← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 111

Sashe 45

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nasha fadamaka yarinyar nan batada masaniyar abinda ke tsakaninka da mahaifinta, she has no case in this at all, amma ka saurareni? Instead kullum cikin Neman hanyar dazaka quntata mata kake, kullum cikin 6ata mata rai da cimata mutunci kake, what did you expect from her? So kake duk bayan abinda kakemata tazo tana godiya tana washe maka baki? Me zai hanata tsanar ka? Karka manta zuciya tana son mai kyautata mata ne tana kuma Qin mai muzguna mata, kai ka auna kanka a mizani kaga a wane bangare kafada kafin kayi complaining din ta tsaneka" yafada cikin bayyana fushinshi da baida kyan gani.

Haryanzu Ashraf be dago kanshi ba kuma bebar dan bubbuga desk din ba da pen ba amma idanunshi sun kada sunyi jajur don kalaman sadeeq direct suke wucewa cikin zuciyarshi suna mai barazanar tarwatsata.

"Ashraf, saudart mutum ce, tacika yar halak, despite abubuwan dakake mata amma ji abinda ta sakamaka dashi, ta saka alhairi ga sharri, ka tsaya kayi nazari daga farkon haduwarku zuwa yanzu me tayimaka na Rashin dacewa kai kuma me kayimata na Rashin dacewa tsahon wannan lokaci saika dorasu a mizani kaga wane zai rinjayi wani.

Ashraf saudart has a good heart... Golden heart.

Tanada qualities da ba kowacce mace ke dashi ba a wannan zamanin.

*Biyyaya* da *sanin darajar mutum*

Biyyayarta yasata Qin bijirewa mahaifinta dukda ranta besoba, sanin darajar mutane kuma yasa bata ta6a wulaqanta wani ba musanmman mai alaqa dakai dukda abinda ke tsakaninku, kaifa?

A kullum bakada abin wukaqantawa kamar babanta a gabanta.

Tell me, wannan be isa tsaneka ba? Tell me!" Yakai aya Yana dan huci sama sama

Runtse idanunshi Ashraf yayi gamm yana sauraron yadda zuciyarshi ke bugu da qarfi ga wani zafi na musanmman data keyi.

Shima shiru sadeeq yayi yana maida kanshi bisa jikin kujera yana dan sauke numfashi ahankali.

Sun kusa minti daya babu Wanda yayi magana sannan sadeeq ya dago kanshi daga jikin kujerar daya jingina daita ya kalli Ashraf dake kallon desk haryanzu hannunshi still riqeda pen amma yabar bubbugawa

"Ashraf kayi wa baiwar Allahn nan ba daidai ba, shigowarta arayuwarka alhairi ne, kamanta da abinda tayimaka yanzu, ko babu wannan ta kawo farinciki a ahalinka, Ummy da baby nakasancewa cikin farinciki marar misaltuwa by mere ambaton sunanta, suna Sonta kuma tana sasu farinciki duk sanda sukayi tozali daita, wannan baiwar ba kowa Allah yaba ba, ko anan aka tsaya kasan ta cancanci girmamawa" yafada cikin tattausan laffuza kamar bashi ke fada yanzu ba

Zagayowa yayi kusada inda ya sunkuyar dakai ya dafa kafadarshi sannan yace
"It's not too late, kai ka koyamata qinka, Kai zaka koyamata akasin haka, kawai kayi qoqarin amfani da damarka kar jin kanka ya yaudareka har damarka ta su6uce maka"

Nan ma shiru bece komai ba kuma be dagoba.

Sadeeq bedamu da hakan ba yakoma ya zauna yana cewa
"Yanzu the major thing shine mufara gamawa da case din mutanen nan, saudart tayi fiyeda Rabin aikin, mu saura ide ide. So cheer up guy, munada aiki gaban mu" yafada trying to be carefree.

Ranan dai haka Ashraf ya wuni jiki amace, yarasa abinda ke mashi dadi, duk Yama bar zancen mutanen Spain, sadeeq ne keta fafutukarshi akai shikau saidai ya zauna yayi jigum zuciyarshi fall tunani.

