← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 111

Sashe 68

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Daddy?" Saikuma ta toshe bakinta tana kuka.

Ashraf kanshi na sadde haryanzu idanunshi a lumshe yayinda zuciyarshi kemishi zafi sosai, jiyake komai na dawomashi fresh, tsanar Alhaji shamsu na qara farashi a zuciyarshi.

"Daddy menene? Why are you crying?" Tafada ahankali tana kallon daddyn

Bece komaiba sai sake damqe hannunta dayayi zuciyarshi na qara raunana

"Ashe bazamu sake saduwaba? Bazamu sake ganawa ba? He's gone shalele... Gone" yafada ahankali lokacin dasukayi ada nasake dawomashi fresh.

Saudart batace komaiba sai kallonshi datake itama tana hawaye.

"Ashe bazan samu damar neman gafararshi ba, yamutu da jin haushi na" yafada wasu hawayen na zubomashi.

Zahradini ne yayi karfin halin cewa "meye na damuwa to? Ai dama burinka ya taggayara ko yabarmaka duniyar gabadaya, why making up drama"

Kallonshi kawai alhaji yake batareda yasan inda magananshi yadosa ba.

"Ta dalilin abinda kaimashi yasashi mutuwa, meye na kuka kuma? Bayan abinda kakeso kasamu" inji kawu zahradini yana dan huci trying to control himself

Lumshe idanu Alhaji shamsu yayi zuciyarshi naqara karaya, cikin rawar murya yace
"Bansaniba, b..bansan hakan zaiyi affecting dinshi sosaiba... dana sani..." saikuma yayi shiru yana rufe fuskarshi da taffukan hannunshi.

"Dama tayaya zaka sani? Kayi hakanne don ka wulaqantashi, ya tozarta a idanun al'umma, jin cewa kaine sila yasashi kasa daukar haka, Auwal na sonka da zuciya daya, ya soka da dukkanin zuciyarshi amma ka rasa abinda zaka sakamashi dashi sai wannan don kawai kun samu sa6ani?"

Jujjuya kai kawai Alhaji yakeyi hawaye na zubomashi sosai don ba qaramin zafi zuciyarshi ke mashi ba

"Bansaniba, bansan sa6aninmu zaiyi affecting dinshi ba, nayi kuskure, nayi blunting acikin fushi ne lokacin, ya kamata yasan ba har cikin zuciyata na gayamashi magangganun ba, I was furious ne lokacin, nayi danasanin blunting agareshi tun kafinma yabar gidan" yafada cikin rawar murya sosai

"Ba blunting dinka ba yasashi collapsing, sharrin dakayi mashi ne, ka hadashi da customs su kwace komai nashi? Su biyoshi har gida su wulaqantashi duk don ya nemi kwatantamaka gaskiya? Dama gyara kayanka nazama sauke mu raba ne?" Inji kawu ibrahim da idanunshi shima suka kada

Cire taffikan hannayenshi yayi daga fuska yana kallon kawu ibrahim da jiqaqqun idanunshi cikin rashin fahimta

"Customs? Wulaqantashi? Kamar yaya?" Yafada in confusion

"Bakai bane kamashi kulla kullaba harsu customs suka kwace duka mottocinshi da abinda keciki suka biyoshi har gida suka turning gidan upside down? Ba terere dakayi mashiba yasashi kwantawa jinyar ajali sai yadda ka iya cin amanarshi ka ha'inceshi duk don ya nemi baka shawara as his amini"

Sosai kan Alhaji ya kulle don shi bema gane kan labarinnan ba bare gindinshi

"Ni? Sharri? When?" Yafada cikin mugun confusion....✍

Ummin fasihu ce🧚🏻‍♀️

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖
(Ummin fasihu)

077

"Ni? Sharri? When?" Yafada cikin mugun confusion

Sosai kanshi ya kulle don bema gane inda zancensu ya dosaba.

"Must you pretend? Mu ba wannan bane gabanmu ba yanzu, abunda yakawomu shine samama yaranmu mafita a zamantakewar aurensu, bawai munzo yimaka titsiye ne akan abunda yafaruba shekara da shekaru, wannan tsakaninka da Allah ne da kuma margayi, sakkayar kowa na wajen allah, Allah ba azzalumin kowa bane" inji kawu ibrahim dake ganin kamar rainamasu hankali yakeson yi.

