← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 111

Sashe 3

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Shine mukayi shawara why not muyi haka, muyi trade by barter, mubaka kudin kaikuma kabamu wani abun dazamu riqe harsaika maido kudin sannan mubaka" yafada cikin nutsuwa.

"Me kenan?" Alhaji ya tambaya cikin rashin fahimta.

Kallon Ashraf sadeeq yayi Wanda haryanzu yana jujjuyawane akan kujera sannan ya maido dubanshi ga Alhajin.

"Diyarka" ya bashi amsa ataqaice.

"Diyata?" Ya tambaya cikin rashin fahimta.

"Eh ina nufin kabamu diyarka saimu Baka kudin.."

"Wait, nufinku inbaku diyata sbd kudi? Ko nufinku son kudi zaisa in lallata rayuwar 'yata? This is unbelievable!" Alhaji ya katseshi cikin tsananin mammaki.

"Calm down Alhaji, ba nufina kenanba, you misunderstand us, abinda nake nufi shine zakaba Sir Ashraf auren diyarka bisa yarjejeniyar daka biyashi kudin shi zai sakoma ita, babu abinda zai shiga tsakaninsu, kawai sunan an daura aurene, zai Baka bashin har zuwa 50million idan kana so, all you'll do is sign a contract with him, Amma fa bawai tilas bane, Mr shamsu remember kanada option, this is just...Business" yaqarashe zancen yana mai stressing din business din.

Shiru Alhaji yayi don kanshi yayi mugun kullewa, contract? Aure? AUREN KWANGILA fa kenan? To meye ribarsu? Shikuma meye ribarshi? Tambayoyin daketa mashi kara kaina akai kenan.

"Alhaji kayi shiru" inji sadeeq dake kallonshi.

Dagowa yayi yana kallon Ashraf, yes he's handsome, damn hot! Irin namijin da kowacce mace zataso samu a matsayin miji, ga kuma uwa uba kudi, he's damn rich, zaici riba idan Ashraf yazama sirikinshi koda na kwana dayane, gaggarumin riba kuwa, Amma shi Ashraf din meye ribarshi idan yayi hakan? Dolene yanada manufarshi nayin haka, meye manufarshi to?

"I'll take your silence as NO" Inji sadeeq.

"No, bawai nayi rejecting bane, Saidai shi meye ribarshi idan yayi hakan? Nasan akwai wata manufa akai" inji Alhaji shamsu.

"Good. Kayi tunani mai kyau, dolene yanada manufa, eh yanada ita, as you can see, Ashraf matashine mai ji da kudi da kyau, he's clocking 28 yrs wata mai zuwa, iyayenshi sun tasoshi gaba da mgnr aure har suka bashi wasu adadi lokuta na idan be kawo mataba zasu hanashi da wadda sukeso, shikuma wacce yakeso na schooling ne, sai nanda shekaru 2 zata gama, so shine daya bincika yaga kanada 'ya yaga why not ya aureta, AUREN KWANGILA, Inyaso daka biyashi saiya saketa at that time kuma yarinyar dayakeso is over sai kawai ya aureta, this is just a CONTRACT MARRIAGE, kamar yadda nafadama babu abinda zai shiga tsakaninsu, yadda ka kawota haka zaka amsheta"

Shiru Alhaji shamsu yayi yana sauraronshi, yana kuma hada kalmominshi yana rarrabawa, abunka da businessman harya fara hango hanyoyin samun ribarshi na sosai ma, yes akwai riba, huge riba, babba ma kuwa.

"Kai muke sauraro, ka amincene? Koko musami wani?" Inji sadeeq.

Qara kallon Ashraf yayi Wanda a wannan karon shima shi yake kallo yana jiran amsarshi, nima nayi kasaqe da Biro a hannu ina jiran amsarshi.

Bakajin komai a office din sai qarar A.C

Sauke ajiyar zuciya yayi sannan ahankali ya bude baki yace......✍

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan cuta (covid19)🤲
Allah ka ji6anci lamuranmu karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

006

Sauke ajiyar zuciya yayi sannan ahankali ya bude baki yace
"Idan nace kubani lokaci inyi tunani fa?"

