← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 111

Sashe 19

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta ruga dagudu ta rungume Saudart tana tsalle kamar wata yar yarinya, Saudart namata dariya.

Sukau Nafeesa sagale sukayi suna kallonsu, musanmman baby dabasu saniba, shigartama kadai zai saka sanin yar Masu kudine ga fatarta dake sumul sumul alamun Hutu.

"Wow! Antyna kinganki? Wlh kin hadu! Bari muyi selfie yau akwai status"

Tsaki Saudart taja tana tureta

"Kekam Allah ya shiryaki baby, ke kenan daukan pics da dorawa status. Nikam banso"

"Haba aunty please"

"A'a nikam"

"Wayyo Ummy, wlh anty kuka zanyi" tafada tana zaman yan bori kan gadon dakin tana kwa6e fuska.

Kallon juna Nafeesa da mardeeya sukai sannan suka maida kallon kanta.

"Please anty*

"Ok Amma kwara daya".
Ihun murna tayi ta taso taciro qatuwar wayarta ta kashe Masu selfie.

" wow! Wlh yaya ya iya za6e wlh kinma fishi kyau"
.tafada tana Dora hoton a status da caption din *me and my cute in-law*

Sai a sannan ta lura dasu mardeeya daketa kallonta, suna hada idanu suka janye idanu cikin basarwa.

"Laa, anty suwaye wadannan naga kunadan yanayi"

Murmushi Saudart tayi tana shafa mai tace
"Cousins dinane"

"Wow! Hyy" tafada tana Daga musu hannu fuska fall murmushi.

"Hyy" suma suka amsa suna mata murmushi.

"Kuna kama wlh Saidai Antyna tafiku kyau"

Yatsina fuska Nafeesa tayi tana cewa
"To kina buqatar spec sbd da alama biki kike gani, wannan ai itace hajiya munin cikinmu"

Baby nasamu abinda akeso, aka wani gyara zama sannan akace

"Wa? Ca6 in-law ai ta dabance, kyawunta kamar watane a Daren sha hudu, kuka jerama baza'ama lura dakuba saboda Tun Daga nesa zata dukkan daukan idanu"

Mardeeya tace
"Allah yasa ranace a qarfe sha biyun rana, wannan ai fari ya ceceta, da baqace da kau ba'a magana, cuss kenan"

"Atleast dai farin ya ceceta, wasu kau koda farinma ba kyau sukeba kullum ana cikin yima fuska kwaskwarima" inji Saudart tana Masu gwalo.

"Gayamasu dai anty, farar mace alkyabbar mata, wasu da makudan kudinsuma suke naiman farin, karshe atoye fuska a banza, Daga baya akoma multi colour"

"To kinga kenan kalar mu ce mai tsada, chocolate colour wanda baya saiduwa bare asiya, shi fari ana sayanshi baqifa?"

Haka sukaita cafta tsakaninsu, dayake baby batada baqunta tuni suka dinke yadda kasan dama sunsan juna.

Basu suka kwantaba sai sha biyun dare saboda fira.

Washegari da azahar suka fita dukkansu wankin kai, basuyi wani wahalar rabon iv ba saboda online invitation sukayi Basai anwani sha wahalar zirga zirga ba, anko ma Duk ta online aka turasu da dressing code din walima wanda Arabian gown ne baqa kowa zaisa, a dinner kuma kaya pink and blue za'asa.

A saloon din aka wankema dukansu kai, akayi musu stretching dinshi.

Zo Kaga santi wajen su baby da aka gamama Saudart, don hauka Wai shima gashin daukar shi hoto zatayi ta Dora status.

Dariya su Nafeesa sukaita yima diramarsu don dakyar baby ta hqr bata daukanba.

Nan aka musu manicure da pedicure, qunshi kuma sai saura kwana uku za'ayi.

Basu dawo gidaba sai gab da magrib don Saida suka biya shopping suka jidi Kayan amfani na biki wanda Duk baby ta biya.

Koda suka dawo Sallah kawai sukayi sukaci abinci suka kwanta don Duk a gajiye suke.

Washegari saura kwana biyar biki, ranar kuma za'a kawo lefe, tunda safe su Saudart suka fita kitso banda baby wanda tayi zuciya saboda tace tafison Saudart tabar gashin hakanan ita kuma taqiya shine tace bata rakiyar.

