← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 111

Sashe 71

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sadeeq ma was totally shocked, kallonta kawai shima yake yana son hango bakin gaskiyarta ta cikin idanuwanta.

"Saudart?" Kawu ibrahim ya kirata.

Ahankali ta dago kanta daga sunkuyen dayake ta kalleshi sai kuma ta maida kan qasa.

Daddy kau sai kallon diyar tashi yake yana karantarta

"Meyasa kika amince da cigaba da zama da Ashraf?" Ya jefa mata tambayar yana kallonta.

Shiru tadanyi na yan daqiqu sannan ahankali tafara cewa
"Saboda aganina dakuma tunanina wannan auren hadine na Allah, akwai manufofi da dama acikin wannan auren, ta dalilinshi abubuwa da dama sun warware, zumuncinda ya dade da watsewa yana neman cigaba ta dalilinshi, wannan ba komai bane face ikon allah" ta qarashe maganar asanyaye

"To amma Ashraf fa? Kina sonshi? Shifa aure ba'a zamanshi akan wani dalili kuma baya dorewa idan babu soyayya, wadanda akayi na soyyayama yaya aka cika bare wannan wanda dalilinshi bekai hujja ba, gashi shi da kanshi yafadi abubuwa dadama dayamiki marar dadi a dan zamanku, kina ganin baxaki dinga tunawa ba duk in kin ganshi?"

Hadiye yawun daya tararmata a maqoshi tayi sannan tabude baki dakyar, allah ma yasan dauriya kawai take amma ita kadai tasan me takeji acikin zuciyarta.

"Kawu kamar yadda nafada, qaddara dakuma ikon allah ne ya hadamu, Ashraf... ya bijiro da wannan abun ta dalilin fansar dayakeson daukane, da ba'ayi auren ba akazo har yanzu da haryanzu yana ciki da daddy, yakuma yimana abubuwane bisa rashin sani, da yasan gaskiya nasan baxaiyi hakaba, so kuma allah kesawa azuciyar mutum ya musanya qiyyaya da so alokaci daya kuma... hakan na iya faruwa" ta qarashe zancen taba lumshe idanu, maganarnan datake ita kadai tasan yadda takeji, sosai zuciyarta ke zafi yayinda ita kanta tasan qarya take shirgamasu don batajin akwai ranarda zata ta6a kallon ashraf da sunan so.

Tunda tafara magana dama ashraf ya dago yana kallonta, he can't believe she's saying all these. Atunaninshi yanzu zata qara tsanarshi ne dataji cewa yana amfani daita ne dan daukar fansa, atunaninshi tsanarshi zata qara hauhawa ne acikin zuciyarta, ashe zata fahimceshi? Ashe zata bashi second chance? She look soo real that yakasa gane she's just framing up ne. Kallonta kawai yake wani sabon kaunarta nasake huda zuciyarshi.

"To alhamdullilahi, yanzu dai kowa yaji amsarta data bada da bakinta da kuma dalilanta, me zakuce?" Inji kawu ibrahim yana kallonsu.

Ajiyar zuciya abba ya sauke yace
"Masha allah, haqiqa dalilanta abin dubawane kuma babu abinda ke ciki sai gaskiya, fatanmu anan shine allah yasa hakan shiyafi alhairi kamar yadda tafada da farko"

Daddy ma yace
"To alhamdullilah, gaskiya naji dadi sosai da faruwar hakan fatanmu allah yabada zaman lfy ya kauda fitina kuma yaqara danqon zumuncinmu"

Kawu zahradini shima yace
"Amin amin, nima nayi farinciki qwarai da hakan allah ya tabbatarda alhairi"

Umma da bata cika magana sosai tun sadda sukazo tace "masha allah allah yabada zaman lfy, ya tabbatar da alhairi"

Kallonsu suka maida gabadaya gun ummy datayi zugum cikin damuwa kawu ibrahim yace
"Kefa? Bakice komaiba"

Ajiyar zuciya ta sauke ahankali sannan ta kalli saudart da kanta ke qasa sai kokowa take da hawayen dake neman tonamata asiri sannan ta maida dubanta kan ashraf dashima kanshi ke qasa sannan tace
"To allah ya tabbatar da alhairi yakuma sanya albarka aciki"
Duk aka ansa da amin cikin farinciki.

