← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 111

Sashe 15

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba aminin, kayi hqr ka gayamin, please"

Harara ya antayamashi.

"Dan ubanka ya mukayi dakai?"
"Name fa?"

"Bansaniba"

"Wohoho, please ka gayamin mana, idan Nasani zan nuna ban sani bane"

"Na nawa kuma? D'an rainin sense kawai"

"Naji, yi hqr ka gayamin"

"Mtcheew, batun damn contract marriage din mana, ya mukayi dakai, ba cewa nayi ka gayama Ummy ba?"

"Sannu😒 niga rasa kunya kazar birni ko?"

"Au bazaka fada mataba?"

"Ni zan aureta? Kaji qarfin hali"

"Ok, sai kaje kacema wannan tsohon banzan ya dawomin da kudina nafasa"

"Wannan kuma ake kira impossible tense, ka lashe"

Shaqoshi yayi

"Dan ubanka ina wasa dakai?"

"A'a..A'a, yi hqr, bari mufita zan gayamata, Shikenan?"

Sakinshi yayi yana Harara

"Idiot"

Shima harararshi yayi.

"Expired element".

*****************************************

" Ina jinka Sadeeq"

Sosa qeya yasakeyi sannan yace
"Ehmm dama..dama.."

Takaici kamar Ashraf yayi me? Jibeshi kamar wani na Allah.

"Sadeeq Wai ya haka? Menene Wai?"

"Ummy dama Ashraf ne... Ehm...yakeson..ehm.. Atura...ehm atura gidansu Saudart"

Ya qarasa zancen yana susar qeya.

Sunkuyar dakai Ashraf yayi cikin kunya da takaicin Sadeeq, kai Sadeeq mumu ne, haka ake magana? Aikau zaici ubanshi.

Murmushi Ummy tasaki cikin jindadi

"A'a Masha Allah, shine kuke wani sinne sinne Tun dazun? Kai alhamdulilah, aikau zan aika Ayi magana da kawunanka insha Allah, Allah yayi muku albarka"

Sadeeq cikin qara sinne kai da sigar Neman magana yace

"Amin Ummy, Wai kuma yace kar asa da nisa. In so samune..."

Wani dundu Ashraf yakai mashi abaya Wanda ya hanashi qarasawa.

Tashi Sadeeq yayi cikin dariya yagudu sama ganin Ashraf na niyyar kaimashi wani dukan.

Shima Ashraf maramashi baya yayi sukayi sama.

Dariya sosai Ummy keyimusu, abotarsu na burgeta sosai.

Tashi tayi don ta dauko wayarta takira kawunnanshi don sanar dasu wannan abun farincikin...✍

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

023

Kan kace me? Har maganar Neman auran A.A ya zagaye family, Masu murna nayi, yan baqin ciki nayi, Masu Kishi nayi.

Nan da nan kawunnan sukayi bincike akan Saudart kuma suka sami gamshashen sakamako.

Cikin dan qanqanin lokaci aka fidda ranar da zasuje Neman auran Saudart.

Alhaji shamsu baki har kunne dayaji wannan daddadan labarin.

Shirye shiryen tarbar manyan baqi yake kamar zai tarbi sarakuna.

Sai rawar kafa yake, burinshi ya burge ahalin A.A

Alhaji shamsu har office yaje ya tadda mijin mamy ya fadamashi abinda ake ciki don yanaso ya kasance harda dangin uwar Saudart wajen.

Sosai mijin mamy yaji dadi itama mamyn haka don haka itama ta sanarda danginta aka samu mutum daya sai Abba (wato mijin mamyn).

Saudart kwata kwata batasan wainar da'ake toyawaba, sai ranar Daren zuwansu wato asabar taja kamar daddy nacikin busy sosai.

Koda ta tambayeshi ce matayayi baqi zaiyi gobe. Bata kawo komai aranta ba tace Allah yakawosu lfy.

Ranar lahadi kamar yadda tasaba tana gama abinda take Tawuce gidan mamynta.

Nan suka hade da qannenta aka bude chafter fira, sunata bata labarin Maiduguri, dakuma tsarabar dasuka samo.

Itadai mamy sai binta take da kallo tanajin dadi at last Saudart zatayi aure, burin kowacce mahaifiya kenan idan diyarta takai minzalin aure to tayi.

