← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 94 OF 111

Sashe 94

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kai tayi tana mammakin irin wannan barcin nata, wannan tasan har asace bazata saniba

Cire zumbuleliyar hijab dinta tayi ta ninke ta maida wardrobe sannan ta zagaya dayan gefen ta haye gadon tajawo bargon dakyar ta lullu6e kasamcewar duk baby ta kanannade ciki sannan ta lumshe idanu

Ga mammakin ta jitayi barcin yaqi zuwa, saima abubbuwan sasuka faru dazun keta dawomata a kwanya

Tunawa tayi da yadda yasa yatsa baki dazun yana kallon sama alamun tunani saikace wani yaro da yadda yawani yamutse fiska yana ta6ula baki

Girgiza kai tayi, tun ba yau ba tasan shi da wannan sakatar amma tana mammakin yadda shagwa6a kemishi kyau bayan shi namijine.

Wait... Kyau? Yaushe ma tafara tantance kyaunshi? Tambayar datayi ma kanta kenan

No, su6utar tunani ne, bazai ta6a yimata kyau a idanu ba bare harya burgeta, taqarasa zancen zucin tana murguda baki ita kadai

*remember promise bashi ne and I don't forgive debt*

Maganarshi ta dazun ta dawomata

Murmushi tadan saki na gefen tana dan daga gira tace
"Then I'll break your record"

Ta jima ahaka tanata tunane tunane wanda duk na abubbuwan dasuka faru yaune kafin barci ya sadado ya figeta batareda ta saniba

Can cikin barci taji kamar ana tashinta, yamutse fuska tayi tana qara damkar bargon jin kamar za'a janye

"Wohoho aunty wai wannan wane irin barci ne haka?" Inji baby tana qara janye bargon

Dakyar saudart ta bude idanunta dasukayi mata nauyi ta kalleta

"Haba aunty wannan barci kamar na mutuwa? Lallai yaya zaisha fama, kinsan ko tun yaushe nake tadaki?"

Harara saudart ta gallamata tana miqewa zaune, wai nacikin Masai ne zai cewa na waje ka taka kashi.

Miqa tayi tanajin kamar tasake komawa ta kwanta don kwata kwata barcin be isheta ba jitake kamar yanzu ta kwanta aka sake tadata

Saukowa tayi daga kan gadon tanufi toilet jin wasu wuraren har an fara assalatu.

Alwalla ta dauro sannan tadawo dakin ta saka hijab tazo ta tsaya kusada baby data fara sallarta itama ta kabbarta nata tashiga yi.

Yau bata tsaya azkar din safe data saba ba tana gamawa tayi yan addu'o'i ta shafa ta miqe ta cire hijab dinta ta koma kan gado

Girgiza kai baby dake zaune kan sallaya tana azkar tayi tana mammakin irin wannan barcin nata

Ba ita ta sake farkawa ba sai wajajen 10 na safe

Tashi tayi zaune tana karanto addu'ar tashi tana miqa at the same time.

Kallon gefe tayi taga baby ce kwance itama tana shar6ar barcinta.

Komawa tayi ta jingina da jikin gado tana mammakin mafarkin datayi yanzu.

Wai ashraf ne ke nemanta akan tazo ta kawomashi coffee dinshi as promised shine ta shigo daki aguje ta boye gefen gado tsakanin bedside locker da gadon tareda rufe bakinta da hannu bibbiyu donma kartayi kwakwarrar motsi

Batafi seconds biyu ba da buya sai gashi shima ya shigo dakin yana waige waigen nemanta

Qara lafewa tayi tareda qara toshe bakinta ganin yadda yakebin lungu da saqo yana nemanta.

Saida yagama hange hangenshi be gantaba ya haqura yanufi kofa

Ganin haka yasata sauke Ajiyar zuciya 6oyyaya cikin jindadin rashin ganinta

Saida Yakama handle din kofar zai bude kamar ance ya waigo sai suka hada ido da ita a inda take

Hakan yasata saurin miqewa tsaye tana sakin qara wanda yayi daidai da farkawarta.

