← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 111

Sashe 35

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washegari gidan mamy taje ta yini, sosai taji dadin zuwanta don dama tayi kewarsu, wannan karon sun hadu da Abba kasancewar ranar yadawo daga wata tafiya, nan suka hadu sunata fira gwanin sha'awa.

Anan take gayamasu batun tafiyarsu Spain acewarta aiki zaije shine zai tafi daita.

Addu'o'i sukayi mata sosai da shawarwari nagari sai la'asar tabar gidan tawuce mall din daddy.

Dariya taita yimata daddy ganin sai kakkauda kai yake wai besan su hada ido.

Tun yana kunyarta harya ware sukaita fira don saudart bata wani dauki abun dazafi ba yadda yayi tunani.
Sai tambayarta yake ya A.A ke treating dinta sai tace lfy, beyimata komai.

Matsamata yayi akan tayi shopping na tafiya.

Dafarko taqiya amma daya matsamata saita dan tsinci gowns kadan.
Ganin haka yasa Dad yimata shopping din dakanshi, gowns yan kanti ya kwasanmata kala kala kowanne da March na shoes da bag dinshi.

Sosai taita complaining sunyi yawa amma shi ko a jikin shi Shidai burinshi ya faranta mata.

Ba ita tadawo gidaba sai wajajen 9:00pm shima daddy ya kawota dakanshi.

Fitowa tayi tana dagamashi hannu harya wuce, she's so happy, duk saita nemi baqincikinta ta rasa.

Haka tashigo gidan niqi niqi da kaya, tun a parking space tagane yana gidan.

Da sallama tashiga falon, hangenshi tayi kan daya daga cikin cushion din falon ,zaune sanye da baqar singlet da baqin wando ya duqufa kan laptop.

Kallo daya sukayima juna suka kauda kai.

Wuce shi tayi ta hayewarta sama batareda tasake kallonshi ba tashige daki

Toilet tawuce tayi wanka don ta kwashi gajiya sosai.
Koda tafito shirya wa tayi cikin kayan barci sannan tahau shirya kayanta.

Saida ta tabbatar ta kammala komai sannan tabi lfyr gado ta kwanta tana sauke ajiyar zuciya...✍

No editing🙏

Ummin fasihu ce🧚‍♀

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

045

Qarfe goma daidai tafito daga dakinta sanye da wata jallabiya peach colour mai adon pink agaba tayi rolling din gyalen jallabiyar, hannunta daya riqeda handbag dayan kuma janye da qaramin trolley.

Saukowa tayi janye da trolley din jikinta sai tashin qamshi yake.

Tsayawa tayi a falon ta kashe komai na wuta kamar yadda tayi a kitchen da dakinta sannan tafito waje walking majestically kamar ba ita ake jiraba.

Ashraf ya qulu iya quluwa, tundazu ya aika drivern dazai kaisu yakirata amma sai yanzu taga damar fitowa.

Ta side mirror yake kallonta ta taho kunnenta kare da waya da alamu waya take ga wani sihirtaccen murmushi datake saki Wanda ya bayyana jerrarun haqoranta farare Tass ga dimple dinta na dama daya lo6a.

Tsayawa yayi yana kallonta don tunda yasanta be ta6a ganin murmushinta ba she's always moody or expressionless.

Qarasowa tayi driver yayi saurin fitowa ya zagayo ya budemata kofar baya side din dama tashiga ya rufe sannan ya zagaya baya don saka trolley din a booth.

Qamshin turarenshi dataji gab daita yasa gabanta faduwa, batayi tunanin tare zasu tafiba don koda driver yazo dazu tazaci shizai kaita shi Ashraf din yariga yayi gaba.

Cikin dabara ta gyara zama tanasa style tana dan matsawa daga gefenshi.

"Ok sweet dad saina kira din, love yah" tafada tana blowing mashi kiss

Sannan ta katse kiran tana qara dan matsawa daga gefenshi.

Satan kallonshi tayi da wutsiyar ido taga hankalinshi nakan wayar hannunshi fuskar nan kamar anmashi bishara da jahannama.

Ta6e baki tayi ta maida kallonta ga windown motar tana kallon waje yayinda drivern ya tada motar suka fice.

Tsit motar tayi babu mai ko qwaqwaran motsi, kowanne ya maida hankalinshi ga abinda yashamashi kai.

Saudart sai kalle kallenta take ta window, ganin andauki hanyar gida Ummy yasata jin wani irin farinciki har cikin zuciyarta.

Horn daya yayi aka wangale musu gate din suka shiga sannan direct suka nufi parking space

Bata jira akazo aka budemata ba ta 6alle murfin motar tafita da sauri tanufi su Ummy dasuma suka nufi parking space din.

A tsakiyar hanya suka hadu suka rungume juna saudart da baby dake ta tsallen murna itakam saudart sai dariya take.

