← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 111

Sashe 42

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A parking space yayi parking suka fito gabadaya, saudart na qarewa gidan kallo, jitake kamar tayi shekara rabonta da 9ja, komai na dabanne da nacan, hatta iskar damuke shaqa yasha banban Dana can.

Driver ne ya fiddo mata kayanta na booth yakaimata har falo ita kuma tana kaisu can dakinta a sama.

Saida suka gama shigar da kayan tsaff sannan drivern yatafi, shikau Ashraf tuni yasake fita don haduwa da sadeeq.

Saida ta kammala komai inda yakamata sannan tayi wani juyi tana fadawa kan gadon

"Bari na kira wannan chali chalin" tafada tana nemo contact din baby sannan ta Danna mata kira.

A bangarensu Ummy kuwa suna zaune baby tayi matashin Kai da kafar Ummy taji wayarta na ringing.

Kamar bazata dubaba saikuma ta daukota tana dubawa.

Wani ihu tayi tana zabura daga kwancen datake a kafar Ummy har saida Ummy tadan firgita.

"Oh my God! Wlh anty ce, itace!" Tafada tana qara ware idanu tana kallon screen din wayarta.

"Wannan wane irin hauka ne baby?" Inji Ummy a qule

"Sorry Ummy, kalla wlh anty ce da number Nigeria, kenan sun dawo? Bari na daga karta tsinke" tafada tana daga wayar.

Ihu ta challarawa saudart cikin kunne Wanda saida saudart ta janye wayar daga kunnenta tana dariya.

"Aunty? Dagaske kece? Yaushe kuka dawo? Shine ko agayamana ko? To munyi fushi" inji baby tana kallon Ummy dake kallonta itama fuskarta da murmushi

"Ayyah autar mata, am soo sorry, surprise mukayi muku, kuma wlh dawowarmu kenan, ina Ummy?"

"Gatanan tana jinki, abata?"

"Eh bata"

Nan ta miqama Ummy wayar

"Aslm alaikum" inji Ummy cikin muryarta mai cikeda natsuwa da kwarjini

"Wslm Ummy, barka da wuni Ummy" inji saudart cikin ladabi

"Barkanki dai daughter, ya kuke? Ya hanya? Wannan surprise visit haka?"

Dariya saudart tadanyi tana cewa
"Ayyah Ummy, kuyi hqr, surprise mukayi muku"

"Ai babu komai, surprise Nada dadi ai, amma da kun fada da na turo baby ta gyara muku gidan kafin Ku iso"

"Ayyah Ummy, babu komai ai, zanyi besides gidan bawani qura yayiba sosai"

"Dukda haka bari tazo ta kama maki, kunsha hanya kuma sai a Dora da wahala? Bari tazo yanzu"

Nan sukadan ta6a fira, itakau baby tanajin maganar tafiya daman ta haye sama dagudu don shiryawa.

Cikin dan qanqanin lokaci saigata ta sauko cikin shirinta, lokacin har sun gama wayar, ta amshi wayarta tayimata sallama sai rawar jiki take sannan ta fice.

Saudart taji dadin zuwan baby sosai don tare suka gyara gidan kuma tasata nishadi sosai, surutu kau kamar an kunna radio, saida suka gama sannan tayimusu girki suka zauna sunaci tana gwadamata hotunan dasukayi dasu Reyna a supermarket, baby sai santin hotunan take.

Sai wajajen isha'i driver yazo daukar baby, nan ta hadata da tsarabar datayo musu, trolley qananu biyu.

Sosai baby tasaki baki tana kallon kayan don batayi zaton sunkai hakaba.

Zata fara qorafi saudart ta hayewarta sama tana cewa ta gaida Ummy ta maida kofa ta rufe.

Babu yadda ta iya haka ta kwashi kayan tafito suka wuce.

Agida ma saida Ummy tasaki baki ganin tsarabar, trolley daya na baby daya nata.

Shaqe kowanne yake da gown gown masu kyan gaske sai kayan kwalliya da mayamayai a trolley din baby Itakuma Ummy turarruka da takalmi masu kyan gaske.

Suna zaune suna duba kayan Ashraf yashigo.

Shima bin kayan da kallo yayi don besan dasuba.

Saida ya zauna suka gaisa sannan Ummy tafara mashi qorafin kayan sunyi yawa, anan ya nunamasu shi bema San dasuba.