Dukda Saudart ta lura da kallon datake mata saita share tacigaba da biyewa su Abdul.

A Bangaren su alhaji Shamsu kuwa, tarbar mutunci sukayima dangin A.A, sosai ahalin suka shiga ran dangin A.A saboda karamcinsu, Bayan anci ansha anyi wasa da dariya nan suka bada kudin mungani munaso, sosai adadin kudin yakusan rikitasu da farko sukaqi amsa saida aka Kai ruwa rana sannan suka amsa nan take aka tsaida ranar biki, nan da wata daya.

Taro ya watse lafiya, Alhaji shamsu sai godiya yakema su Abba da abokanshi daya gayyato nan suma suka Kama gabansu kowa zuciya fall da murna.

Zaune suke Saudart na karanta musu wani story book na yara. Duk sun zuba mata idanu kamar TV basusan ko motsawa tayi saboda yadda labarin ya dauko dadi, cikin nutsuwa take Masu karantun cikin lafiyayyen turancinta ga yadda take acting kamar itace don da anzo inda mayya ke magana saita qarama muryarta girma takoma naban tsoro, da anzo inda diyar sarki zatayi magana sai ta maqe murya, da anzo wajen kuka saita kwa6e fuska tana magana cikin muryar kuka.

Hakan yasa labarin kemusu dadi sosai kowa ya maida hankali yana sauraronta harda mamy dake zaune kan kujera tana saqar hannu.

Sallamar Abba ne ya katsesu, dukkansu dagowa sukayi suna amsa sallamar Saidai sa6anin da dasuke rugawa su rungumeshi yau kowa Daga inda yake zaune yake aikamashi sannu da zuwa don basusan abinda zai katse musu story din.

"To? Yau ba tarba? Wato antynku tazo anbar yayina ko?"

Dariya sukasa gabadaya harda Saudart.

"Abba sannu da dawowa" inji Saudart

"Yauwa daughter, ya weekend?"

"Alhamdulilah Abba"

"Oya kutashi mutafi sama, oya oya get up" tafada tana zungurin qeyarsu don suba su mamy waje.

"Saudart idan kin kaisu kidawo muyi magana"

Dukda gabanta yadan fadi saitayi murmushi tace "to Abba"

Sannan ta tisasu gaba suka haye sama.

Aminullah dake sama dama don acewarshi baya shiga cikin yara Wai karsu rainashi. Yana ganinsu yamiqe zaune yana hade rai.

"Anty lafiya naga kun dawo nan?"

Harara ta dalla mashi

"Lafiyar ce takawo hakan"

"Haba anty ni dan Allah Ku chanza room wadannan yaran damuna zasuyi da hayaniya" yafada yana gallama su Abdul Harara

"Sannu babba, wlh Saidai kai ka chanza room. Ace mutum kwata kwata beson qannenshi su ra6eshi? Kuma wlh karka saki ka ta6asu. Ka ta6asu nida Kaine" ta gallamashi Harara sannan tafice.

Afalo ta taddasu da alama suna cikin farinciki don fuskarsu Duk a washe suke.

Qarasowa tayi ta zauna qasa dan nesa dasu.

"Qaraso nan daughter"

A kunyace ta qaraso kusadashi tana sinne kai.

"Masha Allah, Alhamdulilah. Babu abinda zamuyi a wannan lokacin sai godewa Allah, dakuma fatan Allah ya sanya alhairi acikin lamarin.

Allah ya tabbatar da alhairi kuma yasa abokan rayuwane Ku har mutuwa ta raba"

Kan Saudart ya kulle sosai don tarasa inda batunshi ya dosa.

Nasiha sosai Abba yayimata mai kashe jiki mamy ma ta Dora da nata, sai Daga baya taji Abban nacewa ansa biki, waikuma bikinta da A.A ban da wata daya kacal.

Diff.. Wutar Saudart ta dauke, tashin hankali wanda bata ta6a tunanin zata shigeshiba tashiga, Aure? AUREN KWANGILA? kenan ya tabbata AUREN KWANGILA zatayi? Kenan ya tabbata A A din zata aura.

Zufa yaita qetomata Daga inda take zaune. Gabanta banda bugun uku uku babu abunda yake.