"Kaifa oga gauro? Baxaka tofa naka albarkacin bakin ba?" Inji kawu zahradini yana kallon sadeeq.

Murmushi yayi a kunyace sannan yace
"Allah yabada zaman lafiya, ya kauda fitina"

Duk aka amsa da amin.

Itadai saudart kanta na qasa amma zuciyarta inbanda suya babu abinda take, tasan tayi wauta sosai, wautar da har ta mutu bazata bar ganin sakamakonta ba, ta ida wargaje rayuwarta da hannunta, ta ida tabbatar wa kanta bazata ta6a yin rayuwar auren da ta dade tana tsarawa kanta ba. Shikenan bakin alqalami ya bushe, there is no going back.

"To alhamdullilah yanzu sai ayi maganar tarewa ko? Koko sai munsake shagalin biki tunda wancan na contract ne wannan kuma na gaskiya?" Inji kawu ibrahim cikin sigar tsokana.

Duk dariya sukayi inka cire saudart da ashraf sai ummy data murmusa, shikau sadeeq duka 36 dinshi suna waje don dariya.

"Duk yadda kukayi ai daidai ne" inji daddy cikin fara'a

"A'a badai yanzu ba, abari amarya tagama shirye shiryenta sannan, su da kansu zasu bamu lokaci" inji umman sadeeq tana murmushi.

Haka dai suka gama tattaunawarsu wanda saudart kawai jinsu take, aqagare take awatse ko tasamu ta ke6e taci kukan dake cinta yadda ya kamata, lumshe idanu tayi jin kanta na dan sara don hayaniyartmsu ma kanta bataso.

Sadeeq kau a 6angarenshi sai mintsinin ashraf dako kwakwarar motsi beyiba tundaxu yana mashi rada saidai ko kadan be nuna yasan yana yiba, farincikin dake ranshi kawai ya isheshi.

Yanajin yadda mutanen falon suke tashi suna barin falon har yarage saura sadeeq kadai sai shi da saudart, wani mintsini mai uban zafi yaqara mashi sannan shima ya tashi yafita.

Murmushi yadan saki wanda saika lura zakasan yayishi sannan ya daga kai yabishi da kallo harya fice yaja musu kofa.

Ajiyar zuciya yasaki marar sauti sannan ahankali ya maido dubanshi kanta.

Tana dai yadda take, zaune lullu6e cikin makekiyar hijabinta kanta a qasa.

Kallonta yake babu ko kyaftawa yanajin wani shauqi acikin zuciyarshi, be ta6a tunanin abubuwan zasu zo da sauki ba haka, a tunaninshi idan tasan gaskiya komai dagulewa zaiyi ashe ba haka bane, ashe zata yafemashi, ashe zata fahimceshi, ashe zata bashi dama.

Motsi yake da baki amma yakasa fadin komai, yarasa ta ina zai fara, yarasa da wacce kalma zaiyi amfani, kallo daya zaka mashi kasan a diririce yake.

Soyake tadago ya kalleta, ya kalli fuskar dake sashi cikin shauqi, fuskarda be gajiya da kallonta, fuskar da ke sashi cikin nishadi.

Ahankali yayi parting din pink lips dinshi cikin muryar rada yace
" *SAUDARH*"...✍

Ngd qwarai da addu'o'inku gareni, allah yasaka ma kowa da mafificin alhairi (amin)

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️
👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)

080

Bata ko motsaba bare asaka ran xata dago daga sunkuyar da kan datayi.

Shiru yayi yana kallonta, he can't believe yanzu tashi ce har abada, atunaninshi izuwa yanzu alaqar dake tsakaninsu tagama yankewa, yariga yacire rai da samunta don atunaninshi abune marar yiwuwa amma dayake allah me yin yadda yaso ne, gashi ya maida impossible zuwa possible.

Kallonta yake wata iriyar soyayyarta na fizgar zuciyarshi, jiyake kamar ya rungumeta a qirjinshi yaita fallasa mata sirrin zuciyarshi gameda ita.

"Thank you" yafada ahankali idanunshi akanta

"Words... can't express how am feeling right now, i feel i am the luckiest person in this world... thanks for choosing to stay with me...forever, thanks for forgiving me, thanks for.... everything" yafada cikin romantic tone.