Sosai Ummy taji dadin abinda saudart tayi kuma hakan ya linka soyyayar datake mata ada.

Nan take ta kirata tana mata qorafin kayan sunyi yawa, itadai iyakarta dariya batace komaiba, sai daga baya Ummy tayimata godiya sosai kamar irin uban kayan nan akayimata amma kasancewar duk qanqantar alhairi dadi ke gareshi yasa taji dadi sosai.

Ashraf kau duk wayar dasukayi yana jinsu, sai bin kayan yake da kallo yana mammakin halin saudart.

Meyasa take son ahalinshi? Meyasa bata tsanesu ba kamar yadda ta tsaneshi?
Meyasa take girmama ahalinshi bayan be dauki nata a bakin komaiba?
Ko sau daya be ta6a takawa gidansu ba ko wajen daddy ko mamy da niyyar gaisuwa tun bayan aure, be ta6a zuwa ba bare su saba dajuna amma gashi ita tazama kusan jininsu don yana ganin zallar qaunar dasuke mata dakuma Wanda take masu.

Haka yabar gidan jiki a sa6ule, kwakwalwarshi chunkushe da tunani Kala kala, yanajinshi cikin wani yanayi marar misaltuwa.

Koda ya isa gida har goma takusa, be isketa a faloba kamar yadda yayi tsanmmani.

Kashe wutan falon yayi ya haye sama ahankali.

Kofar dakinta dake rufe ya tsaya yana kallo batareda yasan dalili ba.

Ada babu ruwan shi da dakinta don gar mantawa yake tana nan, amma yanzu jiyake kamar yaje ya bubbuga ta fito yaganta.

Ya Dade yana kallon kofar sannan ya sauke ajiyar zuciya ahankali ya murda handle din kofar dakinshi yashiga jiki a mace.

A ranar haka yaita juye juye yana tunane tunane har barci barawo yayi awon gaba dashi.

Washegari basu hadeba, lokacin data fito harya fita, office dama sai Monday zatayi resuming don haka yau gida zata ta wuni.

Taji dadin zuwanta gida don murna sukayi tayi dasuka ganta kamar su maidata ciki, Suma tsarabarsu ta fiddo musu ta basu sai murna suke.

Anan tayini sukasha firarsu sannan da marece as usual tawuce mall din daddy.

Sosai daddy shima yayi murnar ganinta sai nan nan yake daita ya rasa inda zai sata don murna.

Shima yasha tsaraba danginsu agogo, takalmi, turarruka da sauransu.

Ba ita ta dawo gida ba sai bayan isha'i.

Koda tadawo shi be dawoba don haka hayewarta tayi sama.

Shima kamar jiya saida ya Dade yana kallon kofarta Yanajin inama ta fito daidai lokacin yaganta.

Ya rasa dalilin son ganintan amma kawai jiyake yanason kallon fuskarta, rabonshi da its tun jiya amma jiyake kamar yayi wata be ganta ba.

Saida yagaji da tsayuwa sannan yasa hannu yana shafa kanshi ahankali

"Ya rabb, take it easy on me" yafada yana kallon kofar again, sannan yayi ajiyar zuciya ya bude nashi kofar yashige.

Agurguje🙏

Yau Monday.

Rabon da Ashraf yasaka saudart a idanu tun ranarda suka dawo daga Spain.

Yau kwana hudu kenan, tun yana daukan abinda yakeji a wasa har abin yafara bashi tsoro.

Sosai yabi ya sussuce don ma miskiline shiyasa ba'a ganewa amma shi kadai yasan abinda yakeji.

Gashi gida daya suke amma miskilancinshi ya hana yaje wajen ta yaganta don gani yake hakan kamar zubda ajine.

Itakau saudart har mancewa take ma dashi don a ranakun nan tashiga busy ba kadanba, shi kadai ke haukanshi don wani sa'in mancewa takeyi da wanzuwarshi.

Tunda wuri ya shirya yau yawuce office badon komaiba sai don yaganta, he was glad cewa finally zai ganta tunda dole yau tazo aiki.

Haka yaci gayunshi cikin grey suit Wanda yayi bala'in amsarshi sannan yafice.

Saidai me? Yana zuwa company wani mummunar labari ya riskeshi Wanda yayi matuqar girgizashi.