"Please karku barni cikin duhu, ku gayamin, meye kuke nufi da namashi sharri, na wulaqantashi?" Inji Alhaji shamsu cikin kasala

"Look, kamar yadda yaya ibrahim yace ba wannan yakawomu ba, munzo nan ne akan maganar auren diyarmu da danmu ne, meye na pretending? Ai what goes around comes around, gashi bayan shekaru da dama munsake hadewa da bond mai qarfi tsakaninmu wanda baxamuso ya tsinkeba akan kowane daliliba don mu munriga munbaiwa baya baya, gabanmu kawai muke duba, abinda ke tsakaninku da margayi be shafi auren 'ya'yanmu ba, ko yanzu saudart ta yarda ta xauna da danmu zamu riqeta hannu biyu bisa amana don babu abinda tayimana so stop pretending" inji kawu zahradini, kallo daya zakamashi kasan ranshi a 6ace yake.
Abba da tundazu beyi maganaba yayi saurin cewa
"Haba ku kuwa? Duk baikai hakaba, karku manta agaban yara muke and..." saikuma ya kalli daddy dake kallonsu in confusion sannan yace

"Alhaji shamsu, kace bakasan abinda suke maganaba akai?"

"I can swear to you, wlh bansan me suke nufiba"

"Ok zaka iya bamu labarin abinda yafaru bayan rabuwarku da margayi Alhaji auwal?" Inji abba yana kafeshi da idanu

Ajiyar xuciya ya sauke, shi koyaya akace margayin nan sai yaji abu ya ta6amashi zuciya, he can't believe amininshi ne yaxama babu.

Ahankali ya bude baki dakyar yafara cewa
"Auwal ba a aboki kawai na daukeshi ba ko amini, duk yawuce nan, auwal ya mayemani gurbin danuwan da bandashi, auwal komai ne agareni, masoyi, aboki, yaya.

Duk damuwata shi nake kaimawa muhadu cikin ikon allah musamu mafita, shike kwa6ata idan nayi ba daidai ba batareda yin la'akari da yadda zanjiba, shike bani shawarwaru wanda suke matuqar yimin amfani.

Nasan bani acikin jerin mutane masu hallayen kirki, inada son kudi, ina nemansu at every narrow way, wanda hakan yasamo asaline tun kuruciyata da ban saka komai agabanaba sai neman kudi don atunani sune jindadin rayuwa, sune komai.

Auwal yasha mani fada akan hakan amma ban dauka, saidai in nuna ba gamsu kuma bazan sakeba amma hakan be hanani fasawa"

Shiru yadanyi yana sauke ajiyar zuciya sannan yacigaba dacewa

"Mun samu sa6anine dashi bayan haihuwar shalele, na buqaci muje tacire mahaifarta don aganina diya daya ta ishemu, tara 'ya'ya najawo talauci da wahala.

Nan take tanuna rashin amincewarta da hakan, na buga na raya amma taqiya acewarta baxata kashe kanta da kanta ba.

Hakan yasani fita harkarta na qaurace mata, ban yarda auwal yasan da hakanba don nasan bazai ta6a bani goyon bayaba.

Kawai ranan saigashi har shagona lokacin ban gina mall dinaba, fada sosai yaimani kamar zai cinyeni don sosai ranshi ya6aci ashe khadijah taje tasameshi ta fadamashi da abun ya isheta.

Ban tankamashiba harya gama banbaminshi yakuma ce bazata cire mahaifaba saidai ni inje a ciremin kwayakwan haihuwa idan dagaske haihuwarce banso aiba dole sai ita zata cire mahaifaba.

Raina yayi mugun 6aci a ranar kuma bawai fadan auwal yafi 6atamin raiba, A'a qarata da khadijah takai wajenshi yafi 6atamin rai.

Ina komawa gida nima najuyemata nawa kwandon masifar, ataqaice dai munfi sati ana abu guda, har allah yakawo qarshen aurenmu asanaddiyar hakan.

Bayan mutuwar aurenmu da kwana biyu Auwal ya ritsani gida, ashe labari ne yakaimashi.

Ranar naga 6acin ran auwal da ban ta6a ganiba don sosai ya wankeni tass sai akayi rashin sa'a nima lokacin awuya nake don tun bayan rabuwarmu komai yaqi yimin dadi arayuwa.

