← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 111

Sashe 69

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ahankali yakai hannu ya shafa kanta yana dan murmushi
"Saudart kadai ke gareni, ita kadai ta ragemin duniya da lahira, itace farincikina nine nata, she can do anything just to make me happy amma kwadayina da son kudi yasa nayi tampering da nata happiness din... i forced her, taso nunamin kuskuren haka amma naqiji, na fake da ciwon qarya duk don ta yarda don nasan bazata ta6a jurar ganina cikin damuwaba takasa yimin maganinta muddin tanada ikon yin hakan, haka na tilastamata ba don komaiba saidon nasan zan qaru, itama haka amma dayake allah allah ne saigashi yajuyemana komai ba kaman yadda na tsaraba, ya gwadamin ban isa inyima kaina abinda beyi niyyar yiminba saigashi i end up hurting my one and only child, sanyin idaniyata"

Shasheka saudart keyi ahankali kanta kife da cinyarshi tanajin wani abu na ta6amata zuciyarta.

"Kuyi haquri, words can't express how sorry i am, just find a place in your heart and forgive this greedy man" yafada yana lumshe idanu.

Shiru falon ya dauka, bakajin komai sai sheshekar saudart shima can qasa, anrasa wanda zai magantu cikinsu.

Dakyar kawu ibrahim yabude baki vayan wani lokaci yace
"Kenan vakai kasa aka kamama auwal kayaba?"

Bude idanunshi yayi ya kalleshi yace
"Wane kaya? Ni nakasa gane abinda kuke nufi"

"Bayan rabuwarku da Alhaji da shekaru biyu bakai ka hada baki da customs ba suka kama mashi mottocinshi ba da kayyayakinshi? Har suka biyoshi gida suka burkice gidan?" Inji kawu ibrahim

Girgiza kai Alhaji shamsu yayi cikin confusion
"Customs kuma? Ni alokacin ina dubai"

Abba ne ya sake cewa
"Please ko zaku gayamana abinda yafaru bayan rabuwar margayi alhaji auwal din da Alhaji shamsun?"

Shiru dakin ya dauka sannan ahankali shima kawu ibrahim yashiga bada labarin abinda yafaru bayan rabuwarsu zuwa kama mottocin margayi da akayi zuwa yadda aka gayamasu sa hannun alhaji shamsu ne zuwa jinyarshi zuwa rasuwarshi zuwa wahalhallun da iyalansa sukasha har kawo yanzu.

Sosai Alhaji shamsu tashiga tashin hankali, banda innallilahi babu abinda yake maimaitawa hawaye na zubar mashi.

Kasa cewa komai yayi don he's speechless ma.

"Amma waya fadamaku Alhaji shamsun ne keda sa hannu akan hakan?" Inji abba

"Abokan aikinshi ne"

"Can you specified?"

"Yes, tsohon ubangidanshi ne mallam tukur sai wani abokin aikinshi mallam yunusa"

"Alhaji shamsu waya cemaka margayi shamsu yabar qasarnan gabadaya?" Inji abba yana kallon daddy

Shiru yayi don he is still shock

Dakyar yabude baki bayan wani lokaci yace
"Mallam yunusa"

"Then... akwai wata qullala anan, lokacin da abun yafaru alhaji shamsu ma be qasar koko kuna ganinshi ko jin labarinshi?"

"A'a, tun bayan rabuwarsu da margayi ko labarinshi bamu sake jiba" inji zahradini

"Gaskiya to something is fishy here" inji Abba

"Yes, ni saima yanzu nafara tuna wasu abubbuwan da hankalina be karkata gareshi ba alokacin" inji kawu zahradini

"Kamar?" Inji abba cikin alamun tambaya

"Mallam tukur, farko farkon da margayi yafara hada motarshi yadan chanzamashi kullum shine yayyatashi ga mutane wai beda godiyar allah wai dan qauye yashigo qauye yanason fin ubangidanshi, alokacin banwani dauki abin serious ba don naga lafiya lau suke mu'amallarsu kamar da saidai idan benan ne zaita sukarshi, da allah ya ida budamashi kuma shi dakanshi mallam tukur din yanemi ya ajiyemashi motarshi tunda shima yazama ogan kanshi, mafari kenan dayabar tuqi, shikuma mallam yunusa dama aminin tukur kansu ahade yake.

