← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 111

Sashe 109

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su habeeb basusan hakan ma Abba hakan yasa gidan yayi shiru

Tun a kallon farko da Mamy tayiwa saudart tagane ba ita kadai bace, duk yadda akayi akwai abinda ke lafe a mararta

Hakan yasata farinciki sosai nan taita jide masu kayan ciye2 kala2

Ashraf beji ba dayawa sai saudart data barraraje ta kwashi girkin don dama kwanakin nan haka take, ashraf har mammaki take bashi saboda cinta, kome tasamu ciki

Sun dan jima anan sannan suka wuce gidan ummy

Ananma tarba suka samu sosai daga uummy, su baby ba'a nan

Itama ummy a kallon farko asirin saudart ya tonu, itama tayi murna sosai don tamafi Mamy murna da hakan

Anan itama suka jidemasu nasu tsarabar ummy nata murna dasa albarka

Sai anan take gayamasu kawo kudin neman auren baby da akayi

Sosai saudart taji mammakin wanda akace ya turo while shi ashraf beji irin mammakin nan ba don dama yasan za'a rina

Sosai suka nuna farincikin su akan hakan balle saudart dataga dacewar hadin

Anan suka qarasa wunin ranar inda saudart tasamu baby bayan tadawo ta tisata gaba da tsokana itakau sai rufe fuska take tana Dariya

***

Saida wata Monday din ta zagayo sannan suka koma aiki

Saidai wannan karon shiriritar tafi yawa ta 6angaren saudart

Batada aiki sai ciye ciye, Kwata Kwata batajin dadin bakinta ya zauna hakanan don kasa hade miyau take shiyasa koda yaushe cikin ciye2 take

Haka zatazo ta zauna a office din ashraf ta tusa kayan ciye2 agaba wanda duk yawanci malaqi ne, taita jidama ciki babu ko gajiya

Ashraf tun abin na bashi mammaki harya fara damunshi don ko hanata yayi saita tusashi gaba da kuka

Ya lura ba ciwon ciye2 kadai ke damunta ba harda na kuka don yanzu tazama wata ruwa ruwa, qiris take jira ta 6arema baki

Yauma zaune yake a office dinshi yana typing a system dinshi yanason qarasa wani aiki da ake buqatarshi cikin gaggawa

Dagowa yayi a karo na ba adadi ya kalli saudart dake zaune kan wata sofa dake gefen office din ta tankwashe kaffafu bowl din soyayyar gyada mai 6awo a gabanta sai wani bowl din a gefe tana zuba 6awon aciki

Cin gyadar ta takeyi tana lumlumshe idanu kamar mai cin soye

Tunawa yayi da darun dasuka sha kafin asiya gyadar

Daga ganin mai tallar gyada a hanyarsu ta tahowa ta tibure dole saiya tsaya ta saya

Daya qiya tasamashi kuka wurjanjan kamar wacce akayi was dukan tsiya, babu arziqi yajuya ya saimata nan ne fa yasamu lfy

Girgiza kanshi yayi ya maida kanshi a system din gabanshi yana ayyana dolene ma suje asibiti yau idan sun tashi don abin yafara yawa kar ace wata cutace basu Sani ba sai ta girmama tafi qarfin magani sannan

Da wannan tunanin yacigaba da aikinshi wanda ita yakamata ta kama mashi amma yasan idan ya matsa mata shi zai kwashi kayan haushi don kamar asiri datahau system da niyyar aiki saita bingire da barci, kai dolene ma yau ayita ta qare, dole yakaita aduba lfyarta don shi abin yafara bashi tsoro

(Wayaga first enter🤣🤭)

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚

*FINAL🤸🏻‍♀️*

Koda suka tashi daga aikin asibiti yawuce daita straight

Yanajin tanata mitar ita lfyarta qalau yayi banza daita don shi yasan ba lafiya ba

Koda suka Isa asibitin haka suka fito suka nufi ciki saudart bakinnan a ture ita Allah Dole fushi take wai ya kawota hospital on no purpose

