← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 108 OF 111

Sashe 108

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

(Tofah🤔 dama abinda yake nufi kenan da kawo diyar motane office, nidai ina ganin rayuwa ni shatu🤦‍♀️ aradu nakusan barin bibbiyar mutanen nan don naga dagaske dai disvirgining din idanuna zasuyi, ina dalili?😠)

Har nayi zuciya zan tattara takarduna akayi knocking din kofa

Jarabbabun basuji ba sai ana uku sannan sukayi saurin releasing juna ta zira hijabinta ta koma wajenta da sauri ta zauna sai a sannan yabada umarnin shigowa

Sadeeq ne yashigo da niyyar balbaleshi da bala'i sai ganin saudart yasashi Fasawa yashiga gaidata

Ita kunya ma taji, gashi jitake kamar ya dago abinda suke hakan yasa ta amsa akunyace sannan ta tashi ta kwashi wasu files da batamasan na menene ba tawuce tafita

Saida tafita sannan sadeeq ya zauna yana mashi shaqiyanci wai to karfa zuwan saudart yasashi shiririta zagewa zaiyi ya kwashi aiki don yasan halinshi

Shidai ashraf be tanka mashi ba, saida ya tabbatar ya quleshi sosai da shaqiyancinshi sannan yabaro office din yana dariya

Ba'a jimaba shima yafita yawuce office din saudart inda duk nan ya shiritar daita shi beyi aiki ba be bari itama tayi na kirkiba

Haka suka tashi lokacin closing batareda sun tsinana wani abin kirkiba inda wannan karon saudart ta maidosu gida

Haka suka cigaba da rayuwar su cikin tsantsar soyayya da girmama juna

Koda wasa basa qaunar 6acin ran juna koda yaushe cikin taka tsantsan suke wajen gujema abinda zai jawo 6acin rai ga dayansu

Kullum suna manne dajuna ba gidanba ba company ba donma saudart wani sa'in botsarewa take idan taga alamun shiriritar na neman yawa, koda yaushe haka zaka gansu cikin farinciki da annushuwa basa qaunar abinda zai nisantasu daidai da minti daya

A cikin sati na biyu dafara zuwansu aiki ashraf ya shirya musu business trip zuwa Dubai wanda acan qasan ranshi ba business kawai zai kaisu canba harda honeymoon

Cikin dan qanqanin lokaci suka gama shirye shiryensu na tafiya sannan sukabi gidajen iyayensu sukaje bankwana inda sukuma suka bisu da addu'ar dawowa lfy

Ranar Talata da qarfe 12 na hantsi jirginsu ya daga zuwa shaharariyar qasarnan Wato Dubai...✍️

Manage👏

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️
[12/15, 7:49 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖

107
(Semi final)

*DUBAI*

Sai can da marece liqis jirginsu ya sauka a airport din babbar Birnin tarayyar Dubai

Kai tsaye a wani kataffaren hotel mai suna *AN-NUR INTERNATIONAL HOTEL* suka yada zango

Daki mai ciki da falo da toilet suka kama wanda aka zuba kayan alatu da more rayuwa aciki

Kasancewar agajiye suke, wanka duk suka fara yowa suka sauke sallolin Kansu sannan sukaci abincin dasukayi ordering

Bayan sunci abincin ashraf ya fita itakuma tadan gyagyara wajen tareda shirya kayansu a closet

Tun kafin tagama aka fara kiraye kirayen sallar magrib hakan yasa tana gamawa ta dauro alwalla tayita ta zauna lazimi kafin ayi isha'i ta tashi ta yita itama.

Tana gamawa ta tashi ta linke sallayar ta maida a closet din sannan ta tu6e ta daura towel tashige wanka

Koda ta fito sama sama tayi shafa saboda gajiyar dake nukurkusarta ga barci dake idanuwanta, tasamu ta chanza zuwa kayan barci ta lalla6a ta kwanta

Batasan dawowarshi ba saidai ta tashi cikin dare tajita ajikinshi ya qanqameta

Jin hakan yasata qara shigewa jikinshi wani dadadden barcin na sake daukarta

Kwana biyu sukayi suna abinda yakaisu dangane da aikinsu suka kamalla suka tura reports wa sadeeq ta e-mail sannan suka shiga honeymoon dinsu gadan gadan

