← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 103 OF 111

Sashe 103

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kiyi harkokinki yadda kika saba koma fiyeda hakan, idan ke keda laifi zafin zuciyarshi zai rage ganin yadda kika hidimta mashi idan kuma shi keda laifi jikinshi zaiyi sanyi ganin yamaki laifi amma baki qullaceshi ba saima alhairin dakika sakamashi dashi

Aduk abinda kike ki tuna bautar Allah kike kuma neman aljannarki kike, neman aljanna Nada wuya amma mu mata sai inga kamar Allah ya saukaka mana, mijinmu aljannanarmu, mu kyautata musu musamu aljannarmu, so simple but hard to many of us saboda girman kai irin namu

Wasu gani suke yawan kyautatawa miji raini yake kawowa, wasu kuma kyashin yin wani abin suke saboda gani suke daya suke dashi, wasu kuma raini dama yariga yashiga tsakaninsu gani suke mutuminda tsirara yakeyi gabansu ai bawani batun girmamawa

To annabi s.a.w yace 'da anama wani sujjada bayan Allah subhanahu wata'ala to da an umarci mata dasuyima mazajensu sujjada'

Idan zaki kalli mijinki karki kalleshi a matsayin miji kawai, ki kalleshi a matsayin wanda zai Kama hannunki ya shigar dake aljanna, ki kalleshi amatsayin tsaninki zuwa aljanna

Bayan wannan kuma akwai yanmata yanzu birjik masu neman damar auren mijin sakarya

Mijin wacce batasan inda kemata ciwoba, damunsan yadda wasu yanmatan goggagun yan bariki ke neman irin wannan damar damun qara tamqe belt dinmu don wasu yanmatan ko zawarawa sunfison ire iren wadannan mazan wanda matayenshi basusan komaiba gameda damqe miji ahannu sai shashanci daya cikamasu kwalwa, yadda sukuma zasu shigo su murza kanbunsu yadda sukaga dama, kina hangame da baki kiga miji yamaki Nisan da saida tantado zaki iya hangenshi yadda daga baya kokin dawo kina abinda yadace abaya kiyi bakiyiba bazaki isheshi kallo ba don bazaki burgeshi ba don ihu bayan hari kikayi kuma bazai ta6a yarda don Allah kikayi ba gani zaiyi dan kinga Amarya nayi shiyasa kema kikafara hakan ba qaramin zubarmiki da mutunci zaiyiba a idanunshi. A word is enough for a wise💁🏻‍♀️

Now back to business😎

A falon ta kawo abincin kamar yadda ya buqata

Sauka sukayi a centre carpet suka zauna tashiga serving dinsu

Saida tagama sannan ta dago ta kalleshi taga ita yake kallo hakan yasata kashe mashi ido daya tana dagamashi gira daya alamun xupp?

Murmushi yayi mata kawai ya maida hankalinshi akan abincin yafaraci suna dan ta6a fira

Can saita sarqaho hannunta cikin nashi ta kwantar da kanta bisa kafadarshi

Hakan yasa yadan juyo ya kalleta

Itama kallonshi tayi saita marairaice fuska tana turo baki tace
"Am sorry"

Murmushi yadanyi yace
"For what?"

"For everything, bansan kalamaina zasu 6atama raiba dazu I wouldn't have use the words, am sorry" tafada tana kama kunnuwanta

Murmushi yasake yimata sannan yadan sunkuyo kanshi yayimata kiss a goshi yace
"Apology accepted"

Wara idanu tayi ta qanqame hannunshi dake cikin nata tana murna tace
"Oh thanks my Zuma" taqarashe tana kissing din damtsenshi

Murmushi yayi shima yayi kissing din forehead dinta yace
"Thanks also my sweet, and nima forgive me"

"Ni bakayimin komaiba"

"Nayi mana, am trying to force you against your wish"

"No your wish is my command, I shouldn't have argue with you amma gani nayi as a wife kamata yayi ace ina gida always taking care of you and our home"

"Yes amma nidin dazaki kula dani wuni nake a office, idan na fita tun safe sai da marece sometimes sai dare, kinga saina dawo zaki kuladani while ina buqatar kulawarki duk yinin ranar, saudart bansan daliliba banason matsawa ko nan da can daga wajen ki, I always miss you, ina kewar firarki, your smile, your face, your scent, everything