Shidai be kulata ba saima kama hannunta dayayi suka shiga cikin qayattaciyar asibitin

Cikin qanqanin lokaci sukaga likita kasancewar sunada family doctor a asibitin

Saida ashraf yagama koramashi bayanin abinda ke damunta fuskarshi dauke da damuwa sannan yace dan Allah a gwadata kar ace wani ciwon ne

Shidai doctor murmushi yayi sannan yakira nurse ya umarceta da diban jinin saudart

Dakyar tabari aka diba don saudart daman mugun tsoron allura take

Saida aka diba sannan doctorn yafita zuwa lab dakanshi don aunawa yabar ashraf da aikin rarrashinta don hawaye take sosai dama tusa hali bare anci wake

Saida doctor yakwashe fin 30mins sannan yadawo fuskarshi washe

Congratulating dinsu yafarayi sannan ya miqa mashi result din yana fada musu abinda ke ciki

Mutuwar zaune duk sukayi suna kwalalo idanu waje sannan suka kalli juna

Saurin fizge takarda tayi daga hannunshi ta duba tana qara wara manyan idanunta

Ciki? Ciki fa? Kuma na haihuwa, how come bata ta6a kawoma ranta hakaba? Dama haka ake samun cikin a 6agas ba ciwo ba wahalar komai? Ita harga Allah bata ta6a kawo hakan a ranta ba don tasan yawanci masu ciki suna shan wahala sosai a farkon samun cikin fa yawan amaye amaye, itakau ki ciwon kai bata ta6a ba gashi period dinta dama duk wata biyu takeyi shiyasa bata damu da rashin ganinshi ba wancan watan ba don it's something normal to her

Zokaga murna wajensu musanmman Ashraf, bakinan ko sayuwa beyi, sujjadar shukur yayi cikin farinciki sannan ya kama hannun doctor cikin yin musabaha yana kwarara mashi godiya sannan yakoma wajen saudart da itama takasa 6oye murnarta yayi hugging dinta batareda yasani ba yashiga kwararamata godiya kamar maroqin da aka biyama hajji

Itadai saudart kunya ma ta rufeta ganin yadda yake irin wannan 6arin jikin agaban doctor sai dariya doctor kemasu

Saida doctor ya gindaya mashi abubbuwan daya kamata ta baryi har cikin yayi kwari kamar daukar abu mai nauyi da ayyukan wahala kuma ciye ciyenta da yawan barcinta is normal ya kyaleta kuma yadinga siyanmata abubbuwan data nuna tanaso except kayan sanyi da zaqi sannan ya sallamesu

Ranar saudart taga rawar jiki takuma qara tabbatarda namiji kunya be isheshi ba don a daren babu wanda be kiraba ya gayamawa, wai harda surukanshi da rashin ta ido

To su dama su ummy da mamy sun sani sunede da basuda man kai suka kasa gano hakan, sosai sukayi murna akan hakan most especially Daddy, ranar saida ya shige daki yaci kukanshi na farincikin diyarshi daya tilo zata samar mashi jika kuma tsatson babban amininshi margayi Auwal

Tofa daga ranar ashraf yakoma bayada aiki sai kulada saudart da unborn dinshi

Duk motsinta akan idonshi saiya tambayeta meke damunta, ko me take buqata

Saida yayi kwana uku agida yana kula daita sannan ya koma aiki shima koda yaushe suna maqale a waya da kuma zuhr tayi zai dawo gida ya duba lfyar matarshi sai bayan asr zai koma

Saudart likafa taci gaba, yanzu dai babu zuwa aiki babu aikin komai saina ci, koda yaushe ka ganta to bakinta yana motsi don irin cikin nanne mai tara yawu, sosai takeba ashraf tausayi musanmman idan yaga tana barcin nan nata na fama, wani irin sonta yakeji a zuciyarshi da tausayinta yana addu'ar Allah ya rabata da abinda ke cikinta lfy

A bangaren maganarsu sadeeq kau tuni akasa rana, nan da wata hudu Wato bayan graduation dinsu baby