Kwanaki biyar suka qara a Dubai suna yawon shaqatawa da bude ido agefe guda kuma suna gwangwaje amarcinsu

Duk wani wuri na shaqatawa da bude ido dake Dubai saida sukajeshi ciki harda tourist centres da zoos ddss

Satinsu daya a Dubai suka sake cirawa basu dira a koinaba sai Philippines

Ananma saida sukayi sati suna kwasar amarcinsu a wani dan qaramin island(gida a tsakiyar ruwa) dasuka sauka wanda dan wurine zagaye da ruwa, a wurin akwai ginin dan qaramin bukka wanda ita kanta abin kalloce don dukda bukkace ba qaramin tsaruwa tayiba

Zagaye suke da ruwa don ko fita zasuyi cikin gari saidai su hau kwale kwale akai su hakama idan zasu dawo

Sosai saudart taji dadin rayuwar wajen it's so quiet and has a romantic atmosphere

Tsakaninsu da wata bukkar akwai dan tazara don haka island din yake bukkokine jefi jefi hakan yasa wajen yacika shiru dayawa, da marece haka zasu fito su zauna bakin ruwan suna shan sanyayyar iskar wajen suna fira wani lokacin kuma suhau kwale kwale ayawata dasu cikin ruwan

Satinsu daya aqasar suka cira kuma, basu dira koina ba sai SPAIN

Fadin murnar da saudart tayi 6ata bakine don ko a jirgi ma sai mutsu mutsu take jitake kamar tayi tsuntsuwa taganta can

Bata ta6a tunanin zata sake zuwa wannan qasar ba, tayi missing din mutanen qasar especially Reyna da Loveth

Gwara gwara Loveth suna waya suna kuma chatting via media amma Reyna kwata kwata bata samunta

A estate din dasuka sauka wancan karon sukayi dasauki wannan karon ma saidai ba wancan gidan bane, wani ne kuma daban kasancewar dama gidajen na haya ga ire irensu matafiya dabasu son sauka hotel dama tsirarun yan qasar dasuke sha'awar zama wajen

Murnar saudart takoma ciki bayan ta iske duk yawancin qawayenta na wancan zuwan duk basunan ciki harda Reyna data koma qasar haihuwarta Wato Italy

Saidai tayi murna sosai da iske Loveth nan aka zauna anata firan yaushe gamo, anan ne Loveth ke bata sabuwar number Reyna suka kirata video call

Hauka ne kadai Reyna batayi ba don murnar sake ganin saudart tana cizon yatsan takaicin rashin haduwarsu

Ananma saida sukayi sati daya inda a ranar daren da zasu daga wato juma'a ranar Good Friday dasuka saba haduwa awajen don zumunci da sanin juna ashraf ya hadu da gayen da yaso shiga gonarshi wancan karon😆

Sunyi mammakin ganin juna don basu ta6a tunanin zasu sake hadewa ba

Gaisawa sukayi cikin mutuncin kamar ba abinda ya ta6a hadasu, suka zauna kusada juna suka shiga cafta irin tasu ta maxa dukda ashraf be cika tofawa ba

Saudart kau a 6angarensu wannan karon ma nan da nan tayi qawaye, can zaka hangota tsamo2 cikin mutane ana maida yadda

Washegari suka cira daga qasar suka shilla Saudia don yin umra

Sosai saudart tashiga shauqi ganinta gata ga dakin Allah

Ibada sukeyi ba dare ba rana suna addu'o'i da neman kusanci awurin Allah.

Bata ida shiga shauqi ba saida sukaje madina, gata ga qabarin Annabi Muhammad (S.A.W)

Ranar taci kuka kamar ba gobe tana yima fiyayyen hallita kirari (muma Allah ya gwadamana irin wannan rana, amin🤲🏻)

Satinsu biyu anan sannan suka fara shirye shiryen komawa gida Nigeria

*NIGERIA*

Anan kau tun bayan tafiyar su ashraf da yan kwanaki sadeeq yayima ummanshi magana akan wadda yakeso.