Idan ina nesa dake I always feel lonely, hankalina saiya kasu biyu, mafi rinjaye na awajen ki, nasan kona koma office bazan iya abin kirkiba saboda kewarki, zanso ace kina kusadani koda yaushe, mu tashi tare muyi break tare mu shirya tare mu fito tare, yazama kullum ke zaki dinga driving dina zuwa office, nikuma inmaido mu gida vice versa
Besides kinada qualification din zama secretary dina wanda samun mai cancanta irin naki zaiyi wiya, aiki tareda ke wancan karon ba qaramin nasara yakawoba a company din dukda alokacin ba shiri mukeba, to inaga yanzu? Kuma kowa zai zama secretary dina anan gaba baxan iya trusting dinshi ba kamar yadda zanyi trusting dinki don kingama winning din trust dina, baki ha'inceniba sadda muna maqiya ya za'ayi kiyi yanzu muna amatsayin ma'aurata kuma masoya?

Amma ba komai tunda bakida ra'ayin hakan baxan takura miki ba, zan samu wata, zansa a liqa vacancy letter nasan insha Allah zan samu wanda itama zata cancanta" Yaqarashe yana daukar spoon don cigaba dacin abinci

Saudart da tunda tafara magana takejin wani sanyi na sanyaya mata zuciya ta hade rai jin kalamanshi na qarshe

Binshi da kallo tayi ganin yama maida hankalinshi ga abincin yanaci hankalinshi kwance, nan take taji wani abu yazo ya tokare mata zuciya

Sunkuyar da kanta tayi tana hadiye abinda ya tsayamata wuya yayinda takejin wani mahaukacin kishinshi na tasomata

Wato zai samu wata, duk abinda ya lissafa suyi, yaita ganinta koda yaushe, suyita magana kuma koda wane lokaci suna tare ita kuma tana gida sake da baki saiya dawo sannan zata ganshi

Tunawa tayi da haduwarsu tafarko da tsohuwar secretary dinshi, tunawa tayi da shigarta, yanzu haka zaisamo wata tayita shigar dataga dama ta janye mata shi?

Nan take taji ranta ya jagule, ranta ya 6aci, abincin Kwata Kwata yafita ranta

Ganin kamar bataci yasashi dagowa ya kalleta

"Why are you not eating?" Yafada yana kallonta

Kallonshi tayi fuska a kumbure saikuma ta juyamashi baya

Dan lekota yayi ta bayanta yace
"Menene?"

Matsawa tayi daga gefenshi takoma can dan nesa dashi tace
"Ni ka kyaleni"

Galala yayi yana kallonta yace
"Ni menayi kuma?"

"Oho? Bacewa kayi zaka samu wata ba? Saikaje kasamu" tafada idanunta nakawo

Shiru yayi na wani lokaci yana kallonta saikuma yafashe da Dariya sosai yana nunata

To dama mai neman kukane aka jefa da ledar kashi
Ganin hakan yasata 6ata fuska ta maida kanta tsakankanin gwiwa tafara hawaye

Da farko ya dauka wasa take amma jin sheshekar kamar ta gaske yasashi dago fuskar

Mammaki yakamashi ganin fuskar jage jage da hawaye

"Subhanallilah, wai dagaske kuka kike?"

Ture hannunshi tayi ta maida kanta bisa gwiwa tana cigaba da kukanta

Dariyar dake neman kufcemashi ya danne ya rungumota jikinshi yace
"Oh am so sorry, wlh bansan kinji haushi ba"

Fizge kanta tayi daga jikinshi tana cewa
"Leave me alone, kaje kasamu watan saime?" Tafada cikin muryar kuka

Riqe baki yayi saikuma yasake kamota ya maidata jikinshi yace
"Haba my princess, meyayi zafi? Kefa kikace bakiyi?"

Qara fizgewa tayi tace
"Ni yaushe nace hakan?"

Wara idanu yayi yace
"Kefa kikace bakya ra'ayi"

"Yanzu kuma nace inayi" tafada tana murguda mashi baki

Dariya yafashe da ita harda tafi yace
"Someone is jealous here oh"

Fadawa tayi jikinshi tana dukan qirjinshi tana kukan shagwa6a shikau sai Dariya yake

Ganin bazata bariba yasashi kamo hannayenta ya riqe yana qara rungumeta

"It ok..it ok, yanzu kin yarda zakiyi?"

