← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 111

Sashe 85

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kuma shine akace don you begged and begged and begged taqi sauraronka saikayi giving up? Dama yaya lafiyar giwa? Allah ne kawai ya dubeka yaji qanka badon halinka ba yabaka ita akaro na biyu, maimakon kayi grabbing din opportunity dinka ka gyara kuskurenka kajawota jiki ka dasa sonka azuciyarta ta hanyar wanzar da shakuwa atsakaninku shine zakayi nisa da ita har kana ikirarin ka haqura? Mtcheew amma a gaisheka" yafada yana girgixa kai.

Shiru ashraf yayi yana auna magangganun sadeeq don bakomai aciki sai gaskiya.

Yasan halin ummy idan ta nace kan abu dakyar take chanza ra'ayi gashi dukda yayi zuciyan abun na maqale aranshi don sosai abin ke damunshi kuma yasan ba qaramin aikin ummy bane tashareshi tayi kamar batasan yana yiba harsai ya jigata sosai

"To yanzu meye mafita?" Yafada yana kallon sadeeq.

Harara sadeeq ya watsa mashi sannan yaja tsaki yana cewa
"Kayan takaici kawai"

Shidai bece komaiba don yasan shike nema don haka dole yayi haquri

"Ni nazaci wlh tun ranar zaka magance abin amma dayake kai solo6iyo ne kodayake harda wauta irinta yan fari..."

"Look yafa isheka, wai yaya don zaka bani shawara zaka tisani gaba kanata debemin albarka tundazu, wlh kashiga hankalinka ina ganin girmanka" inji ashraf yana makamashi mugun kallo.

"Au dama yaushe kafara ganin girman nawa? Da kana ganin girman nawa da duk rashin m din dakake shufkamin bazakamin ba"

"Naji please let's talk like two matured people, please let's be serious" yafada cikin dan kwantar dakai

Tsaki sadeeq yaja yana yamutse fuska irin ana nema wurinshi dinnan sannan agadarance yace
"Yanzu abinda zakayi shine ka tattara yanaka yanaka kabi matarka wlh, idan ka zauna zakaga zama ne na rantse, follow her there and pretend ku kadaine agidan, ka nuna bakasan da zaman kowaba gidan, abin nufi duk kulawa da tarairayar dazakayimata kuna ku biyu kayimata acan ba ruwanka dasu, ka cire kunya ka nunawa matarka love agaban koma wanene, am telling you su zasu koma sunajin kunya idan kuma abin ya ishesu bashiri zasu hadoka da matarka su watsoku waje, koya kace?" Ya qarashe zancen yana dagamashi gira daya

"Kenan in koma gidan?,but how sure are you ba zata bani ita din?"

"Mtcheew kai hamago ne wlh, kai ai zakasa tabaka din kotaqi ko taso, cire kunya zakayi kana abubuwan da dole zasuji kunya da gangan, pretend ku kadai ne agidan, afterall matarkace ai, kazama bita zaizai, duk inda take ka bita, kaita maqalemata kana baje kolin love dinka babu abinda yashamaka kai, idan taga rashin kunyar tayi yawa da kanta zata baka matarka.

Ca6 ai anbar sanya yanzu, ni har umma zata riqemin mata tayi kwana uku wajenta? Lallai na rantse idanba aranar idan naga damar kasancewa da matata saina kasance daitaba intafi tsaye, ko dakinta ta 6oyeta saina lalla6a nabita wlh.

Ka duba kaga fa, yau 5months kenan da aurenku amma babu abinda kuka tsinana, sai yanzu komai ya warware shine kuma za'a tsiro wani sabon case? Ca6!

Kodayake harda laifin ka ai, Allah ma yaqara, tun farko kaine ummul'abaisan faruwar komai, shegen girman kanka yajamaka tun farko kaqi bada kai bori yahau shiyasa ai aketa garaka takoina, dama ai ance idan bakayi sharar massalaci ba zakayi na kasuwa, da..."

"Yanxu dai ya isheka, nagode da shawararka, zan duba ingani don haka atashi abarmin office hakanan, thanks for the concern" yafada yana 6allamashi harara.

Sakin baki sadeeq yayi yana kallonshi a mammakince sannan yace
"Kutt.. hakama zakace bayan kasamu na nemomaka mafita?"