Da qarfe hudu na marece dangin A.A suka kawo lefe na gani na fada.

Set biyu shaqare da tsadaddun kaya da wata mota da aka sako Kayan ciki fara qall qirar Prado.

Sosai akayimusu tarbar mutunci da karamci kuma suka basu tukuici mai tsoka.

Baby kau sana'ar aka hau yi.

Hoto taita daukar Kayan da motar sai iyayi take.

Sai tsokanarta danginsu suke Wai tagudo gidansu Amarya ai datayi hqr har gida zatazo tasameta, ita taita biyemusu suna raha.

Yauma sai can magrib suka dawo sukaga gida haryanzu dinke da yan ganin lefe.

Jikin Saudart ne yayi Sanyi ganin akwatina baje tsakar falon, batace komai ba ta haye sama batareda tayima akwatinan kallo biyu ba.

Su kau mardeeya wuri suka samu suka zauna sunata duba lefen suna santi.

Koda Saudart tashiga daki kuka ya kufce mata ta toshe baki da tafin hannun damanta tana kuka.

Dagudu tafada kan gado tana kukan, Shikenan dagaske auren dai za'ayi mata.

Wayarta taciro takira daddy taita mashi kuka.

Sosai yaita rarrashinta, saida yasha wahala kafin yasamu tayi shiru.

Tananan kwance su baby suka shigo dakin, kamar hadin baki suka fada Mata ajiki.

Nanfa suka shiga tsokanarta baby na kareta, itadai Saudart banza tayi dasu don ba Sune gabanta ba.

Sai Daga baya baby tazame dankwalin Saudart taga kitson.

Nanma rudewa tayi don yau tamafi jiya rudewa.

Shikku akayi mata qananu an tamkesu da qaton ribbon ya sauko har wuya.

Nanma Wai hoton kitson zata dauka, dakyar ta hqr da daukar hoton don Saudart qin yarda tayi, su Nafeesa mezasuyi musu inba dariya ba suna musu ihun sunji Kansu.

Yauma sai kusan dayan dare suka kwanta, yayinda Saudart bata samu barci ba sai wajajen uku sbd yadda Taita juyi tana tunane tunane...✍

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Ramadaan Ramadaan!! Ramadaan!!!

Watar alfarma Ramadaan

Wata mai cike da haske da ni'imomi Ramadaan

Watan da babu kamarsa Duk cikin wattani, Ramadaan.

To ya? Ko kun fara yima babban baqonmu tanaji?

Idan Baku faraba to Ku fara, mu dage mu kwashi gara6asar wannan wata mai albarka.

Mu nemi kusanci ga ubangijinmu mu kasance Masu yawaita istigfari, mu kasance Masu yawaita tilawar Al Qur'an mai girma.
Mu kwashi gara6asar wannan watan sosai don idan damar yin haka ya kufce mana ba lallai bane musake samun wata damarba domin babu mai tabbacin wani shekarar zai zagayo yanada rai.

Allah kabamu ikon yin tsarkakkaken ibada agareka a wannan wata mai alfarma🤲

Allah ka amshi ibadunmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

028

Yau saura kwana hudu biki, yau Saudart na gida bataje koina ba while su Nafeesa da la'asar sunje wajen tailornsu dasukaba dinki.

Zaman nata cikin kadaici yasata samun tunani da hasaso rikittaciya da 6audaddiyar rayuwar auren dazasuyi da wanda zata aura wanda a tarihin rayuwarta bata ta6a jin irin wannan auren yafaru awani wajeba.

Haka ta wuni zurr kwance dama ba tsarki garetaba so bata wani damu kanta wajen tashi ba, Saidai ta mirgina nan ta mirgina can, sam tarasa meke mata dadi.

Yauma da marece liss suka dawo kowa da shopping bag dinshi don shopping suka wuce Daga wajen dinki, itama Saudart sunmata nata sayayyar.

Nanfa aka dasa fira, uwar kaudi kau har gwada Masu irin rawar dazatayi take, kuma ba laifi ta iya rawa don sosai rawar tayimata kyau.