Bazanso tuna magangganun dana fasamashi ba a ranar... idona yarufe... nakasa gane kuskuren danake tafkawa.... ataqaice dai aranar abotarmu ta watse don kowa alokacin zuciyarshi awuya take ankasa samun daya daga cikinmu dazai ankare da 6arnar damuke shirin aikatawa.

Korar wulaqanci nayi mashi.... nakuma yimishi iyaka da gidana da ni kaina, shima yayimin alqawarin babu shi babu ni.

Tun fitarshi a falona kafin ma yakai gate nafara danasani saidai girman kai ya hanani aikata abinda zuciyata ke rayamin wato inbishi mu sasanta.

Haka na kwana cikin baqinciki da 6acin rai, abu ya hademin goma da ishirin, na farko na rabu da matata da shalelen diyata ga asarar babban jigo danayi.

Ganin garin ya daina yimin dadi kullum ina cikin damuwa yasani barin kasar gabadaya.

Ban tashi dawowaba sai bayan shekaru uku wanda alokacin allah ya budamin sosai naqara arziqi saidai zuciyata naga Auwal dina ina matuqar kewanshi don a daddafe nayi wannan shekarun a can qasar.

Bayan dawowata nigeria na shiga nemanshi saidai tashin farko nakasa gane gidanshi, gadaini a unguwar amma gidanshi ya 6acemin haka nagama bulayi na nakoma gida.

Ahankali ahankali nacigaba da naimanshi amma shiru, ga inda yake aikinshi babu alamun masu irin aikinshi duk ancanzama wurin fasali.

Ataqaice nakusan wata uku sannan allah ya hadani dawani abokin aikinshi Mallam yunusa wanda irin sana'arsu daya dama shima motoci gareshi don yama fi auwal jimawa a harkar.

Sosai nayi farinciki alokacin don aganina nasameshi nagama saidai abinda yafadamin yasa murnata komawa ciki, baqinciki ya maye gurbinta.

Cemin yayi shekararsu daya kenan da barin qasar wai ya saida gidanshi da mottocinshi sun koma turai dazama dashi da duk family dinshi

Haka nakoma gida jiki a mace, ban daddaraba na shirya naje garinsu wudil dukda zuwana daya lokacin rasuwar mahaifinshi.

A wudil ma haka naita galbaro na nagaji don garin ya canza sosai jama'a su qara yawaita, kwanana biyu nabaro wudil jiki a sanyaye nadawo gida.

Haka nakusan cinye sati ina jimami sosai sannan dakyar nacigaba da al'amurrorin gabana saidai auwal nanan maqale a zuciyata ina kuma roqon allah kowanne sallah ya hada fuskokinmu duk daran dadewa.

Ganin kadaici yamin yawa yasa na nemi a maidomin saudart jin mamarta aure zatayi.

Dakyar suka bani ita, sai alokacin nadan samu sauqi don sosai take debemin kewa.

Haka nacigaba da rayuwata daga ni sai yata, nakasa qara aure don mata tsoro suke bani, bana fatan auro wanda zata cutarmin da yata wanda nakejinta kamar tsokar jikina.

Haka naita zama dagani sai yata ina kulada ita agefe kuma nacigaba da business dina inda daga baya na bude mall dina mai suna A.S MALL INTERNATIONAL LTD.

*A.S* din na nufin *AUWAL.SHAMSU* don har alokacin nakasa mantawa dashi, haryanzu... har gobe"
Shiru yayi yana kallon mutanen falon wanda sukayi tsitt banda kallonshi babu abinda suke, ummy idanunta sunyi jajur don tayi hawayen tayi hawayen harta gaji itama umma sosai jikinta yayi sanyi don kallo daya zaka mata kagane hakan.

6angaren su kawu ibrahim ma kallonshi suke suma da alama jikinsu duk yayi sanyi.

Sadeeq dake zaune qasan rug kusada ashraf shima kallo daya zakamashi kasan shima jikinshi amace yake don sai kallon daddy yake da expression din tausayi a fuskarshi, shikau goga Ashraf baka iya gane yanayin dayake ciki don haryanzu kanshi na qasa idanunshi kuma a lumshe saidai daga nesa kana iya hango jijjiyar data fittomashi rado rado a gefen wuya.

Saudart kau kanta na kife akan cinyar daddy tana hawaye silently.
Chapter 68 · 0% Book details