Sai six yauma yabaro company yayo gida direct.

Tun a parking space ya tabbatar da bata gidan don babu motarta a space din.

Parking yayi ya fito cikin sanyi yashiga cikin gida still hannunshi damke dawayarta dake hannunshi.

Da sallama yashiga falon yana dan sassafta daurin necktie dinshi yana qarewa exclusive falon kallo.

Saida yagama loosening din necktie din sannan yanufi stairs yafara takawa ahankali harya haye sama.

Kamar yadda tasaba yan kwanakin nan tsayawa yayi yana kallon kofar dakinta tunani kala kala na Kai komo a zuciyarshi.

Ya Dade ahakan sannan yashige dakinshi.

Ana kiraye kirayen sallar magrib yafito da alwala don tafiya masjid.

Qara kallon kofar yayi yana ayyana tadawo tunda duk inda take bata wuce magrib.

Jin ana Neman tada iqama yasashi sauka yawuce masjid.

Saida yayi isha'i ma sannan yadawo.

Kallon parking space yayi yaga still babu motarta, tsayawa yayi yana kallon wajen tunani kala kala namashi yawo a qwanya.

Wucewa yayi yashiga falon ta zauna daya daga cikin kujerun falon ya kunna kallo yana kallo amma hankalinshi kwata kwata yana waje yana sauraron dawowarta amma shiru har 10.

Tashi yayi yana wondering what keep her so long outside, waje yafita ya tsaya a balcony yana kallon hanyar shigowa gidan.

Ya Dade sosai a tsaye yana tsaye yana kallon kofar shigowa amma babu alamun ta.

Ganin har 12 bata dawoba yasashi juyawa asanyaye yakoma falon ya zauna kan three seater din falon yana tunanin to inatake, ko tana gidansu? No ai it's not yet over, bazata tafiba just like that, she can't.

Zamewa yayi kan kujerar yana mai tausayawa kanshi don yafi kowa sanin kanshi idan ya kwallafa rai akan Abu yakuma so abun Tofa ya dinga wahala akanshi kenan yasan be iya son Abu ba kamar yadda be iya Qin Abu ba.

Fiddo wayarta dake hannunshi yayi ya kunnata yayi sliding, wannan kyakyawar fuskar, ma'abociyar fara'a da kyawu ta bayyana.

Tsayawa yayi yana kallonta kamar yau yafara ganinta, sannan ahankali yashiga cikin gallery dinta yafara bin hotunanta daya bayan daya yana kallo yayinda abinda yakeji gameda ita ke qara hawa, zuciyarshi na qaimi wajen zaburar dakuma rura wutar soyyayarta a zuciyarshi...✍

Tofa! Team A.A sai a tanaji handkerchief don yanzu the mighty Ashraf is in saudart mercy😆

Team S.S lokacin Ku ne💃 amma fa a tausayamana kar a wahalar damu dayawa.

Insha Allah da komai ya warware zaku dinga samun update akai akai

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Am back💃💃💃

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

056

Wasa wasa tun Ashraf na zuba idon ganin dawowar saudart har yafara surewa.

Yau Friday Wanda yayi daidai da ranarda akayi shara'a da mutanen Spain.

Anyi bincike anga basu kadai suka yaudara ba, sun yaudari mutane da dama ta wannan hanyar don haka aka yankemasu hukuncin zaman gidan yafi na tsawon shekaru goma bayan sun biya duk wadanda suka yaudara kudadensu, qarshe ma company dinsu akasa kasuwa aka siyar sannan aka ba kowa haqqinshi cikinsu harda su Ashraf.

Duk wannan bidirin da ake hankalin Ashraf be wajen sosai, duk sadeeq ne ya tsaya a komai don yakasa gane kan Ashraf, yakoma wani soo silent dashi, dama yanada dan miskilancinshi tou sai abin ya hade da damuwa sai ya kasance duk inda kaganshi zaune yake shi kadai yana qurama waje guda idanu.

Kwana hudu kenan rabonshi da ita, bata zuwa office, bata gida, bata bakery don kullum ne sai yaje bakeryn yayi parking daga nesa yana kallon masu shige da fice amma ko mai kama daita begani.