Sudai su mamy basu wani luraba, koda suka gama mata nasihar suka sassamata albarka sai suka sallameta.

Ahankali ta nufi stairs idanunta na kawo ruwa. Haka taita takawa ahankali har takai sama dakyar tashige wani dakin da babu kowa ciki ta fada kan gado tana lumshe idanu Wanda hakan yaba hawayen idanunta damar gangarowa.

Maido kallonta mamy tayi kan Abba dake kallonta itama adorably.

Rungumeshi tayi cikin farinciki shima ya qanqameta.

Saida ya dagota yaga Ashe hawaye take.

"Subhanalillah Rahma ya haka"

Share hawayen tayi tana murmushi

"Abbansu. Am very happy, words can't express my happiness, Wai yau diyata aka sama biki?"

"Saiki godewa Allah kuma azo afara shirye shirye don wannan biki da alama na manyane"

Dariya sukasa gabadaya nan mamy taita kiran yan uwa da abokan arziqi tana fadamusu shima Abba hakan take awajenshi don Saudart yarinya ce yar gata mai shiga ran jama'a koda yini daya tayi dasu.

Duk Wanda aka gayamawa sai yayi farinciki musanmman idan sukaji Wanda zata aura don aganinsu sun dace dajuna sosai.

A bangaren oga Alhaji shamsu hakan take, don tuni yafara yagama shelar sa bikin ga abokan kasuwancinshi da kuma abokan arziqi.

Nan suma sukaita tayashi murna suna mai fatan alhairi.

A bangaren baby kau labari nakai mata ta danna wani uban ihu tana tsalle.

"At last! At long last!!". Duk Wanda yaganta zaiyi zaton Murnar auren take Saidai ita Murnar nata kashi biyune na farko yayanta zai auri balarabiya kyakyawa mai kirki na biyu zai tafi yabar mata gidan ta wala ta Shana son ranta.

Dagudu ta haye sama ta lalubo wayanta ta dannama Saudart kira.

Saudart kau kuka take hurjanjan tana tunanin makomarta, ringing din wayarta yasata dan tsagaitawa ta kalli wayar, ganin mai kiranta yasata Jan tsaki ta kashe wayar gabadaya tayi cilli daita.

Ganin bata dagaba harta tsinke yasata sake bugawa nan taji switch off.

" Tofah? Halan kunyata takeji" tafada tana ta6e baki.

Datarta ta bude tahau direct Tawuce group din CLASSIC LADIES tayi breaking din news din, zokuga hauka wajensu teema sai kakkafi suke suna kicihi suna fadin yadda bikin zaizama one in town, sukau team Suzy ana la6e Saidai su karanta massages dinsu Amma anrasa wacce zata fito ta tanka.

Suzy kau hauka tuburan tafara dataji labarin sa auren, sai kurma ashar take dana Zage Zage.

Beebah ta dannama kira tana dauka tahau masifeta, ta inda take shiga batanan take fitaba, beebah taita kwantar mata da hankali akan tabari Allah yakaisu gobe har bakery dinta zasuje su tisiyeta.

Dakyar tasamu ta lalla6ata harta haqura Saidai zuciyarta uwa ana hura garwashi...✍

More comments, more post.

Gaskiya aqara flow din comments sunyi kadan.

Aqara ko in nad'e hannu😏

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

024

Mu leqa hajji A.A😕

Kwance yake kan gadon dake dakin Sadeeq, ya wani rigingine yayi matashin kai da hannayenshi idanunshi a lumshe, Kai ka zata barci yake Amma idanunshi biyu hasalima sauraron Sadeeq daketa waya da abokanansu yana gayamusu sa biki yake.

Ya kusan mintuna talatin yana Abu guda, sai bugama mutane waya yake kai kace bikinshine akasa.

Ajiye wayar yayi Bayan yagama sannan yazo gefen Ashraf dake kwance haryanzu ya d'ad'a mashi bugu a cinya.

Bude idanu yayi bashiri ya tashi zaune.

"Kutt.. Dan ubanka ni ka daka?" Inji Ashraf yana kaimashi bugu shima.

Dojewa Sadeeq yayi yana dariya.

"Dan ubanka ka barni sai qone credit dina nake wajen kiran mutane Bayan Kaine ka cancanta kayi hakan"
Chapter 15 · 0% Book details