← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 111

Sashe 91

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"And I won't leave without my coffee for crying out loud" yafada shima cikin yanayin data fada

Sauke Ajiyar zuciya tayi tace
"Ok kasaki hannuna tukunna"

"Ki gudu?"

"Zuwa ina?"

"Oho but I assure you kina yunkurin guduwa zan daukeki cak wlh bazan direki koina ba sai cikin mota and direct gida zan kaiki saidai ummy ta farka taga babu ke, kuma try me and see" yafada in a very serious tone

Tsayawa tayi tana kallonshi a mammakince, ganin zai iya yasata sauke Ajiyar zuciya tace
"Alright naji sakeni"

Babu musu ya sakarmata hannu yana kallonta without blinking

Dan murza ankle din hannunta tayi sannan ta bude baki dakyar tace
"Yanzu me kakeso nayimaka?"

"Simple.. Just make my coffee ki kaimin apartment dina shikenan"

"Ok zanyi maka gobe i promised"

Wani kallo yayi mata
"Are you kidding me?"

"Please.. Kaga yanzu dare yayi and ummy na iya jiyomu ta tashi and you know what the result will be, I promised gobe insha Allah zai zama first thing tomorrow morning, I promised"

"Hmm, I need my coffee now not tomorrow miss, idan ma ummy kikeji yanzu am sure she's fast asleep kuma aiba hayaniya zamuyiba... You know what? Da wannan 6ata lokacin damuke da yanzu kin manta da kin hada kin dawo kin kwanta, all I know is yau bazan kwanta ba saina sha coffee dina" yafada firmly yayinda cikin zuciyarshi Dariya kawai yakemata ganin yadda take kallonta in confusion

Dafe kanta tadanyi cikin rasa abin yi ga takaicin baby dake kwance kamar gawa wai ace duk abinda ake bataiba saikace mai barcin mutuwa?

Dagowa tayi ta kalleshi taga shi dinma ita yake kallo yawani jingina da bango ya harde hannayenshi a qirji yana kallonta kamar ya samu mirror

Sauke Ajiyar zuciya tayi nannauya sannan ahankali tace
"Ok"

Murmushi yasaki sannan yamiqe tsaye yace
"Let's go

Badan ranta yasoba ta ziro qaffafunta qasa ta sauko.

Sleeping gown baqa ce a jikinta mai kauri wanda takaimata har qasa sai hular net ja dake kanta wanda ta cusa duka gashinta aciki.

Gwada mata hanya yayi ganin batada niyyar wucewa hakan yasata gittashi ta wuce ya bita abaya

Maimakon tanufi qofa saita maida akalar tafiyarta ga wardrobe din dakin ta bude taciro long milk colour hijab dinta tazira sannan ta nufi qofar fuskarnan hade kamar zatayi bindiga, binta yayi yana murmushi yanajin kamar ya rungumota ta baya ya dauketa in a bridal style yakaita har kitchen din.

Kamar munafukai haka suke sanda wurin sauka stairs din, saudart agaba hannunta tattare da gaban hijab dinta dake jan qasa shikuma biye a baya suna tafiya sadaf sadaf.

Suna gab da sauka qasa hijab dinta ya tadeta tayi gaba zata fadi.

Saurin riqo hannunta yayi ya janyota jikinshi ya tallabe

Ajiyar zuciya ta sauke don ta sadaqar faduwa zatayi

Dagowa tayi daga jikinshi ta sakarmashi harara mai cike da jin haushi sannan taqara sa hannu ta tattaro hijab din ashraf na tayata sannan suka cigaba da tafiya sadaf sadaf kamar qwarrarun 6arayi dasuka qware wajen sanda...✍️

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️
[12/2, 8:33 PM] +234 701 416 6830: 👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖

096

Cikin gida yanufa cikin tafiyarshi ta qasaita.

Koda yashiga falo be tarar da kowaba hakan yasashi haurawa sama domin gaisawa da ummy

Tsayawa yayi yana kallon kofar dakin baby kamar mai shawara can kuma ya janye idanunshi yashiga knocking din kofar ummy

Saida yasake knocking sannan yaji muryar ummy daga ciki tana bashi izinin shigowa.

