← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 111

Sashe 104

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rungumota yayi yana Dariya sosai sannan yashiga mata chakulkuli itama fashewa tayi da Dariya tana zillo tana bashi haquri

Saida ya jigatata sosai sannan ya kyaleta ta fada jikinshi suna sauke Ajiyar zuciya tare

Tana sauke numfashi ahankali tace
"Ammafa kai mugune, wlh cikina harya fara amsawa"

Dariya yayi yace
"Gakinan babbar muguwa, kiri kiri kin hanani aiki Kwata Kwata"

Waro idanu tayi tace
"Yaushe na hanaka?"

"Kin fini Sani ai Yar rainin sense kawai, kin hanani zuwa office nan dinma kin hanani kata6us, wancan anacen tun yana takuramin haryayi fushi ya qyaleni"

Dariya tasake yi kafin tace
"Ni na hanaka zuwa office?"

"Eh mana, inba keba waye? Wlh kiji tsoron Allah" yafada yana 6ata fuska kamar zaiyi kuka

Dariya tasake yi tace
"Kodai kaji tsoron Allah, halan da igiya na daureka nave bazaka fitaba?"

"Ai yamafi igiya, please saudart let's be serious ya kamata kiyi considering zancena, bekamata kinamin hakaba wlh, please jan ajin ya isa hakan"

Dan hade fuska tayi tace
"What are you talking about?"

"Kinfini Sani saudart, wai meyasa tana tado wannan maganar saiki chanza mood dinki?"

"Then kabar tadowa, final" tafada tana juyamashi baya

Kwantowa yayi kan bayanta ya zuro hannayenshi ta cikinta yaqara jawota jikinshi yace
"Saudart meyasa bazaki zama secretary dina ba akaro nabiyu? Ko haryanzu komai be wuceba awajenki?"

Lumshe idanu tayi ta bude kafin tace
"Idan komai be wuceba awajena bazanyi qaryar cewa ya wuceba, ina son kasani wancan karonma da dalilin yin hakan, ni Kwata Kwata banida ra'ayin white collar job ko aiki a qarqashin wani, plus banida burin aiki da aurena, nafison in zauna gida as a house wife inyaso bakery dina ya isheni, I can run my business anan gida"

Shiru taji yayi bece komaiba hakan yasata juyowa

Ganin ya kafeta da ido yasata itama tsayawa kallonshi don a iya zamanta dashi tasan kàso mai yawa koda ba duka bane a hallayenshi

Tasanshi da saurin hawa, yanzu hakan 6acin ran dayake qoqarin 6oyewa take hangowa a idanunshi

Lumshe idanu yayi yana hadiye yawu dakyar sannan yabude ya kalleta yaga still ita yake kallo

"Bakison aiki a qarqashin wani? Nine *wani?*" yafada ahankali yana kallonta da piercing idanunshi

Girgiza mashi kai tayi cikin inda inda tace
"N..no, ba haka nake nufi b.."

Katseta yayi ta hanyar manna mata light kiss a baki ya dan shafa kanta yace
"It ok uhm? Bari nayi wanka"

Bejira cewarta ba yatashi yawuce toilet tabishi da kallo jiki a sanyaye

Tashi itama tayi zaune ta jingina da gadon tana kallon kofar toilet din

Ita harga Allah badon ta 6atamashi raiba tayi wannan maganar

Ita bakin gaskiyarta ta fadamashi, shiyasa tun sadda yafara tadomata wannan maganar taketa zillemashi saboda gudun irin wannan

Ita harga Allah batason aikin office, don babban burinta tazama full house wife wanda zata kula da ragamar gidanta batareda wani abu ya raba hankalinta biyu

Tun tana yarinya aure ke burgeta kuma take tsara yadda take burin aurenta ya kasance

Shiyasa bata ta6a ra'ayin aiki ba don aganinta duk silar raba hankali biyu ne shiyasa tun farko taqi aikin office ta za6i tabude nata business din wanda ki tana a gida zata iya running din abinta batareda ya shigarmata a hidimar gidantaba, shiyasa duk nacin daddy saidai yagaji ya kyaleta

Ita bata ta6a tunanin zai dauki wannan abin dazafi ba, dukda ya waske yanuna kamar beji haushi ba ita tasan he's boiling inside