Yatsine fuska ashraf yayi yace
"Kuma cema akayi amfani da crooked shawarar taka zanyi? Idanma kaga nayi amfani daita to dama can nayi niyyar yin haka tunkafin kafada don haka atashi abarmin office nace, gauro kawai" yafada cikin son qular dashi

"Kutt.. amma kau wlh kayi da dan halaq, zaka gane bakada wayau wlh" yafada yana miqewa cikin fushi

"Eh, agayas, gauro kawai" yafada yana qyalqyalewa da dariya ganin yadda ya kunnu

"Gakanan jibgegen gauro, ai gwara ni dakai wlh tunda ni banida matar ne amma kai gashi kanada matar amma baka tashi a layin gaurayen ba kuma insha allahu ummy bazata baka matarkaba sainan da shekara daya, insha allahu saina rigaka angwancewa" yafada cikin kumfar baki

Qara kecewa da dariya ashraf yayi yace
"Oho dai, a duk lalacewar goma tafi biyar albarka kuma dai dolene ko a suna ne akirani da mai iyali don wlh nafi qarfin akirani da gauro kuma ko shekaru nawa ummy zata dauka kafin tabani ita bazai ta6a chanza batun narigaka aure ba bare insha allah saina rigaka angwancewa, kai in taqaicemaka da d'ana zamuje daurin aurenka insha allahu, so jeka rungumi transformer" yafada yana dariya sosai kamar ba A.A dinnan ba mai saurin hayaqa.

"Allah ya kiyaye wlh, bakinka ya sari danyen kashi, wazai zauna harku gama wannan shirmen naku har kusamu d'a beyi aure ba? Bakada hankali kuma wlh munanan dakai zaka sake zuwamin da matsalarka, zakaga yadda ake ainihin rashin mutunci" yana kaiwa nan yabude kofa yafita ya maidota da qarfi.

Dariya ashraf yasake fashewa dashi yana komawa kan kujera yana jujjuyawa, sadeeq is just the best, sadeeq ba qaramin kyauta bane da allah yabashi, bazai iya misalta yadda rayuwa zata kaya batareda shiba, gashi cikin dan qanqanin lokaci yakawomashi mafita yakuma sauya mashi mood daga baqinciki zuwa farinciki.

Jujjuyawa yacigaba dayi kan kujerar yana qara tunanin magangganun sadeeq yana ayyana yadda zai gudanar dasu a zahirance...✍

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️
[9/22, 8:32 PM] +234 909 007 1867: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖
(ummin fasihu)

092

Haka ya wuni ranar yanata jujjuya magangganun sadeeq, koda suka tashi daga company ko kallon gefen ashraf sadeeq beyiba shi ala dole fushi yake, shikau ashraf ganin hakan yasashi tisashi gaba da tsokana yana mashi dariya, haka yadawo gida feeling so excited yanajin kamar yayi tsinsuwa yaganshi gidan ummy.

Bayan yagama komai nashi yayi shirin kwanciya yahau shirya kayanshi cikin wata qatuwar trolley, kaya sosai ya loda don ya quduri aniyar duk rintsi bazai dawo hannu biyu ba, duk dadewar dazaiyi ya shirya idanma takama ayi zaman auren can sai ayi ai ba akansu aka fara ba.

Ataqaice dai shine har wajajen 12 yana shirin kaya, dakyar yasamu yagama ya lalla6a ya kwanta cikeda zumudin gobe, jiyake kamar yajawo daren gari ya waye hakanan.

***

Washegari as usual qarfe 9 saura ya isa company, kamar yawuce office dinshi saikuma yajuya yanufi office dinshi.

Murda handle din yayi yajishi gaam alamun babu kowa ciki.

Wani malalacin murmushi yasaki yana wurwura keys dinshi yanufi office dinshi.

Saida yayi settling sannan ya zaro phone dinshi ya danna mashi kira ya kara a kunne yawani murtuke kamar yana gabanshi.

Ringing taitayi harta katse ba'a dagaba hakan yasashi sakin tsaki yasake danna mashi wani kiran yana ta6e baki wondering ko ina yashiga?

Saida kiran yakusan tsinkewa sannan aka daga.