Wannan karon Ashraf yayi magana cikin husky cool voice dinshi
"You can have your time to think, is not as if tilastama akeyi, wannan deal ne kawai Wanda bazai yiwuba sai duka 6angarorin sun amince kuma sunyi sign, ni, kai sai daughtern ka, kanada ikon janyewa it's your right, Saidai remember millions of people are outside waiting for opportunity irin wannan, idan beyimaba karka ji kunyar fada. Am good with any of your answer" ya qarashe zancen yana qara balancing a kujerarshi.

Ajiyar zuciya Alhaji yayi.
'Thank God. At least fargabana na aurama diyata kurma ya kau' yafada cikin zuciyarshi.

"Babu matsala insha Allah, kawai dai kubani time inyi tunani"

"Zuwa yaushe?" Inji sadeeq

"Nan da Monday insha Allah"

"To Allah yakaimu"

"Amin thanks, I'll get going"

"Alright mungode sir"

"You're welcome" yafada yana miqewa tsaye tareda miqama sadeeq hannu sukayi musabaha sannan ya d'an sack kallon Ashraf sannan yafice.

Kallon juna Ashraf da Sadeeq sukayi Bayan sun rakashi da idanu.

"Did you think the jerk will accept?" Inji Ashraf cikin yamutsa fuska.

"Ina jiyo qamshin nasara dai, he won't afford to loose this opportunity, besides wazai the whole SIR ASHRAF?"

Murmushin gefen baki yayi yana sake balancing a kujerar.

"It better be" yafada yana shafa sajenshi ahankali murmushin still a fuskarshi.

****************************************

Tuqi yake Amma kwata kwata hankalinshi na wani wajen.

AUREN KWANGILA? Contract marriage? Da familyn A.A? diyata tazama daya Daga cikin familyn A.A?
Wow! What an incredible opportunity! Ni? In-law din A.A family?

As for me banda problem but Saudart...

Shiru yayi yana tuna aqidar Saudart na tsanar mutuwar aure, koyaya taji aure yamutu saita shiga damuwa da 6acin rai, musanmman idan antara iyalai.

Tashin datayi cikin broken family yasa ta tsani mutuwar aure, lokaci da dama takan gayamishi ra'ayinta na son yin auren MUTU-KA-RABA, Akoda yaushe maganarta baya wuce
"Dad katayani da addu'a Allah yabani miji na gari, ko bashi da kyau bashida arziqi ya kasance mai kyan hali, Wanda zamu Gina ingantacciyar zuri'a nan gaba, Wanda zamu hadu muba 'ya'yanmu tarbiyya, Wanda mutuwace kawai zata rabamu"

Wani sa'in ya kan tsokaneta da marar kunya tana fadamashi irin wannan mgnan a matsayinshi na mahaifinta.
Takan yi dariya lokuta da Dama tana rufe fuska sannan tace "Dad, ai gaskiyane, Aure wajibine ga dukkan musulmi Duk cikarka bazaka ta6a zama cikkake mai darajaba saikayi aure, name zanji kunya Bayan nasan koba dade koba jima saina yi auren?

Hakan daya tuno ba qaramin tada mashi hankali yayiba.

Me zaice mata? Zan hadaki AUREN KWANGILA da A.A sbd farfadowar company na? Impossible!
Bazai iya kiyasta tashin hankalin fasata shigaba idan taji hakan, aure? Na Wanda bata saniba kuma bata ta6a ganiba? Kuma qarin gishiri a ciwo Aure na taqaittacen lokaci? Kai da kamar wuya.

Haka yaita tunane tunanenshi harya iso gida jikinshi yayi matuqar la'asar.
Shidai abinda yasani no matter what, bazai bar wannan damar ta wuceshiba.

WAIWAYE (Adon tafiya🕴)

Manage please🙏

Ummin fasihu ce

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan cuta (covid19)🤲

Ya Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

007

WAIWAYE (Adon tafiya🕴)

Alhaji shamsu d'ane tilo ga Mallam yahya.

Su yan asalin garin kanjiyane dake jahar katsina.

Tun yana Dan shekara shida mahaifinshi yakaishi cikin birnin katsina almajiranci.
A makaranta wani babban malami wato mallam Ballo.

Haka suke rayuwa a wannan makarantar Wanda yawanci abincin dazasuci sai sunje bara suke samu, wani sa'in idan basu samuba haka suke haqura su kwanta kasancewar iyayensu basu wani had'osu da abincin kirkiba, gashi shima malamin ta kanshi yake don bazai iya daukar nauyinsuba kasancewar shima bamai wani hali bane ga d'aliban dayawa.