Ajiyar zuciya ta sauke bayan tagama tuno mafarkin tana mammakin yadda abinda yafadi jiya ya tsaya mata arai har tayi mafarkinshi don dama ita idan Abu ya tsayamata arai sosai saitayi mafarkinshi

Tashi tayi ta sauko daga gadon tanufi toilet don tayi freshen up

***

Ringing din wayarshi ya sashi dakatawa daga tsane jikinshi dayake da qaramin towel din hannunshi

Nufar mirror yayi yajawo wayar yaduba, ta6e baki yayi ganin mai kiran

Saida takusan katsewa sannan ya daga ya kara a kunne yace
"Uhum?"

"Ango! Ango!! Ango!!! Ango kasha qamshin ne koko dasaura?" Inji sadeeq cikin shaqiyanci

Tsaki ashraf yaja yace
"Fadi abinda zaka fadi am busy right now"

"Inyee? Ka fadi hakan Ai amma wajen neman taimako ka iya marairaicewa kana qanqan da kai kamar dan maula"

"Mtcheew, kamar yadda nafada maka dazu am busy so idan bakada abin fada kindly hang the call"

"You're busy doing what?" Sadeeq ya tambaya in a naughty way

"Bansàniba"

"Kar Allah yasa kasani, dullie kawai wanda besan arziqiba" inji sadeeq cikin son qular dashi

"Naji nagode, Ai kai kasan shi ko? Hakan Ai ya wadatar" ya amsa in an i-dont-care mannar

"Mtcheew ba laifinka bane, laifinane Dana kiraka"

"Gwara daka gane hakan, gwauro kawai"

"Gwauraye dai"

"Kana hauka, waye gauron, kai bakama ji kunyar fadin haka ba"

"Kunyar me? Ba gaskiya bane?"

"Oho dai, idan zaka ajiye shiririta kayi aure ka aje kayi don na kusan Barin mu'amala da gwauro" yafada yana taje kanshi

"Hmm wai kura zatacema kare maye, kai har kanada bakin yima wani gori? Aikin banza kawai bansan abinda yasama na kirakaba at the first place, mtcheew mood spoiler kawai" yana kaiwa nan ya katse wayar

Dariya ashraf yayi yana ajiye wayar kan mirrorn yanufi closet dinshi

Agurguje ya shirya cikin wasu qanannun kaya wando da T-shirt baqaqqe tareda feshe jikinshi da turarenshi mai dadin qamshi ya dauki wayoyinshi ya fice daga dakin...✍️

Manage pls👏

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖

097

Dole ta tashi tabar falon jin ana kiraye kirayen sallar magrib

Alwala ta dauro tazo ta gabatar da sallar magrib ta zauna bayan ta ida ta zabga uban tagumi

Tunani kala kala na kai kawo a kwakwalwarta

"To ko fushi yayi? Amma Ai ita yayima laifi meyasa shi ke fushin kuma?" Tambayar datake tayi ma kanta kenan

Tarasa dalilin dayasa rashin kulawarshi agareta na yini daya yayi affecting dinta sosai har haka

Gashi ego dinta ya hana ta lalubeshi ta waya koda ta text dinne, gani take hakan zubda mutunci ne agareta.

Tana nan zaune tana karatun jaki har aka fara kiraye kirayen isha'i, saida ta chanzo alwallarta sannan tazo ta gabatar da ita itama

Zaune suke a dining sunayin dinner

Ummy tun dazu take nazartar saudart ganin yadda take tsakurar abincin kamar bataso dama tana lura da ita duk yau kamar bata cikin walwalarta don takoma wata sukuku daita

"Daughter?"

Dagowa saudart tayi ahankali ta kalleta

"Meke damunki ne? Is anything bothering you?" Ta tambaya cikin kulawa

Itama baby tsayar da cin abincinta tayi tana kallonta don itama tun dasafe ta lura yau Auntyn tata bata cikin walwala don ko magana bata cika son yiba

Murmushin yaqe saudart tayi tace
"Am fine ummy, kawai am not feeling well ne"

"Me yasameki to, is it fever?" Tafada tana ta6a wuyanta donjin temperature dinta

"No ummy kawai slight headache ne kuma banida appetite" ta amsa asanyaye

Cikin jimami ummy tace
"Eyyah, now ki daure kiqara cin abincin ko yayane saina baki medicine, ok?"