Bayan rasuwarshi kuma sune nafarkon juyaman baya sukaqi bani mota acewarsu basuda empty mota bayan nasan akwai kawai qin badawane sukai, gaskiya nima i smell something fishy"

"Kenan sune suka hada baki aka cuceshi?" Inji kawu ibrahim cikin wani yanayi

"Bama ceba, amma definiately zasusan wani abu gameda hakan" inji abba.

Shiru falon yasake dauka, shidai daddy besake cewa komaiba don abinda ya dameshi ma ya dameshi, he's soo lost in thoughts

Ashraf kau haryanzu be dagoba saidai jikinshi yayi mugun sanyi, jinshi yake so guilty, bugawa sosai zuciyarshi take kanshi na harbawa. Tsoronshi daya shine kar ace he's taking revenge on the wrong person....✍

Please fans asani acikin addu'a, i really need your prayers, allah yacikamani da kowama burikanmu na alhairi👏

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)

078

Ba Ashraf ba su kansu kawu dasu ummy jikinsu saida yayi sanyi, they never thought Alhaji shamsu was innocent, sanin halinshi na greediness yasasu yarda cewa zai iya aikata hakan, basu ta6a kawoma ransu bashi bane.

"Hasbunallahu wani'imal wakeel! Alhaji shamsu kenan all these years damuke riqe dakai azuciya you're innocent? Ta ina zamu fara baka hqr?" Inji kawu ibrahim a sanyaye.

Shiru falon yasake dauka kowa da abinda ke ranshi, saudart kau haryanzu bata dagoba daga kifa kan datayi a lap din daddy

"Alhaji shamsu we're so sorry, mun makance mun kasa tuna shaquwa da zumuncin dake tsakaninku har muka yarda da magangganun mutanen nan, alokacin gani muke zaka iya dubada yadda abotarku ta watse kukayi baranbaran atunaninmu fansa ka dauka ta wannan hanyar don quntatawa margayi.... will you please find a place in your heart to forgive us" inji kawu zahradini shima asanyaye

"Shiyasa akace zato zunubi koda yazama gaskiya, da wane ido zamu kalleka shamsu?" Inji ummy tana share hawaye.

Ajiyar zuciya daddy ya sauke zuciyarshi na quna, shikau me yayima su mallam tukur zasu jamashi wannan sharrin? Yana iya tuna lokacin da suke aminta da margayi yadda mallam yunusa ke zuwamashi da maganar margayi cewa yaceme kaza yace kaxa duk don yaji haushi amma beta6a biyemashi ba saidai yanuna mashi bakomai ai shima yasan da zancen, bejin zai iya yafemasu, sune sanadin margayi auwal, sunsa ya mutu da baqincikinshi.

"Dan allah ku daina neman yafiya awajena, ni bakumin komaiba, ko nine a matsayinku alokacin dolene in yarda da hakan, idan ma batun yafiyane saidai in nemi naku, wataqila da banso kaina dayawaba na nuna banson haihuwa da bamu samu sa6ani da margayi ba bare har akaiga haka, kuyi haquri mu yafi juna, tabbass na koyi darasi, ko ince darussa, na gane kwadayi mabudin wahalane kuma zafin nema baya kawo samu, please forgive me too"

"Mune xamu nemi yafiyarka shamsu, ka yafemana" inji kawu ibrahim

"Allah ya yafemana bakidaya, yajiqan Auwalu na yasa ya huta yakai rahma a qabarinsa yakuma hada fuskokinmu gabadaya a aljannatul firddaus"

Da amin duk mutanen falon suka amsa cikin sanyi
"To alhamdullilah, dama komai dake wakana a rayuwarnan rubuttacene jikin lau'un mahfuz, gashi cikin ikon Allah komai ya warware mana cikin sauqi, naji dadi sosai da warwarewar wannan matsalar nakuma yi farinciki da bayyanar gaskiya adaidai wannan lokacin, Allah kenan! Kunga ikon Allah ko, bayan shekaru kusan ashirin saigashi yasake hadaku don warwaremuku gaskiya, wannan ba qaramin abun farinciki bane, fatanmu anan shine allah ya jikan margayi dama kullihin musulmai yakuma tona asirin masu sa hannu a sanadin ajalinshi, allah yacigaba da karemu daga sharrin mahassada da maqiya na zahiri da 6uya" inji Abba

Duk da amin suka amsa wanda hakan yai daidai da kwala kiran sallar azahar.