"Heelloo?.." yaji anfada cikin muryar barci

Dan waro idanu sadeeq yayi sannan ya kalli agogon bango yaga 9 saura minti 2 hakan yasashi cewa
"Inyee? Wato barcima kake haryanzu, don ubanka qarfe nawa?"

Cikin muryar barcin yasake cewa
"Yes... am...coming"

"Coming din gidanku? Mtcheew wlh danazo naga baka zoba i thought ka dauki shawarata ce yanzu haka kana gidan ummy, amma kai kasani ai, scallywag kawai" ya katse wayar yanajan tsaki.

Wani mugun tumble ashraf yayi daga kan gado sai jinshi yayi qasa kasancewar dama baki bakin gadon yake.

Wawware idanu yashigayi don shapp ya mance dawanu zuwa gidan ummy, wai tayama wani barcin ya daukeshi, abu na qarshe dazai iya tunawa shine ya zauna gefen gado ya dan kishingida da kan gado yana lazimi yana jiran garin yadanyi haske yatashi yafara shiri. Kai amma a gaisheshi.

Saurin miqewa yayi tsaye yana cire brown jallabiyar jikinshi.

Agaggauce ya tu6e ya rage saura boxer kawai ajikinshi ya rataya towel a wuya yashige bathroom.

Saida yakusan awa daya sannan yafito don yau wanka na musanmman ne😉 ba irin na kullum bane.

Koda yafito direct yawuce gaban mirror dinshi yaja kujera ya zauna kamar irin mace ta zauna zatayi kwalliya.

Sosai ya 6ata lokaci wajen shafe shafenshi don yau komai saida aka qara akan nada, sumar kanshi banda kyalli babu abinda take, dan siririn sajenshi sun kwanta luff sai shining suke, roll on ma saida ya murza kala uku duk masu shegen sanyin dadi.

Saida yagama kwalailaitar sannan yawuce gaban closet dinshi yabude yaciro kayan da dama tun jiya aka riga aka waresu akan su za'asa yau.

Cikin dan qanqanin lokaci ya gama shirin.

Wow! As-in WOW! duk inda haduwa takai to ya kureta, sosai ya hade cikin qannanun kaya wando fari mai layi biyu a gefe gefe kalar royal blue, rigar kuma kalar royal blue mai hula daya saketa abaya, a bayan rigar akwai logo da akayi printing kalar fari mai taken *MONARCH*

kaffafuwanshi sanye da fararen shoes hannunshi na dama daureda agogon kirar Apple fari sai wani qwamemmen shade daya qwamama fuska shima fari amma glass din baqine wulik don bakama hango kwayar idanunshi.

Turarruka saida yafeshe kusan biyar sannan ya gamsu, wayoyinshi ya kwasa ya saka daya a aljihu ya riqe daya sannan ya sauko qaton trolley din jiya ya fiddo qarfen yashiga ja yanufi kofar yana duba agogon hannu shi.

Ganin har 12 ta gota yasashi qara azama ya fita daga dakin ya kulle sannan ya sauka qasa janye da trolley din.

Saida yakashe komai na wuta agidan sannan finally yafita ya kulle kifar yanufi parking space yana wani tafiyar taqama wanda kallo daya zakamashi kasan akwai abinda ya taka.

Haka ya qarasa wajen wata baqar mota wulik ya danna key tun kafin ya qarasa yana wani yamutse fuska.

Yana qarasawa ya bude booth ya kinkimi trolley din yasaka aciki sannan yamaida yarufe ya zagaya mazaunin driver ya bude ya shiga yana kada kai.

Maido kofar yayi ya rufe sannan yajawo seat belt ya daura yayi connecting din wayarshi da mp3 din motar yasanya waqar jaruma ta hamisu breaker yawani qure volume sannan ya tada motar ya figeta gwanin burgewa ya harba kwalta.

💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖💖

Parking yayi a parking space yana sauke ajiyar zuciya.

Bin gidan yake da kallo yana ayyana abubuwa da dama a ranshi.

Kashe kidan motar yayi ya bude kofar ya sauko.

Sake bun gidan yayi da kallo tacikin google din idanunshi yana qarasawa bayan booth.
Chapter 85 · 0% Book details