Turo baki tayi ta qara sinne Kai ajikinshi

Dariya yayi ya dagota yayi cupping din fuskarta
"Uhmm?"

Saida ta harareshi sannan tace
"On one condition"

Dariya yayi yace
"Harda sharadi?"

Bata amsamashi ba sai hura hancin datake

"To inaji meye sharadin"

Sniffing tayi sannan tace
"Saika gayawa ummy sannan"

Dan kafeta da idanu yayi sannan yace
"Why?"

"Saboda yin shawara da nagaba dakai musanmman mahaifa yanada kyau domin sunfimu hangen nesa"

Sosai yaji dadin abinda tace sai cewa yayi
"Naga dai alamar sokike ki nuna kinfini son ummy, to ummin nan dai tawace naga alamu qwace kikeson yimin tuntuni, to kin makaro" yafada yana mata gwalo

"Kwace tun yaushe nayimaka? Kaidaine baka farga ba" tafada tana mashi hararar wasa

"Eh din kidau ummin dama ta isheni ni zan komawa Mamy" yafada shima yana hararta

"Oho dai, idan Mamy ce gaka gata"

"Jealousy kawai" yafada yana Dariya yayinda itakuma ta hade rai tacigaba dacin abincinta

Haka suka qare cin abincin cikin raha da tsokana sannan yatashi ya dauketa kamar Yar tsana ya haye daita sama...✍️

Ummin fasihu🧚🏻‍♀️

[12/10, 6:57 PM] +234 813 274 0349: 🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Story written by Ashaanty love💖

103

*A WEEK AFTER*

Zaune yake bakin gado, jikinshi sanye da farar singlet wanda ta fiddo muscles dinshi sai wando baqin three quarter

Laptop ke gabanshi yana operating sai mug din coffee dake gefenshi yana tururi, aiki yake a laptop din yanayi yana daukar mug din gefenshi yana kur6a akai akai

Jin qarar budewar kofa yasashi dagowa daga laptop din

Tsayawa sukayi suka kafe juna da kallo nawani lokaci kafin tasaki wani kafirin murmushi na gefen baki ta qaraso cikin catwalk dinta

Tana zuwa ta dauke laptop din cinyarshi ta maye gurbinta ta tareda saqalo hannunta around wuyanshi

Cusa kanshi yayi aqijinta yana shaqar qamshinta yana moaning ahankali

Ture kanshi tayi tana Dariya ahankali tana cewa
"Naughty boy"

Saurin maidota yayi a cinyarshi ganin tana neman tashi ya rungumeta gamm yace
"And where did you think you're going?"

Dan bude idanu tayi tace
"Kwantawa zanyi, ga laptop dinka kacigaba da aikinka nizan kwanta, sleepy" tafada tana hamma saikuma ta daga hannaye sama tana miqa wanda ko ba'a fadaba kasan ta tsokana ce

Rungumeta yayi sukayi rolling zuwa tsakiyar gadon ya dawo samanta ita tana qarqashinshi

"Are you trying to seduce me? Tell me" yafada yana dan cizon kunnenta in a sexy way

6ata fuska tayi tace
"Seduce kuma? Nidai kaje kacigaba da aikinka am sleepy"

"Bakiso inyi aikinba Ai"

Kafin tace wani abu ya hade bakinsu waje guda suka Lula duniyar ma'aurata

Kwance suke bayan komai ya lafa, sunja bargo ajikinsu tana kwance ajikinshi tana wasa da gashin qirjinshi

"Mi-lady wai meye sirrin ne?"

Dagowa tayi ta kalleshi sannan tace
"Sirrin me?"

Saida yayi kissing din forehead dinta sannan yafada cikin rada
"You're always sweet, kullum qara dadi kike? What's the secret behind this?"

jan gashin qirjin nashi tayi da dan qarfi hakan yasashi sakin qara

"Ouch! It hurt" yafada yana Sosa wajen

Saudart data tashi zaune tun sadda tayi mashi muguntan ta fashe da Dariya tace
"I know, dan wulaqancin saikace ina dadi?, ni abinci ce"

"A'a ke abin ci ce" yafada yana kashe mata ido in a naughty way

Fashewa da kukan shagwa6a ta fada jikinshi tana kaimashi dukan wasa a qirji
Chapter 103 · 0% Book details