Sashe 12
Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dagowa yayi suka hada ido nan Kowanne yasakarma juna murmushi.
"Ummy dakanki? Da kin aiko nazo" yafada yana matsarda laptop din Daga gabanshi.
Zama Ummy tayi gefen gadon tana murmushi.
"A'a babana, ba gashi nazoba? Tundazu nake baza idanu kozaka shigo Amma shiru shiyasa nabiyo sahu"
"Wlh Ummy wani aiki nakeyi saura kadan ma in qarasa shut ban fitoba, ina kwana" yafada yana matsowa kusada ita tareda yin matashin kai da kafarta.
"Lfy lau, ya gajiyan jiya? Shine kadawo ko kashigo?"
"Wlh Ummy agajiye nadawo ne kuma nayi tunanin kun Riga kunyi barci ne"
"Ayyah, to ya partyn ya tafi?" Ta tambaya tana shafar sumanshi dake kwance luff luff.
"Great, anyi taro lfy an tashi lfy"
"Yayi kyau, shine kuma mu Saidai muji a salensa? Daka fara gwada mana budurwarka gwara ka fara gwadama duniya?"
Shiru yayi don dama yasan arina.
"Dakaifa nake son, yanzu fisabillilah Saidai muga photonku kaida budurwarka a t.v ko sanin da ita bamuyiba? Ka kyauta kenan?"
"Ummy bahaka bane.."
"To yaya ne? Uhm? Wato mu munanan kabarmu munata haukanmu Duk yarinyar Dana kawoma kace bata yimakaba Ashe kanacan kana campaign wani wajen"
"Ummmy..."
"It ok, ai hakanma daidai ne, ni dama bason tilastama nakeba, nafi son ka za6o za6inka, kuma gaskiya tayima, ina ganinta ta kwanta min, yaushe zaka kawota muganta"
"Haba Ummy Bayan ganin da kuka yimata yanzu?" Yafada yana turo baki zuciyarshi fall da haushi.
Dungure mishi kai tayi
"Wato rowarta zakayi mana ko? To Baka isaba, dolene ka kawota muganta tunda Allah ya tona asirinka, Ayi a sanya biki Ayi auren dama ka isheni da shagwa6arka, gwara ka qara gaba matarka taji dakai niba inji da autata" tafada cikin sigar tsokana.
Tashi zaune yayi yana turo baki cikin shagwa6a.
"Dama Ummy batun yauba nasan kin gaji daniba, ba komai" yafada yana juyamata baya.
Dariya Ummy tayi tace "atoh ba dole in gaji dakaiba mutum godai godai dashi sai ta6ara, kaiba autaba Amma ka kwacema autata autanci, oya tashi muje muyi break"
Tafada tana kamo kunnenshi,
Dan qara yasaki cikin raki, hakan besa tasakeshi ba har saida suka fito sukazo har dining.
Baby daketa faman maida yadda akayi a wani group dinta mai taken CLASSIC LADIES akan hotunan data Dora a status.
Ganin fitowarsu yasata saurin kulle datar ta ta ajiye wayar ta nutsu.
Sai kicin kicin kwace kunnenshi yake ganin Baby a dining Amma Ummy taqi saki saida ya zauna sannan tasakeshi sannan itama ta zauna kusadashi.
"Ina kwana yaya?" Inji baby a nutse.
Cikin cin magani yace "lfy"
Ta6e baki tayi cikin zuciyarta tana cewa "kaji dashi, Amma da agaban babyn taka kake da fuska kamar gonar auduga"
Serving dinshi Ummy tayi ta turamashi, shima turomata yayi yana tsuke baki.
Girgiza kai tayi tace "matarka dai tabani, wannan ta6arar taka ai ko auta albarka"
Baby cikin zuciyarta tace "aikau dai, ai harna tausaya mata, Kodayake mace fa shu'umace idan tasan takan aiki shi zaizama bawanta, Nidai Allah yasa Ayi agama dawuri kona sarara, kai zamusha biki sai gwargwarona ya dinga yima mutane daquwa, zamu sha zanku" Duk cikin zuciya take wannan zancen azahiri kau murmushi take.
"Ke!"
Firgigit tayi Daga daydreaming dinta ta dago ta kalleshi.
"Get lost!" Yafada bawasa a fuskarshi
"Haba son. Metayi kuma?"
Shiru yayi bece komaiba
Shan ruwa tayi sannan tamiqe ta dauki wayarta tabar wajen don shine rufin asirinta don kallon dayake watsamata ya isheta.