Yayi parking din motarshi ya hayo sama cikin nishadi da Farincikin zaiga muradin idanunshi.

Saida ya kalli empty office dinta yaga wayam batanan sannan ya kalli agogon hannunshi yaga duka duka 7:45

Murmushi yayi yana shafa kanshi ganin uban safkon dayayi saboda ganinta.

Office dinshi yashiga Wanda yake qal qal sai zuba qamshi yake.

Be Dade da zamaba saijiyayi an bude kofar batareda anyi knocking ba Wanda hakan yasashi saurin dagowa don duk a tunaninshi saudart ce.

Ganin sadeeq ne yasashi binshi da kallo ganin kamar fuskarshi na daukeda damuwa.

Ahankali sadeeq ya qaraso gabanshi fuskarnan a dagule babu fara'ar nan babu tsokana da shaqiyanci.

"Kai kuma fa lfy?" Inji Ashraf yana kallonshi

Bece mashi komaiba sai wata takardar daya ajiye mashi agaba yana kallonshi.

Ganin hakan yasashi dauka tareda dubawa.

Abinda yagani yasashi zabura tsaye yana ware idanu

"What!" Yafada cikin firgici yana sake ware idanu akan takardar

"Am sorry Ashraf" inji sadeeq asanyaye

"Innalilahi waina ilaihi rajiun, innalilahi waina ilaihi rajiun, innalilahi waina ilaihi rajiun" yafada cikin dimuwa...✍

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

053

Jiyayi kaffafuwanshi na Neman Gaza daukanshi yasashi komawa ragwaf akan kujera yana cigaba da maimata innalilahi

"Ashraf please don't take it easy on yourself" inji sadeeq yana Qarasowa wajen shi yana dafa kafadarshi

Kasa magana yayi sai kallon takardar dayakeyi

"Sadeeq how come? Garin yaya hakan yafaru?" Ya tambaya cikin surewa

"Destiny.. Ashraf qaddara ce, please kayi tawwakali, Allah shine me badawa kuma mai amshewa, shiya hallici riba da faduwa" inji sadeeq cikin tattausan laffazi

"Sadeeq kasan millions nawa nayi asara? Why? Why me?" Yafada yana dafe kai zuciyarshi na wani irin quna

"Kayi hqr Ashraf, bakai kadai kayi asara ba harda su, remember Rabin kudin ka bada, kaga kenan Suma sunyi asarar, tunda matsayin Suma Rabin kudin sukayi asara" yafada yana dan murza kafadarshi.

Dafe kanshi yayi da hannu biyu ya Dora a desk zuciyarshi na tuquqi

"Why? Jirgin betashi collapsing ba saida ya dauko kayana? Ya Allah wannan wace iriyar qaddara ce?" Yafada cikin matuqar surewa.

"Ashraf please karkayi sa6o, ka dauki qaddara please, wannan na cikin cikar imaninka, qar6ar qaddararka aduk yadda tazo maka" inji sadeeq cikin jimami.

Ringing din wayarshi ce ta katse su.

Kasa dagawa yayi hakan yasaka sadeeq dagawa yasa hands free.

Labari dayane, can su Hussain suka bugo suke fadamashi yadda abin yafaru har jirgin ya jirkice cikin ruwa, kuma ba'a tsira da komaiba.

Ashraf na sauraron su amma yakasa cewa komai har suka gama wayar, he felt soo empty don sosai ya zuba dukiyarshi hundreds of million don aganinshi sana'ar ta samuce.

Sunanan jugum jugum sukaji ana knocking din kofa.

Kamar yadda ta saba knocking uku tayi sannan ta bude ta shigo.

Turus tayi ganin su jigum jigum, hakan yasata Qarasowa ciki ahankali tana kallonsu.

Dauke kai yayi daga kallonta zuciyarshi na tafasa don yanzu besan ganinta musanmman da zuciyarshi ke kitsima mashi wani Abu.

"Good morning" tafada tana kallonsu daga wannan zuwa wannan.

Sadeeq ne yayi qarfin halin qaqalo murmushi ya nunamata wajen zama yana cewa

"Morning miss, please sit"

Zama ta qarasa tayi tana kallon Ashraf daya kauda Kai gefe sannan ta maida kallonta kan sadeeq da alamun tambaya a fuskarta.

"Mr sadeeq, hope everything is ok?" Ta tambaya innocently
Chapter 42 · 0% Book details