Murda kofar yayi ya bude yashiga bakinshi dauke da sallama

Caraff suka hada idanu da saudart dake zaune saman bedside locker din ummy tana ninke mata kaya

Sauke idanunta tayi qasa gabanta na faduwa yayinda mafarkinta na dazu yashiga dawomata a qwanya

Kanta a duqe tana cigaba da ninkin kayan hannunta tana sauraron gaisawar dasuke cikin soyayya da nuna kulawa da juna dukda haryanzu ummy bata sakarmashi fuska sosai

Saida suka gama gaisawar sannan itama saudart ta gaidashi batareda ta yarda sun hada idanu ba

Amsawa yayi yana kallonta cikin so da qauna ko kunyar yimata irin wannan kallon agaban ummy beji.

"Kayi breakfast?" Inji ummy batareda ta kalleshi ba

"No, saukowata kenan Ai" ya amsa batareda yabar kallon saudart din ba

"Ok sai kaje kaci" tafada tana janyo wayarta tana dan dubawa

Kallonshi yamaida akan ummy sannan ya yamutse fuska yana yin alamun gajiya yace
"Ummy akawomin nan, am very tired"

Dan kallonshi ummy tayi sannan tadan ta6e baki tace
"Aikin me kayi harka gaji?"

"Ummy jiya fa sai wajajen two na kwanta, am busy working with my secretary"

Jin hakan yasa saudart Satan kallonshi suka hada ido ya kashemata ido daya yana smirking

Janye idanunta tayi tacigaba da abinda take

Ta6e baki ummy kawai tayi bata qara cewa komaiba, can ta dago ta kalli saudart dake ninke kayan wanda ba abinda yasamesu kawai son aikine irin nata da rashin son zama hakanan yasata takuramata saida tabarta tayi din

"Daughter"

Dagowa saudart tayi ta kalleta tana murmushi tace
"Na'am ummy?"

"Jeki ki kawomashi breakfast dinshi kinji?"

Sadda kai tayi tace
"To ummy"

Ajiye veil din hannunta tayi ta tashi ta nufi kofa a kunyace

Binta da kallo yayi harta fita ta rufo kofa sannan ya maida kallonshi ga ummy da ke kallonshi itama

Harara ta gallamashi ta dauke kai hakan yasashi sunkuyar dakai yana Sosa gefen wuya murmushi a fuskarshi

"Meya hanaka zuwa aiki?" Inji ummy batareda ta kalleshi ba

"Nayi taking leave ne" ya amsa a taqaice

Bata sake cewa komaiba saima maida kallonta datayi a wayar hannunta

Suna haka aka bude kofa ta shigo da sallama hannunta dauke da tray data hado kayan Karin akai

Qarasowa gabanshi tayi a kunyace ta ajiye mashi tafara niyyar tashi

Riqo hannunta yayi yana wishpering
"Wazai maki serving din?"

Saurin kwace hannunta tayi daga nashi tana satar kallon ummy a rude sai gani tayi hankalinta ma be wajen su

Hararar shi tayi da wutsiyar ido cikin jin haushi sannan tafara qoqarin hada mashi breakfast din

Ta rasa dalilin dayasa yakeson kunyatata agaban ummy, da tagansu fa? Gaskiya beda kunya ko kadan

Tana cikin hada mashi tea yadan sunkuyo saitin kunnenta ya rada mata
"Fatan baki manta da deal dinmu ba"

Saurin dagowa tayi tana kallonshi sannan taqara satar kallon ummy taga still basu take kalloba

Wai me ke damun wannan gayen ne? Abinda ta tambayi kanta kenan

Dan matsawa tayi daga kusadashi tana cigaba da hadawa a gaggauce don ta qagara ta tashi tabar wajen

Murmushi yasaki na gefen baki wanda shikadai yasan yayi abinshi.