"Hmm Allah ya shiryeka son, yarabaka da wannan baqin ran"
Bece komaiba ya cigaba da amsar abincin datake feeding dinshi.
Shiga daki tayi tana gunagunai tana harare harare.
Ringing din wayarta ne ya katseta
Ganin mai kiranta yasata sakin ihu sannan ta Daga.
Ihu aka saki Daga dayan 6angaren, itama tasaki nata sannan suka kyalkyale da dariya kamar sabbin kamu.
"Shegiya, haka akayi? Dazu nahau naga hotuna"
"Kedai bari sis, na dasa bomb" inji baby tana dariya.
"Aikau yadasu, hawo kiga bala'i. Gasu team dinsu Suzy can sai ashar suke saki, group ya hargitse"
Waro idanu baby tayi
"Haba?"
"Shegiya ai kyace hakan Bayan kin dasa bomb kin tsere"
"Wlh Ummy takirani nafita yin break Amma bari nahau.."
Ding.. Ta katse wayar, har kyarma take wajen bude data tashiga WhatsApp.
Waro idanu tayi ganin massage sunfi 200 Daga saukanta zuwa yanzu.
Bi taita yi tana kallon abubuwan dasuke tattaunawa akai tanacin dariya saboda yadda su team Suzy suka fito da Kishi qarara suna masifa.
Saida tagama bi sannan ta tura wani sticker na baby tana hura chewing gum.
Ai ana ganinta group yaqara hargitsewa, nan Abu yadawo sabo don tsagerune suka hadu, sai shaqiyanci suke suna qara cusama qawayen Suzy haushi.
"Babban goro sai magogin karfe, sama tayiwa yaro nisa Saidai yatada kai yayi kallo, yayana alluran cikin ruwane, ruwanma na kogi mai rabo ke dauka" inji baby cikin shaqiyanci
Teema qawarta dasuka gama waya yanzu tace
"Fadi da ihu ki qara da wayyo yar uwa, yayanmu sai balarabiya mai natural kyau ba dangin bleaching da qonewar fata ba"
Wata cikin qawayen Suzy tace
"Ji tura kai ba kwarjini, su kalan dangi anji jiki, Wai yayanmu lol"
Baby tayi charaf tace
"Ai kalan dangima iyawace, idan fitsari banxane kazama tayi"
Wata princess Amee cikin qawayen baby tace
"Anayi ina jin nice ana bari inajin haushi" ta Dora sticker gwalo.
Haka sukayitayi Daga baya taranmasu qawayen baby sukayi kasancewar qawayen Suzy bawani yawa ke garesuba, gashi sun fisu baki. Dole suka sauka suka kyalesu.
Duk abinda ake Suzy na kallo tana kuma saurare.
Ta Kasa yarda da abinda takeji kuma take gani.
Ashraf dinta? Ashraf dinta dawata?
Ashraf dako kallo saitayi dagaske yake kallonta shine take ganin pics dinshi da wata da sunan ita zai aura?
Cabdi aikau za'a yita...✍
Wata sabuwa😳
Ummin fasihu ce🧚♀
🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)
Yaa Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)
Ya Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲
Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)
020
Girrr! Girrr!! Girrr!!!
Kamar bazata daukaba saikuma ta Daga ta kara a kunne batareda tayi magana ba.
"Suzy? Wai ina kika shiga ne abubuwa nata faruwa baki ko fitowa, shin kinma san abinda ke faruwa kuwa? Ki hau yanar gizo kisha news"
"Nasani Beebah, a tunaninki Duk abinnan da'akayi bansaniba?"
"Au kinma sani kenan, to zokiga yadda waccan qallemar ke cimana mutunci a group da ita da tsinnanun qawayenta"
"Duk Nagani beebah yanzu ni batasu Nike ba, wlh ni kadai nasan yadda nakeji acikin zuciyata, beebah Ashraf yaci amanata, Ashe Duk abinda nake aikin banzane yana can yana bin wata?"
"Hmm kya qara gani ai, ina kaiki kina kauce hanya, a tunaninki shima ba zuciya ke cikin kirjinshiba da bazai fada son wataba?"
"Hmm wlh beebah am broken, tunda naga wannan abun Nike cikin damuwa, nama Kasa tashi inyi komai, beebah kiban shawara, please me zanyi? Mezanyi in mallaki Ashraf? Me zanyi in mallakeshi ni kadai?" Ta ida zancen tana sakin kuka.