Tasan Ashraf kuma tafishi sanin wannan bangaren nashi saboda shi yafara gwadamata

Tasanshi da saurin fushi kuma tunda ta yanke shawarar zama dashi na har abada tasan tanada aiki gabanta, dole saitayi haquri da wannan halin nashi na saurin fushi amma batayi tunanin tun yanzu zasu fara samun matsala dashi ba, this is just three weeks da tarewarsu, be kamata ace sun fara samun sa6ani ba

Buga tagumi tayi da hannu daya tana tunanin mafita

Jin qarar budewar kofar toilet yasata dagowa

Shine yafito cikin bathing robe yanufi mirror batareda ya kalli side dinta ba

Binshi da kallo tayi harya jawo stool ta zauna gaban mirror din

Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta sauko itama hannunta riqe da bargon data siturta jikinta dashi ta qaraso bayanshi

Yana kallonta ta madubi ta qasan ido harta qaraso wajenshi ta amshe brush din hannunshi tana cigaba da sharce mashi gashin

Bece mata komaiba sai jawo lotion dinshi dayayi zai shafa

"Are you angry?" Ta tambaya a tausashe

Saida ya kalleta ta madubi sannan ya janye ido yana matsa lotion din a hannunshi yace
"No" a taqaice

Zuro kanta tayi ya gefen wuyanshi tana kallonshi ta mirror tace
"You are, am sorry bansan zakayi fushi ba"

Dan ta6e baki yayi yace
"Meyasa zanyi fushi? Ra'ayin ki fa kika fada, bakison aiki under *wani*" yafada yana stressing din Kalmar *WANI* din

Ajiyar zuciya ta sauke sannan tace
"Ba yadda ka daukaba nake nufi, you misunderstood me, Kwata Kwata bana ra'ayin aikinne"

"Shine nace fine ko? Tunda baki ra'ayi ai baxan maki doleba" yafada yana ajiye lotion dayagama shafawa

"You still don't understand me"

"Meye ban fahimtaba? Da Hausa muke magana, why zakice ban fahimta ba?"

"Saboda baka fahimta ba, daka fahimta da bakayi fushi ba" tafada tana danja baya ganin yana niyyar tashi

Closet yanufa yabude yace
"Eh nayi fushi ne dazu saboda ban fahimta ba amma yanzu na fahimta"

"Haryanzu baka fahimta ba tunda ba barin fushin kayiba"

Juyowa yayi ya kalleta hannunshi dauke da kayanda yaciro

"Waya gayamaki am still angry?"

Nuna idanuwanshi tayi tace
"These"

Yar Dariya yayi yana barin gabanta yace
"Then idanunki sun nuna maki ba daidai ba don ni am not angry" yafada yana warware kayan zaisa

"Then musu na burgeka" tafada tana qarasowa gabanshi

Da taimakonta yasaka kayan ya feshe jikinshi da turarrukan shi yasa takalmi

"Where are you going?" Tafada tana kallonshi

Dan kallonta yayi kafin ya kauda kai yace
"Waje"

Dan murmushi tayi ta qaraso wajenshi tace
"Ahakan? Zaka fita kana fushi dani?" Tafada tanadan langwa6e Kai

"Injiki ba"

"A.A bekamata wannan abin yazama wani abu daban ba, ka tsaya my fahimci juna"

Tallabo fuskarta yayi yamata light kiss a kumatu yace
"Ni na fahimceki saidai idan kece baki fahimceni ba, bakison aiki a qarqashin wani, fine.. I won't force you"

Zata sake magana ya dora yatsarshi a la66anta yace
"Shhh please muyi dropping wannan topic din ok? Please... Zan tafi mezan siyamiki"

Girgiza kanta tayi ahankali tana kallonshi

"Bakison komai?" Ya tambaya a tausashe still yana riqe da fuskarta

Kadamashi kai tayi kawai

Kiss ya doramata a lips sannan yace
"To natafi, kije kiyi wanka uhm?"