Besake cemata komaiba harta gama hada mashi komai ta tashi takoma wajen kayan datake ninkewa

Jitake kamar ta tafi amma sai gani tayi bedace tabar kingin kayan ba hakanan

Cigaba tayi da ninkin wannan lokacin cikin sauri don jinta take a matuqar taqure

Tana cikin ninkin taji wayarta tayi beeping alamun shigowar massage

Bata damu da ta dubaba tacigaba da abinda takeyi kawai

Wani massage din ya shigo followed by another one duk atare

Hakan yasata dakyar wayar don ganin massage din dukna menene haka jejjere

Number data ganine yasata dagowa ta kalleshi

Kashe mata ido daya yayi yana smirking

Dauke kanta tayi yacigaba da abinda take taji wani text din yasake shigowa

Rolling din idanunta tayi sannan tasa hannu tayi sliding wayar ta bude lock din tashiga massages din

Samun kanta tayi da sakin murmushi ganin abinda ya turamata, kamar bazatayi reply ba saikuma tayimashi replying da emoji din *I don't care🤷🏻‍♀️*

Yana ganin haka shima yasaki murmushinshi yasake tura

*I'll make sure you do babe, it's better ki cika alqawari for your own good amma*

Ganin abinda yaturo yasata ta6e baki sannan ta turamashi emoji din
*oho dai💁🏻‍♀️*

Murmushi yasakeyi yasake mata text da
*hmm don't take it as a joke, am deadly serious, Zan baki mammaki idan kikayi tunanin playing dina cos there will be no mercy*

Data karanta nanma sake ta6e baki tayi tayimashi reply da emoji din🙄🙄🙄

*we shall see* yaturamata yana kwafa afili wanda yasa ummy dagowa ta kalleshi da alamun tambaya

Basarwa yayi yacigaba dacin abincin shi

Bata dadeba tagama ninkin duk ta maidasu cikin closet ta jerasu gwanin sha'awa sannan tacema ummy zata tafi

Cikin fara'a ummy ke mata godiya tana qarajin qaunarta acikin zuciyarta don saudart mutum ce data iya zama da mutane kuma tasan takan yadda zata sace zuciyar mutane da hallayenta kyawawa.

Shidai A.A be dagoba hartayimata sallama tafita

Bata dade da fita ba shima yamiqe ya kwashe kayan yafita dasu

Saida yakai kitchen, maid dinsu dake kitchen din tana qoqarin Dora girkin rana ta amsa cikin girmamawa sannan yadawo yaqara haurowa saman

Wannan karon kofarsu baby ya nufa

Kwankwasawa yayi har sau uku sannan aka bude

Mammaki yakama baby ganin shine don rabonda yazo kofar dakinta har mantuwar ta mance idanma wani abun yake buqata saidai ya kirata a waya ko ya aika a kirata

"Yaya? Good morning"

"Morning" ya amsa cikin basarwa yace
"Tana ciki?"

Tasan wanda yake nufi don haka tabada amsa da
"A'a yanzu yanzun nan tafita wai ta tafi wajen ummy"

"Ok" kawai yace yajuya

Binshi da kallo baby tayi tana gulmarshi acikin zuciya ta shige ciki tana kada kai

Bebi takan dakin ummy ba ya sauka yafita yanufi parking lot

Yashiga motarshi yafice daga gidan

Koda yadawo ma be gantaba, haka yasha zamanshi a falo duk don yaganta amma ko wulginta be ganiba.

Da zasuyi dinner ma bata saukoba saisu ummy shikuma yakasa tambaya

Haka yaita zuba ido ko zai ganta amma shiru

Da daddare ma saida ya lalla6a yaje dakinsu saidai wayam baby kawai ke dakin wanda hakan ke nuni da yau dakin ummy saudart ta kwana

Haka yakoma part dinshi yana cizon yatsa tareda ayyana yadda haduwarsu zata kaya.

Wasa wasa kwana uku kenan suna wasan yan 6uya tsakaninsu

Basu haduwa sai a lunch da dinner don yanzu abinda ke sauko da ita kenan tinda taji yadawo gidan shima da zama, da angama zata haye sama tashige dakin ummy

Kwata Kwata bata yarda su hade a inuwa daya su biyu kacal, kullum tana maqale dakin ummy.

Saidai hakan be hanasu magana through text massage, koda yaushe cikin warning dinta na karta yarda su hade don with every passing day tana adding salt into injury ne
Chapter 91 · 0% Book details