"Kuka? Kuka fa kike Suzy?"
"To mezanyi beebah, I've loose Ashraf for good"
"Ya da saurin karaya? Ashraf nakine ke daya, ki sanya wannan aranki, babu wacce ta isa ta rabaki dashi. Kedai kawai ki cigaba da bin Duk yadda nace"
Haka taita rarrashinta har tasamu tayi shiru sannan sukayi bankwana akan zata shigo su tattauna akan lamarin.
Saukowa take tana tafe tana zira hannun hijabinta.
Sanye take cikin atamfa mai zanen kalar fari da purple, dinki Riga da skirt pieces, sai farar three quarter din hijab mai hannu wanda yake daidai gwiwa.
A falo ta tarda daddy yana kallo.
Qamshin turarenta ya fargar dashi isowarta.
"Wow shalele, kinyi kyau"
Dariya tayi tana qarasawa wajenshi ta zauna kusadashi.
"Daddy ina kwana?"
"Lfy qalau shalele, ya gajiyan jiya"
Shiru tayi bata amsaba.
"Shalele kinga yadda aketa nuna hotunanku a t.v kuwa? Cab! Wlh kunyi kyau gashi sai nannata sunanki ake dakuma bakery dinki kinga ko anan ma kinyi tallar bakery dinki ga wadanda basu saniba"
Hmm kawai ta iya cewa tana kauda kai.
"Shalele, wannan auren alhairine agareki kai ga dukkanmu gabadaya, ji Tun kafin Ayi auren ma harmun fara ribantuwa inaga anyi auren."
"Hmm dad sai wani nanata Kalmar aurennan kake kamar wani mai dorewa, auren da na lokaci ne?"
"Eh na lokaci ne, Amma ai kana naka Allah na nashi, wayasani ko yazama dorarren"
"God forbid! Allah ya tsareni, ko maza sun qare bazan iya zama dashiba Wai da sunan aure na dindindin, me zanyi da wanda besan darajar mutane ba"
"Haba shalele, ki dinga yiwa mutane uzuri, a yanzu bazaki fahimci halayenshi ba saikun zauna tare"
"Aikaudai, dad bari Kaga in qarasa, na kwana biyu ban leqa bakery ba"
"To Shikenan Allah ya karemin ke sweetheart"
Peck tayimashi tana cewa "Amin sweet daddy".
Tunda tashigo bakery din ta lura da irin kallon da ake binta dashi Wanda bata saba ganiba.
Sharewa tayi ta cigaba da aikin gabanta, tana nan zaune maryam P.A dinta tashigo da sallama.
Dagowa tayi tana amsawa fuska sake.
Gaisheta maryam tayi cikin girmamawa sannan tafara gabatar mata da ordern da akayi kwana biyun da batazoba.
Saidai Saudart nalura da kallon da maryam din kemata wanda yasha banban dana.
Saida suka gama, har maryam tajuya zata tafi saikuma ta tsaya.
" uhum? Wani Abu?" Inji Saudart
"A'a ma'am, kawai..kawai tayaki murna zanyi"
"Murna? Ta me?"
"Yau.. Yau dasafe naga hotunanku da fiancée dinki, congratulations"
Sai a sannan Saudart tasan dalilin kallon da aketa binta dashi.
"Oh thanks"
"Allah ya sanya alhairi yakawo zuri'a dayyiba"
"Ok jeki Ku qarasa dan Allah kinsan ba isashen time ne garemu ba" tafada batareda ta amsa addu'arta ba
A ladabce ta juya tafice, ta6e baki tayi, ta maida hankalinta kan aikin gabanta.
Wajajen karfe uku tana tsaka da aiki aka bubbugo kofa
"Yes come in" tace kanta kan rubutun datake.
Maryam ce tashigo
"Ma'am kinyi baqi"
"Baqi?"
"Yes ma'am"
"To? Kishigo dasu"
Da to ta amsa tafita can saigata tasake shigowa dawasu yanmata biyu biye a bayanta.
"Yeah! Antynmu!" Inji Baby tana rugawa wajen Saudart ta rungumeta.
Kasa motsawa Saudart tayi don mammaki.
Sakinta baby tayi tana dan jabaya tana kallonta.
"Wow! Wlh anty kinfi kyauma azahiri, Wai kin ganki?"
"Mtcheew Wai baby zaki nutsu ne kokuwa?" Inji teema da takaicin rawar kanta