Nan ta zauna tana basu labarin qawayenta musanmman bestie dinta teema har tana cemasu karsu damu ai gobe zasu hadu a walima.

Haka sukaita hirarsu itadai Saudart na kwance tana jinsu idanu a lumshe, don abinda ya dameta ya daketa bata tasu takeba.

Washegari Tun goma nasafe mai qunshi wata yar Indonesia tazo gidan da ita da yaran aikinta biyu.

Nanfa suka kama aiki.

Ogan ita kema Amarya, yaran aikin kuma nama su yanmatan amaren.

Sai wajajen azahar aka gama.

Zokuga qunshi, ba irin jagwalgwalonmu ba🤣

Combination akayima Saudart jaa da baqi akayi mata wasu irin design kamar ba hannu yazanasuba.

Sosai qunshi ya hau da farar fatarta, suma su baby ba laifi nasu ma yayi kyau Saidai fa kunsan komai na Amarya yafi kyau.

Nanfa gida yafara dinkewa da jama'a yan walima dukda qarfe hudu za'a fara.

Su teema sai wajajen uku suka qaraso su biyar yan gayu yan kwalisa.

Nan suka hade aka fara 6arin iyayi, sai a sannan su Nafeesa suka gano dalilin kaud'in ta saboda Duk kusan haka qawayenta suke.

Nanfa daki ya hargitse da hayaniya kowa qoqari yake yafadi cikinshi, babu abinda ke tashi dakin sai shewa da surutu.

Da dai Saudart taga abin nasu azimun ne saita sulale tabar musu dakin takoma bedroom din mamy.

Wajajen qarfe 3:30pm saigasu maryam da Duk ma'aikatan bakery dinta mata.

Tafe suke da manya manyan robobi shake da snacks kama Daga cup cake, meat pie, doughnut, sausage roll, samosa, pizza, da dai sauransu.

Sosai Saudart tayi mammaki ganinsu da wadannan Kayan don kwata kwata batama Masu magana kwatankwacin hakaba.

Nan akayimusu maraba suma Duk sanye suke da baqar after dress wasu kuma Nada kwalliyar wasu kalolin.

Sosai Saudart tanuna jindadinta akan karamcin dasukayi mata wanda hakan ba qaramin dadi yayimusu ba.

4:00pm dai dai shaharrariyar malamar nan wato mallama wasila ta iso, izuwa lokacin harabar gidan dinke yake da mutane kowa cikin Arabian gown black.

Dayake harabar Nada girma sosai anan aka jera kujeru kowa ya zazzauna suna facing din inda mallamar ke zaune, itakau Saudart an tanadar mata mazaunin ta Daga gefen dama.

Saida komai ya lafa sannan aka fito da Amarya.

Wohoho nanfa kallo yakoma sama😳

Sanye take da atamfa Riga da skirt pieces Masu kalar jaa da fari saita Dora qatuwar alkyabba irinta ya'yan sarakuna fara qall mai aikin golden da zaiba , ta sanya hular alkyabbar wanda tarufe Rabin fuskarta.

Sosai akaita santinta saboda ta hadu iya hadewa, su baby Sune Masu tattare mata wutsiyar asoya dake Jan qasa harta samu ta qarasa wajenta ta zauna.

Nanfa akafara abinda ya tarasu, zikiri aka farayi mai ratsa zukata sannan aka dasa kirari mai sa jazaba don daidaikune wadanda basuyi hawaye ba Daga qarshe ta rufe musu da wa'azi mai ratsa jiki musanmman ga Amarya, tana gwada Mata nauye nauyen daya rataya akanta amatsayinta ba matar aure tana mata misali da Nana fadima da matan annabinmu Muhammad (s.a.w)

Sosai jikin Saudart yayi liqis, Kanta a duqe babu abinda take sai hawaye, don sosai wa'azin matar ya ratsa ga6o66in jikinta.

Sai wajajen shidda aka gama, nan aka shiga raba ledoji Masu dauke da sallaya ko doguwar hijabi da cazbaha hadeda snacks da akayi wrapping cikin irin wannan abun mai kyalkyali.

Anan na hango su tawagar yan AUREN KWANGILA NOVEL GROUP sun Kasa zaune sun Kasa tsaye kowacce burinta tasamu rabonta.
Chapter 19 · 0% Book details