Sosai umma taji dadin wannan hadin don haka batareda 6ata lokaci ba ta sanarda danginta Dana margayi babanshi (baban sadeeq yarasu tun sadeeq na shekaru 5 sanaddiyar hatsarin mota)

Suma sosai dangin sukayi murna don dama sadeeq ya Isa aure masha Allah kuma sun jima suna Mashi magana akan haka

Cikin qanqanin lokaci aka tura kudin mungani munaso inda aka tsayar za'a tsaida ranar aurenne idan babban yayan yarinyar yadawo daga tafiya.

*SAUDI ARABIA*

Tun saura kwana biyu sudawo Nigeria suka fara shopping din kayan tsaraba

Kaya suka jida sosai kamar basujin zafin kudinba kowanne zuciyarshi cikeda dokin komawa gida

*NIGERIA*

Qarfe 5:00pm sukayi landing a filin jirgin sama na Aminu kano

Baby da sadeeq dasuka zo tarbansu suka shiga baza ido don ganin ta ina zasu 6ullo

Acikin mutanen masu Saukowa suka hangosu suma hannunsu sarqahe ana juna

Baby tafara hangosu hakan yasata qara gwala idanu don tabbatar da eh su dinne

"Ya sadeeq kalla" tafada tana nuna satinsu da yatsa hakan yasa shima yabi inda ta nuna din da kallo

Shima hangame baki yayi cikeda mammaki don shima a kallon farko be ganesuba

Sun chanza sosai sun wani yi fresh especially saudart ga kumatun da kowanne ya ajiye ku6ul2😆

Sunyi kyau sosai cikin shigar ankon dasukayi black and white sun taho hannunsu sarqahe dana juna gwanin sha'awa

Baby jitake kamar ta ruga taje ta taryosu saidai tanajin nauyin yin hakan gaban sadeeq hakan yasata tsayawa tana kallonsu fuska awashe

Sai daga su saudart ma suka hangosu nan take dadi yakama saudart tasaki hannun ashraf tayi saurin qarasawa ga baby daketa washe baki suka rungume juna baby harda dan ihun murna tana cewa
"Sweet auntyyy"

Shikau ashraf yana qarasowa suka gallama juna harara shida sadeeq kamar irin basuji dadin ganin junaba amma karka bincika zuciyarsu don cike take da murnar sake ganin juna bayan fin wata basusa juna a ido ba

"Hmm sai yanzu kuka gama business trip din?" Inji sadeeq yana watsa mashi harara

Yatsina fuska ashraf yayi yace
"Shafa kaji"

Tsaki sadeeq yaja yace
"Kaji dashi, zonan ba don halinka ba" yafada yana jawoshi ya rungumeshi

Shima ashraf hugging dinshi yayi yana murmushin daya bayyana haqoranshi don ba qarya yayi missing dinshi sosai

A bangaren su baby kau sakin saudart tayi daga rungume juna dasukayi tadan ja baya tana kallonta tace
"Ehhh? Wai aunty kin ganki kuwa? Wannan murjewa haka? Meye sirrin"

Yitayi kamar zata bata rankwashi hakan yasata saurin noqewa tace
"Sirro, ni ina ummy na?"

"Hajiya ummy ana gida, cewa nayi nice first din ganinku tunfa 4 something Muke nan muna jiranku, ammafa wlh hajiyata kin wanku, halan dakukaje chan cikin injin din wanke fata aka saki? Wannan murjewa haka?"

Itadai saudart bata sake bi takanta ba don idan da sabo tasaba da halin baby

Juyawa tayi suna gaisawa da sadeeq dake mata shaqiyancin wai daga business trip shikenan sai baba tagani?

Itadai dariya kawai tayi daidai lokacin kuma baby ke gaida ashraf tana mashi ya hanya amsawa yayi sannan suka dunguma suka shiga motar, su baby na baya su ashraf na gaba inda sadeeq ne mai tuqi suka fice daga airport din.

A qofar gidansu suka ajiyesu babu yadda basuyi dasuba akan su shiga amma suka qiya suka juya suka bar wajen

Haka su saudart suka shiga gida cikeda gajiya hade da farincikin dawowa qasarsu lfy.

Sai washegarin ranar suka bude tsaraba kowa aka ware mashi tashi sannan suka gama hanyar gidajen iyayensu

Gidan Mamy suka fara zuwa, sosai Mamy tayi farincikin ganinsu ta tarbesu cikin jindadi tana nan nan dasu
Chapter 108 · 0% Book details