Kada mashi kai tayi sannan tace
"Allah ya tsare" a sanyaye

Amsawa yayi da amin yana sakin fuskarta sannan yafita tabishi da kallo

Ta dade nan tsaye tana kallon ruffafiyar kofar kafin tasaki Ajiyar zuciya ta wuce toilet donyin wanka

Wunin ranar haka ta idashi a sanyaye batajin dadin komai, komai yinshi take kamar marar lakka gashi yaqi dawowa har magrib

Hakan yasanya ranta ida jagulewa tana jin kamar taita ihu ko zataji sauqi

Shikau a 6angaren ashraf koda yafita rasa inda zaya yayi, he's angry, very angry shiyasa yaza6i yafice daga gidan don beson yayi pouring din anger acan

Karo na farko kenan daya ta6a shanye 6acin ranshi, ada idan yayi fushi yana bursting ne nan take amma yau sai tsintar kanshi yayi da son qin nunawa, shiyasa ma yayi saurin barin gidan saboda yadda yakejin zuciyarshi don qiris yake jira yayi bursting

Awani eatery ya tsaya yashiga, soft drinks kawai yayi ordering aka kawo mashi

Zubawa yayi a cup yafara kur6a ahankali

*wani?* wai *wani*, wai shi take referring da *wani*

Sake kur6ar drink din yayi yana lumshe idanu

Shi a yadda ya dauketa yanzu be kamata ta kirashi da *wani* ba, ya dauka Ai yanzu sun zama daya, komai nashi natane natama nashi ne amma ga yadda ya fahimceta yanzu ita ba haka ta dauka ba

Tana mashi kallon A.A din da, haryanzu mu'amalantarshi take irin na da, idan ha haka ba why zata kirashi da *wani?*

Yasan she's proud amma yayi tunanin wancan karonma don basu shiri shiyasa take nunamashi hakan Ashe a jininta yake

Idan bahaka ba me take nufi da hakan? Wato tafi qarfin tayi aiki qarqashinshi ko?

Haka ya zauna awajen yanata saqa da warwarewa shi daya, Karon farko da yaji be sha'awar sharing damuwarshi da kowa, ciki harda babban amininshi sadeeq

Gani yake wannan matsalar a tsakaninsu ne kuma a tsakaninsu yakamata suyi solving dinta

Bashi yabar wajenba saida akafara kiraye kirayen magrib

Tashi yayi yawuce masjid din kusada wajen yayi magrib yatsaya akayi isha'i dashi sannan yanufo gida...✍️

Meye shawararku ga saudart?

Ta yarda koko ta zauna kan bakanta?

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️
[12/12, 7:47 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖

104

A parking space yayi parking din motarshi yafito yana wurwura makullan hannunshi

Bayan seat ya bude yaciro ledojin dake ciki sannan ya kulle motar yanufi cikin gida

Da sallama yashiga falon, qamshin daya riga ya kama falon tafara mashi maraba gawani sanyi mai dadi da A.C ke badawa

Shiga yayi falon ya nemi wuri a kujera mai daukar mutum daya ya zauna

Jingina da kujerar yayi yana sauke Ajiyar zuciya sannan yadago kafarshi daya ya doro a dayan yana qoqarin zame safarshi

Jin qarar taku yasashi dan dakatawa sannan yadago calmly

Murmushin nan nata mai bayyana beauty point dinta tayi tana cigaba da tunkaroshi cikin salon takunta

Nan take kaso mai yawa daga fushinshi ya yaye yayinda yaji wani sanyi na ratsa zuciyarshi

Lumshe idanu yayi yasake budewa akanta

Sanye take cikin skinny red trouser sai farar top mai fadadden kafada wanda yaba smooth kafaddunta damar fitowa

Kanta sanye da jan hula hakama qaffafunta sanye suke da jan takalmi sai tashin qamshi mai fitinnanen dadi take

Tana kusan isowa wajenshi ta shagwa6e fuska

Sauke kafarshi yayi ya waremata hannu, ganin haka yasa ta qarasa da sauri ta fada jikinshi ta qanqameshi ga mammakinta saiji tayi idanunta sun kawo ruwa

Shima rungumeta yayi yana cusa kanshi a gefen wuyanta yana shaqar daddadan qamshin dake tashi ajikinta

Sundan jima ahakan sannan ya dagota yayi cupping din fuskarta ya hade goshinsu yana kallon cikin kwayar idanunta dake kyalli saboda ruwan dasuka taru ciki
Chapter 104 · 0% Book details