Zokaga murna wajen sadeeq, nanfa yafara yima ashraf wani gani gani wai shima yakusan zama angon yaga ta gori

Shidai ashraf dariya yakemashi yace Ai kuma na gaba yayi gaba kuma dole akira mijin iya baba, wai yabishi ahankali don shi surukinshi ne idan yakawo mashi raini saiyayi mashi buqulu yaga ta tsiya, Dariya sadeeq keyimashi yace wannan labari ne

Haka akaita rarrafawa inda saudart da ashraf suka cigaba da rainon cikin dasuke ma so marar misaltuwa while su baby da sadeeq ana gefe ana shirye shiryen biki wanda saudart tayima laqabi da *Auren zafafa biyu* don a tsakanin sadeeq da baby ba'a San gwani ba don hallayarsu daya daga zafin dumin har rawar kan, tasan dai gidansu dandalin drama zai zama don zani ce ta tarda muje

***
Biki fa ta matso inda ake shirye shirye tako wanne bangare

Kallo daya zakayiwa shirye shiryen bikin ka tabbatar da na yana gaban goshi ne bana bayan qeya ba

Ashraf shi ya dauke nauyin komai da za'ayiwa baby both kayan daki da kitchen

Sosai ya narka kudinshi wajen hidimar tilon qanwarshi da duk duniya baida kamarta

Saudart itace jagaba amara qahon qirjin biki don duk da ita ake zuwa siyayyar kayan kitchen, agefe kuma tana koyawa baby nau'ikan girke girke iri2 don shiririta yasa bata wani iya girkin kirki ba

Ummy kuma anata 6angaren zagewa tayi ta gyara diyarta kuma autarta ciki da bai, abin dai chakwai👌

Basu wani tsara bidi'o'i ba a bikin sai kauyawa party da za'ayi ranar Daren biki sai walima ranar biki

Abin yaba kowa mammaki don babu wanda beyi tunanin za'asha shagulgulaba a bikin dubada yadda yanayin amaryar mai jiran gado da angon suke

Qawayen baby dasuka shirya ma bikin sosai suna dokin shi suka shiga mita wai ta za'ayi bikin *mhiz meebie* guda ace event daya za'ayi wai kuma qauyawa?

Bude kwandon shara baby tayi tasakasu aciki ta rufe acewarta batada lokacin su

Biki ba saura 1 week su nafeesa da mardeeya (cousins din saudart) suka antayo daga Maiduguri don tun bayan bikin su ashraf suke zumunci sosai da baby

Sosai baby taji dadin zuwansu, babu 6ata lokaci suka tare dakinta aka shiga maida yadda akayi

Lokacin da su nafeesa suka hade da saudart sosai suka shiga yimata dariya don alokacin ta chanza sosai, ciki ya hurata dukda bawani girman ciki gareta ba saidai ta chanza tawani ajiye wasu tayani muni a fuska nanfa suka shiga saida halin dasuka saba na tsokanar juna irin na abokan wasa

Biki na saura kwana uku wasu qawaye uku ba baby suka qara zuwa gidan cikinsu harda teema aminiyarta

Alokacin daka shigo gidan zaka tabbatar da kashigo gidan biki don yafara cika da yan biki kama daga dangin ummy na yola har dangin abbansu ashraf na wudil

Aranar kayan lefen baby suka duro gidan

Masha Allah, ko hasiddin ida hasada yagani saiya yaba don sosai sadeeq yataka rawar gani a kayan

Su saudart sune gaba gaba wajen ganin lefe sai yabawa ake

Saudart anshiga busy, Ku kau bikin autares kuma qanwar miji guda? Duk hidindimun da akeyi agidan da ita akeyi donma ummy na dan hana wani abin saboda condition dinta
Duk kayan snacks da drinks da ake amfani kuma ake kan amfani a bikin daga bakery dinta suke tana gaba akan wannan

Shima ashraf a bangaren shi yashiga busy, gashi babban aminin ango gashi babban yaya ga amarya
Chapter 109 · 0% Book details