Har spy yasa Wanda zai zauna permanently wajen don ganin ko za'a samu akasi yana tafiya tazo amma duk amsar dayace, babu saudart.

A gida ma Ummy ta lura da yanayinshi dukda idan yaje yakan fuske yaita acting normal amma dayake uwa uwace ko yaya danta ya sauya koda ya 6oyemata saita gane, tasha tuntu6anshi akan abinda ke damunshi amma saiya waske da gajiya ce ko ayyuka sukai mashi yawa.

Dayake su Ummy ma sunada labarin yaudarar da akayi musu yasata ganin qila duk akan maganar ce, saidai har kawo yanzu basu ta6a sanin saudart na aiki a companyn shi a matsayin secretary ba bare Susan itace silar warwarewar wannan qulla qulla ba don ko wannan tafiyar dasukayi su a tunaninsu aiki yatafi da Matarshi don haka basuda masaniya akan komai bare su zargi komai.

***********************************************

*MONDAY*

Zaune yake a kujerarshi mai jujjuyawa, hannayenshi harde a Qirjinshi yayi balancing a kujerar idanu a lumshe sai jujjuyawa yake a kujerar kadan kadan.

Sanye yake da suit saidai tasaman na rataye a jikin wani hanger dake daga gefen office din, sai farar shirt da baqin wandon daya bari a Jikinshi, gashin kanshi kwance luff sai sheqi yake.

Kamar kullum yau ma tunaninta daya zaman mashi jiki yake, dama da ka ganshi haka shi kadai yayi zurfi a tunani to ba kowa ke maqale a zuciyarshi ba sai ita.

Tunaninta ke debe mashi kewa, hotunan ta ke sashi nishadi, don kullum yana maqale da wayarta yana kallon hotunan ta.

Yanzun ma tunanin inda zai ganta yake, koda yake baza'a ce besan inda take ba, hasalima yafi kowa sanin inda zai sameta saidai baya tunanin zai iya binta har wajen, bazai iya binta har can ba don aganinshi hakan ba qaramin zubda mutunci bane, hmm karkuyi tunanin soyyayar saudart ta chanza shi ko yayi laushi.

A'a he's still the proud Ashraf dakuka sani, haryanzu jin kanshi na nan, badan haka ba da tuni yabita har gidan daddy ya dawo daita amma gani yake hakan ba qaramin zubda class bane.

Yes yasan yana sonta amma hakan bazai sa yajawowa kanshi raini ba, shi yanzu kawai soyake tadawo, idan yasamu tadawo to komai zai tafi cikin sauqi, zaisan yadda zai cusamata soyyayar shi, yadda zai yimata mummunan kamu taji duk duniya babu Wanda take so saishi, shikuma sai yadan jamata aji sannan ya nuna yafara Sonta😒

Haka yaita wawwanawa a kujerar yana tsaka yana kwance wa akan yadda zai 6ulloma al'amarin.

Jin bubbugar kofa yasashi dagowa yana kallon kofar office din.

Sake bubbugawa akayi a Karo nabiyu hakan yasashi Jan guntun tsaki don ya tsani a dameshi yana cikin tunani musanmman ma irin wannan.
"Yes? Come in" yafada cikin harsh voice sannan yajawo wata takarda yana kallo fuska a daure.

Murda handle din kofar akayi sannan aka turota aka shigo sannan aka maida aka rufe.

Jin muryar sadeeq na sallama yasashi amsawa qasa qasa sannan ya dago da niyyar tambayarshi lfy?

Idanunshi basu sauka a koina ba sai cikin nata.

Cak bugun zuciyarshi ya tsaya, jinin Jikinshi ya daina gudana yakuma kasa ko kyafta ido akanta.

Cikin takunta Wanda nayau yafi na kullum ta qaraso gaban table dinshi.

"May I?" Tafada tana Jan kujerar gaban table din baya ta zauna batareda ta jira jin ko yabata izinin zamanba ko A'a.
Chapter 45 · 0% Book details