Haka rayuwa ta kasance basa komawa qauyensu saiga damina don taimakawa iyayen da noma, da kaka tayi sai asake turosu da guzurin dabe taka kara ya karyaba.

Rayuwa suke irin na sakakku wadanda babu mai tsawata Masu sai malaminsu shima a lokacin karatu, wani sa'in karatun ma ba dauka sukeyiba saboda ai sai ciki ya dauka sannan za'a maganar karatu, wani sa'in saisun yi aikatau sannan zasu sami abinci.

Haka rayuwarsu ta kasance wani sa'in tufafin dazasu sa sai sunyi bara suke samu shima dakyar, wasu kau Kayan jikinsu sbd tsabar datti ko zanen Kayan ba'a gani, wasu kuma kaya sun 6e66ere Masu ajiki Amma babu halin dinkawa.

Acikin wannan rayuwar wasu suke kauce hanya su fada munanan hali batareda an ankaraba tunda babu Masu sanyamusu ido, sai aga ba'a samo karatunba kuma 'ya'ya sun kangare sun gaggari al'umma.

Shamsu shi Allah ya tsareshi da fadawa irin wadanan halin Saidai yataso da kwadayin abin duniya, kudi ko ta hanyar haram ne yanabi yasamesu, gashi da tarin karatu Saidai be amfaneshiba.

Duk buga bugan dazaiyi yasamu kudi saiyayi don a tunaninshi kudi shine komai, idan kanada kudi to kowama kana iya takawa.

Tun yana komawa kauyensu Duk damina don taya babbanshi noma har ya daina.

Alokacin dakowa ke komawa kauye sai shi yashige cikin gari yana buga buganshi na Neman kudi, wani sa'in ya kwana a tasha wani sa'in a massalaci.

Babu yadda babanshi beyi dashiba don ya dinga leqosu koda sau dayane a shekara Amma firr yaqi, don aganinshi baya iya zaman kauye kuma, yasaba da riqe kudi da cin Abu mai maski mezeje yi kauye?

Abun ba qaramin damun mallam Yahya yayiba gashi shine d'a talin qwal nashi.

Haka ya haqura yazuba mashi idanu don yariga ya kangare bawai maganar kowa yakejiba.

Shamsu likafa taji gaba, Tun yana buga buganshi a katsina harya koma kano jin can anfi kasuwanci kuma anfi samun kudi.

Wani babban shago yasamu aiki na yaron shago inda ake siyarda Cosmetics Kala kala.

Sosai yake samun kudi don shagon shahararene kuma mai shagon na sallama mai tsoka.

Dayake Shamsu Allah yayimashi farin jinin mutane, cikin d'an qanqanin lokaci yasan kwastamomi dayawa, kusan kowa yasanshi saboda barkwancishi da iya mu'amala.

Ahankali ahankali yafara yiwa ubangidan nashi cuwa, yana mashi rinto, wani sa'in idan aka aikashi saro kaya saiya Dora nashi Asama kokuma wurin Saidawa ya qara akai.

Dayake uban gidan nashi ya yarda dashi kuma becika sa ido sosaiba, beyi saurin ganewaba, saida yayi mashi mummunar 6anna, sbd Duk kusan customers dinshi sunbar zuwa sbd yadda kayanshi suke tsada.

Ataqaice dai shago yarushe babu riba kullum sai faduwa, Daga qarshe Saidai ya sallami yaran shagon gabadaya yarufe shagon sbd rashin jari.

Shamsu daketa Tara kudaden dayake samu wajen rintonshi, yasamu wani qaramin shago cikin kasuwar yabude shima yazuba irin Kayan da oganshi ke Saidawa ada.

Ahankali ahankali, kasuwancinshi yadinga ha66aka, Allah yasa mashi albarka a kasuwancinshi.

Abu qarami yakoma babba Tun yana sari garuruwa harya fara fita qasashen waje.

Cikin shekara biyar ya bude wani qaton company mai suna A.S GALLERY

Duk abinda akeso na Kayan alatu yana Saidawa. Company nashi yazama shaharare Wanda ake tutiya dashi garin kano.

Wata shekara yadai runtse ido yayi aikin hajji shima sbd matsa mishi da abokan kasuwancinshi kemashi na yaqi aikin hajji.
Chapter 3 · 0% Book details