"I promise... saudarh i promise to make you happy, i'll make sure you'll never regret your choice" yasake fada, kallo daya zaka mashi kasan he meant what he's saying.

Ahankali ta dago idanunta harta saukesu cikin nashi.

Janye idanun tayi tana sakin wani slight murmushin takaici kafun tace
"Regret? Dana sani yanzu nafara shi and babu ranar gamashi, farinciki kuma banasa ran zan qara dandanashi saidai inga wasu nayi, rabona dashi tunda kashigo rayuwata kuma muddin kana cikinta bazan ta6a qara dandanashi ba, kar kayi tunanin wani abu ya chanza gameda yadda nakeji akanka, koda yake ya chanza din, ya qara hauhawa, hawan da baxai ta6a saukaba, dole kaji you're the luckiest man in the world don ka mallakeni saidai point of correction anan shine bani ka mallaka ba *gangar jikina* ka mallaka, kuma dashi zaka rayu har sadda sila zai rabamu walau mutuwa ko wani abun.

Kaci nasarar samuna amma bazaka ta6a cin nasarar samun zuciyataba, bazaka ta6a samun kofa azuciyataba komin qanqantarta bare kakai ga shiga, remember bakada quality din mallakar zuciyata na ta6a fadamaka haka, you've not reached that standard and you'll never reach it, zaka rayu da gangar jikina ne... har abada"

****************************************************

Lumshe idanunshi yayi ya bude ganin sadeeq na horn abakin gate dinsu.

Haryanzu magangganunta sunqi daina yawo a kunnenshi, sunqi daina mashi zafi azuciya.

Me zaiyi? Me zaiyi ta dena tsanarshi? Meyayi da zafi haka da bazata iya bashi second chance ba? Atunaninshi komai yazama tarihi ashe da sauran rina a kaba? She still hate him har tana ikirarin bazai ta6a samun zuciyarta ba? Wai gangar jikinta kadai ya mallaka? Meyasa ta yarda tacigaba da zama dashi bayan tasan babu abinda ya chanza daga tsanar datake mashi? Meye dalilinta na yarda? Waya tilastamata? Ya zaiyi? Ya zaiyi da sonta daya nacemashi yaqi fita a zuciyarshi? Ya zaiyi?

Dafa kafadarshi sadeeq yayi don ya dade da parking su ummy har sun fita.

Ahankali ya dago ya kalleshi a sanyaye.

"Are you ok?" Inji sadeeq softly

Ajiyar zuciya ya sauke sannan yasa hannu ya bude murfin kofar batareda yace komaiba yafita yarufo kofar yanufi cikin gida.

Da kallo sadeeq yabishi sannan shima yafito daga cikin motar yarufe ya maramashi baya.

A falo ya iskesu duka baby sai tsallen murna take tana ihun murna cikin siririyar muryarta da alamu dai an fesamata abinda ya faru.

Ganin sadeeq yasa tabar tsalle tsallen ta kauda kai still murna fall fuskarta.

Tashi ashraf da babu abinda yakeso awannan lokacin kamar kadaicewa yayi yana cewa zai hau sama.

Da to suka bishi dashi suna kallonshi don yanayinshi is something else dukda kai tsaye bazaka ce yana cikin damuwa ba, kawai dai ba yabo ba fallasa saidai kallo daya zakamashi kasan asanyaye yake.

Cigaba da zubamasu surutu baby tayi tana masu tambayoyi uwa yar jarida duk na saudart kamar ya takoma yanxu? Yaushe zata dawo ddss.

Itadai ummy ko kallonta batayiba umma ce mai biyemata sai sadeeq daya tisata gaba da tsokana tana ramawa.

Hakadai suka kasance cikin raha kowa kagani yana cikin farinciki don fuskarsu ma takasa 6oye hakan, jisuke yau rana ce ta musanmman agaresu, ranar farinciki.

Knocking din kofar akayi ahankali, ko ba'ayi magana ba tasan daddy ne hakan yasa tayi saurin gyara zamanta tana goge hawayen fuskarta.

Murda handle din kofar akayi yashigo da sallama.

Amsawa tayi ahankali tana qirqiro murmushi.

Qarasowa yayi cikin dakin idanunshi kafe da ita harya iso gaban gadonta ya zauna daga dayan gefen yana kallonta.
Chapter 71 · 0% Book details