Gyada mata Kai tayi ta dauki spoon dinta

"Sorry aunty" inji baby

Itama kadamata Kai tayi tashiga cigaba da tura abincin badon dadi ba

She's just missing him so very much

Ayyanawa take aranta da yananan da yanzu yananan ya takurata da wannan mayen kallonshi, da yanzu duk hada idon dazasuyi sauya kashe mata ido, da yanzu yakusan cika mata waya da texts

Haka dai tasamu tadan qaracin abincin, ummy ta rakata sama ta 6allamata maggunguna tasha ta kwanta bisa umarnin ummy

Tana cikin bargo taji ummy na waya da ashraf

Shiru tayi cikin bargon tana sauraronta harsukayi bankwana

Dago wayar dake hannunta tayi tacikin bargon tana kunnata tana kallonta

Gani take kamar daya gama wayar da ummy zai kirata or yaturo text amma har aka kusa shafe awa ba kodaya daga ciki dayayi

*why are you angry?* ta tambayi kanta still tana kallon wayar

*Are you fed up with me already?*

*am I too harsh?* duk wadannan zantukan acikin zuciya takeyinsu

Lumshe idanu tayi tanajin zuciyarta na daci sosai

*am missing you.... So much* tafada under her breath tana dora wayarta akan qirjinta tareda rungumeta

Ahakan barci ya dauketa batareda ta saniba

A bangaren A.A kau dama tun jiya sukayi arranging meeting da wani company mai muhinmmanci

Koda saudart taqi kulashi kyaleta yayi ya kwanta saidai Sam barcin yaqi zuwa hakan yasashi tashi yajawo laptop yadan rage ayyuka wanda hakan yasashi raba dare sai can wajajen uku yasamu ya kwanta

Da asuba bayan yagama sallah kawai yahau shirin office dukda zuciyarshi na azalzalarshi akan yakira saudart ko yamata text yadda yasaba saikuma ya fasa acewar gwara yabata space tahuce ganin yadda tahau sosai jiya inda shi harga Allah besan hakan zai 6atamata rai ba

Koda yafito don gaida ummy sai yaci karo daita a kitchen hakan yasa besamu Damar haurawa sama ba

Dayake sauri yake ko break be tsaya yayi ba yawuce zuciyarshi cikeda son ganinta

A office kau tunda yaje yashiga busy don aiki ne sosai a desk dinshi kasancewar yayi sati rabonshi da office din kuma be samun damar ragewa a gida sanaddiyar shiriricewa dayake da saudart ta waya

Ga kuma meeting din dazasuyi wannan yasa be dawo gidaba sai wajajen 10 don sosai aikin ya riqesu gashi ba secretary bare adan samu saukin aikin

Koda yadawo a matuqar gajiye yake hakan yasa yanufi part dinshi kai tsaye yayi wanka yayi shirin barci don dama yayi dinner awaje, hakan yasashi kiran ummy yayimata saida safe don a yadda yake agajiyen nan be iya sake fitowa

Koda suka gama waya saida yashiga contact dinta yanaji kamar ya kirata sai kuma wata zuciya tace mashi ya kyaleta kawai yadan bata space yadda zata huce sosai hakan yasashi ajiye wayar ya shige cikin duvet nan da nan barcin gajiya yayi awon gaba dashi

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

Washegari ma tun bayan sallar asuba yayi shirin office don yau dinma sunada aiyuka da meeting masu muhinmmanci dazasuyi.

Wajajen 7:30am yafito daga part dinshi yashigo cikin gida saida suka gaisa da maid dinsu dake falo tana mopping sannan ya haura sama dakin ummy

Saida ya kwankwasa sau biyu sannan ummy tabashi izinin shigowa

Da sallamarshi yashiga yaci adonshi cikin blue suit da farar inner yayi kyau sosai sai baza qamshi yake

Amsawa ummy dake zaune akan sallaya hannunta riqe da hisnul Muslim tayi tana dagowa daga littafin

Zaunawa yayi shima qasa kusada ita yana satar kallon saudart dake qudundune a bargo da alamu ma barci take
Chapter 94 · 0% Book details