Anan duk akayi haramar tashi yin sallar zuhr din.

Daddy ya umarci saudart takaisu ummy sama su gabatar da sallar.

A kunyace ta tashi tana masu iso sukabi bayanta.

Haka duk aka fita daga falon aka bar daga Ashraf sai sadeeq.

Matsawa sadeeq yayi kusada ashraf da kanshi ke sunkuye haryanzu yakira sunanshi ahankali.

Shiru ashraf yayi kuma yakasa dagowa.

"Ka tashi mallam muje muyi sallah ko sai munrasa jam'i?"

Sai a sannan yadago ahankali ya kalleshi

"Muje" inji sadeeq yana qoqarin miqewa.

"Sadeeq how will I face this man? Tayaya zan iya fuskantarshi after all i did to him? Ya sallam" yafada yana dafe kai

"Hmm i told you ai, ba'a yanke hukunci akan abinda bakada tabbaci akai now see what happen"

"What am i suppose to do? I can't face him, i want to varnish" ya qarashe kamar zaiyi kuka

"Haba varnish to where? Dole kayi facing dinshi ka nemi yafiyarshi and his daughter, afterall qaddarace da baka nemi daukar fansan ba da ba'a kaiga haka ba, da haryanzu zarginshi kuke"

"Can't face him wlh, ka manta da rashin mutuncin da naita mashi? Wayyo kunya"

Muryar kawu zahradini ya dawo dasu

"Wai bazaku fitoba sai an kabbara?"

Juyowa duk sukayi, tashi ashraf yayi shima yya jera da sadeeq kanshi qasa suka fito suma.

Haka suka dunguma suka nufi massalaci dake kusada gidan don gabatar da zuhr.

A 6angaren saudart ma kasa hada ido tayi dasu, haka dai ta kaisu sama ta nunamusu toilet don daura alwalla kafin su fito kau ta shimfidamasu sallaya.

Suna fitowa itama tashiga ta dauro nata alwallar ta fito itama ta shimfida wata sallayar abaya ta tada nata sallar.

Koda tagama suma tuni sun gama saidai ta kasa dagowa daga sunkuyen da kanta yake don ba qaramin kunyarsu takejiba sai mutsu mutsu take cikin hijab.

Duk sun lura da yanayin datake ciki amma suka basar suka shiga janta da fira.

A kunyace take amsa masu wanda yawanci amsar murmushi ne don jitake kamar ta nutse don kunya.

Ahankali ummy ta dauko maganar aurensu inda take nusar daita cewa karta yarda ta cuci kanta, karta yarda tayi za6in da zai cutar daita, tasan komai kuma bazata ta6a ganin baqinta ba idan suka rabu da ashraf, hakan bazai chanza kasancewarta diyarta ba.

Itadai saudart bata iya dago kanta ba bare ta amsa, jitake kamar ta nutse don kunya.

Bayan sallar duk suka fito daga massalacin suna tafe suna fira cikin raha da jindadi.

"I can't still believe A.A dana ne, d'an aminina kuma my in-law"

Duk murmushi sukayi yayinda ashraf yaqara sunkuyar da kanshi qasa yanajin kunyar yadda daddy ke riqe da hannunshi.

Tunda akace shine dan Alhaji auwal yaketa nan nan dashi don kusadashi ma ya tsaya wurin sahun sallah.

Shikau ashraf jinshi yake so uncomfortable, yakasa koda hada idanu dashi jiyake kamar ya 6ace ya huta.

"Kai alhaji yaushe ka ta6a ganin father-in-law da son-in-law na haka? Ina kunyar?" Inji abba yana dariya.

"Ku kuka santa, ni nan dana ne kuma aboki ko son?" Yafada yana kallon ashraf dake sinne kai kamar wata amaryar qauye

Jiyayi kamar ya nutse hakan yasashi qara sunkuye kai

Dariya duk aka dauka kawu ibrahim yace
"Atoh da alama shi bemanta da ita kunyarba"

"Hmm bawani jinin fulanawa ne dake yawo ajikinshi kawai ba komai ba"
Chapter 69 · 0% Book details