Reyna ce ta zauna mazaunin driver sai saudart gefenta sai Loveth abaya, haka suka tada motar suka bar wajen suka kama hanyar fita daga estate din.

Babu laifi sunyi spending din good time at are, shopping sukayi kamar babu gobe, duk abinda tagani ya burgeta saita dauka.

Haka suka jero suna shopping suna fira da dariya gwanin sha'awa, saida suka gama kaff sannan fa aka bude babin selfie, wai hotunan tarihi.

Sunyi hotuna harna hauka, daga qarshe rasa style din dazasuyi sukayi sai sukaita style din hauka suna dariya, it's a happy moment for them don jisuke kamar karsu dawo gida.

Ataqaice dai sai gab magrib suka baro supermarket din.

Nan suka sako duk kayan dasuka siya a mota suka shiga.

Wannan karon saudart ce ta tuqosu, suna tafe suna tsokanar juna suna dariya.

Koda suka iso gida har angama sallar magrib.

Kofar gidansu saudart suka yada zango don duk tafisu kaya, saida tagama sauke kayanta kaff sannan sukayi sallama akan saisun zo bankwana gobe idan ransu yakai.

Haka ta cicci6i kayan Niki Niki tashiga gidan.

A falo ta ganshi zaune yana danne danne a laptop, kallo daya tamashi ta kauda Kai tawuce shi kayan na rinjayarta.

Binta da kallo yayi harta kai bakin kofarta ta ajiyesu ta bude kofar sannan ta kuma kwasa tayi ciki tarufo kofar.

Ajiyar zuciya ya sauke yana shafa kanshi ahankali sannan ya cigaba da abinda yake.

*********************************

Washegari tunda ta tashi da asuba takasa komawa, dama jiya ba wani barcin kirki tayiba, jitake kamar tajawo lokacin don lokacin be wani yimata Gudu.

Flight din 10:00am garesu amma tun 7:00am take falo zauna sai gyara zama take agogo kau ta dubashi yafi a qilga.

9:00am sai jitayi ana knocking a kofar falon.

Saurin tashi tayi taje ta bude, ihu tasaki ganin Loveth da Reyna ta qanqame su cikin murna

"Hmm muda ba'a ganmu ba saimu juya" inji wata dake baya.

Sai a sannan saudart ta ankare dasu taga sunada yawa ma harda Dr zahra.

Saurin sakinsu tayi tana yi musu iso ciki fuska washe.

Nan suka shigo suka zauna taje ta kawo musu ruwan sha sai washe baki take.

"Hmm sai murna ake za'a gida kamar irin can yafi nan dinnan" inji wata cikinsu

Kamar jira ake nan falo ya kaure da cafta kowa na fadin albarkacin bakinshi itakau Dr sai dariya take musu.

Jin hayaniya a falo yasashi cikin mammaki sosai, to gidan dai babu kayan kallo bare yace kallo aka kunna kuma ma wannan beyi kamada kallo ba yafi jin hayaniyar a zahiri.

Saurin kammala shirin yayi yana duba agogonshi don har Tara da Rabi.

Turus yayi daya fito yaga gugun mutane zaune a falo saudart tsakiyar su suna dariya.

Ganinshi yasasu natsuwa suna gaidashi.

Qarasowa yayi yana amsawa yana kuma gaida Dr.

"Sai Nigeria ko?" Inji Dr zahra cikin tsokana.

Dariya kawai yayi yana shafa kanshi

"To Allah ya tsare, wish you safe journey, Ku gaishe da mutanen Nigeria, insha Allah zanzo watarana har gidanku, tunda duk munyi exchanging din number" tafada cikin fara'a

"To Allah yasa" inji Ashraf yana satar kallon saudart daketa murmushi.

Farincikin datake aciki afili yake baya 6oyuwa.
At last zasu koma qasarsu.

Fitowa sukayi tareda gungun mutanen sai tsokanarta suke tana biyemasu, har mota suka rakata harda budemata kofa tashiga.

Sai kuma a sannan suka fara marairaicewa wai zasuyi missing juna.

Haka dai suka rabu zuciya babu dadi sai dagawa juna hannu suke har suka bar hangen juna.

Komawa tayi ta jingina da kujerar tana sauke ajiyar zuciya tana murmushi.

Shima dayake satar kallonta tundazu murmushin yasaki ya kauda Kai yana mammakin saurin sabo irin nata, ji yadda mutane sukazo rakiyarsu kamar sunyi shekaru a qasar.

Haka motar tayi tsit har suka qarasa airport din.

Suna fitowa daga motar tafara bin airport din da kallo, kamar jiya ne suka shigo airport dinnan da niyyar shigowa qasar amma wai yau sune aciki da niyyar barin qasar zuwa qasarsu.

"Can't wait" tafada cikin zuciyarta tana murmushi

Saida aka gama komai sannan suka shiga jirgin.

Kamar wancan karon kusada juna suka zauna.

10:00am dot aka fara sannarwa na kowa ya daura belt dinshi.

Wannan karon ba'ayi qauyanci ba nan da nan ta daura.

Jin ana sanarwa na jirgi zai tashi yasa ta koma ta lafe a kujera murmushi a fuskarta.

Jin yafara tafiya yasa bugun zuciyarta qaruwa, jin ya daga yasata Sakin nannauyan ajiyar zuciya

"Bye Madrid, bye Spain" tafada ahankali tana bude idanu tana yiwa qasar kallon qarshe...✍

Kuyi hqr babu yawa, haihuwa akamana ban samun zama, wannan ma dasafe nake samu nadanyi kafin infita, da babu kwata kwata Gwara kadan, bear with me har komai ya warware🙏

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

052

Tafiyar awa biyar ne babu yan mintuna, kamar wancan tafiyar, barci ne yayi awon gaba daita ba ita ta farkaba sai gab da zasu sauka.

Jin suna landing a airport yasata jin wani shauqi na dibanta.

"Home, sweet home" tafada cikin zuciyarta tana murmushi.

Jitake kamar tayi tsuntsuwa taganta gida.

Saukowa aka farayi amma sai gani tayi Ashraf beda niyyar tashi don latse latsenshi kawai yake hankali kwance gashi dole saiya tashi itama zata samu damar fita sbd ita ke daga ciki shike waje.

Shiru tayi itama taqi tankamashi amma deep down she's burning.

Saida ya mula yasha iska sannan ya tashi ya kara wayar a kunne sannan yanufi hanyar fita cikin takunshi na qasaita.

Binshi tayi da kallon takaici sannan taja tsaki ta miqe itama tafito.

Kamar wancan karon drivern dazai kaisu gida haryazo.

Shiga sukayi dukansu gidan baya sannan drivern yajasu suka fice daga airport din.
Chapter 41 · 0% Book details