Sakin baby tayi ta qarasa wajen Ummy daketa washe baki ta duqa da niyyar gaisheta Ummy tayi saurin tarota itama ta rungumeta cikin farinciki.

Ashraf daya fito ya jingina da mota Kasa daina kallonsu yayi ganin yadda suke murna daga ganinta kawai kuma da alamu sunma mance dashi.

Be ida sanin sun mance dashiba saida yaga sun juya su duka sun nufi cikin gida cikin raha da dariya.

Kutt.. Yafada yana Waro idanu ganin dagaske fa mancewa dashi din sukayi, afusace yamiqe daga jikin motar shima yanufo cikin gidan kamar zai tashi sama.

A falo suka yada zanyi baby sai zuba take kamar ri6a6iyar radio, sai roqonta take wai dan Allah tayiwa Ashraf magana aje daita Ummy nacewa bata isaba saidai ita ta gayamashi da kanta itakau saudart sai dariyar dramarsu take.

Suna haka sukaji an banko kofa an fado ciki Wanda hakan yasasu dagowa dukansu suna kallon kofar.

"Laa wai Ashe kana waje" inji Ummy Wanda hakan yaqara fusatashi ya turo baki yana ida shigowa falon

Itadai saudart kauda kai tayi tana ta6e baki don ita kwata kwata shagwa6ar dayake haushi yake bata.

Saurin daidaita zama baby tayi tana qaqalo murmushi tana gaidashi.

Banza yayi daita yawuce ya zauna kan wata kujera nesa dasu sai cika yake yana batsewa.

"Ummy ina kwana?" Yafada yana hura hanci

"Lfy lau, lafiyarka kaketa hawa kamar flour da yeast yaima yawa?" Tafada cikin sigar tsokana

Kallon baby dake faman danne dariyarta yayi ya gallamata harara tayi saurin sadda kai qasa sannan ya kwa6e fuska

"Ummy yanzu ace nazo gidannan amma ko lura dani bakiyiba sbd wancan" yafada yana gallama saudart harara, aikau akaci sa'a shi take kallo lokacin daya watsamata hararar, hakan yasata kauda kai tana ta6e baki cikin zuciyarta.

"Saika rungumi sorry, aini idan daughter na waje macewa nake da kowa" inji Ummy cikin halin ko-in-kula

"Amma ai kinsan da tsohuwar Zuma ake magani ko?" Yafada yana turo baki

"Waya gayamaka? Sabuwar ma tanayi, wani sa'in ma tafi guarantee" tafada tana antayamashi harara sannan ta maida hankalinta Jan saudart data sadda kai tana saurarensu tafara janta da fira tana amsawa a kunyace itakam baby anyi 6amm ankasa magantuwa.

Ahaka aka gabatar musu breakfast sukadan ci sannan suka tashi zasu tafi baby sai liqewa saudart take tana mata rada Itakuma saudart na antayamata harara.

Haka suka fito har wajen da motarsu take.

"Anty ayimana tsarabar honeymoon, yan biyu nakeso masu kyanki" baby ta sake radamata a kunne.

Tsarabar harara tasamu harda mintsini Wanda yasata Sakin qara tana dariya.

"Ummy zamu wuce, ayafe" tafada a kunyace.

"To Allah ya yafemana gabadaya, Allah ya tsare daughter ya kaiku lfy ya maidoku lfy kinji? Ya tsareku daga sharrin masu sharri"

Baby ma tayi caraf tace "Anty Allah ya tsare kuma karki manta da tsarabata" tafada tana kashemata ido daya

Harara ta bankamata tana jinjina kai alamun zata gane kurenta ne.

Ashraf dake gefe yanata kumburi ya matso kusa yana cewa

"To saura saniyar ware, nima a taimaka ayimani addu'an"

Dariya sukayi gabadaya sannan Ummy ta rungumoshi shima tana mashi addu'o'i sai wani basarwa yake yana amsawa da amin ala dole fishi yake. Sannan shima yashiga motar driver dake ciki tundazu ya tada motar yajasu suka fice suna dagawa juna hannu.

Ajiyar zuciya yayi bayan sunfita ya koma ya jingina da kujera yana mammakin irin son dasu Ummy suke mata dakuma irin girmamawar da takewa Ummy dukda shi be wani dauki nata iyayen da darajaba.

Cikin yan mintuna suka isa airport din, lokacin shadaya da Rabi saura.

Cikin dan qanqanin lokaci aka gama komai suka shiga jirgin suka zauna mazauninsu dake kusada juna ita daga ciki shi daga baki baki.

12 dot aka fara announcing din kowa ya maqala seat belt dinshi jirgi zai tashi.

Komawa itama tayi zata daura amma duk yadda taso daurawa takasa abinka da sabon shiga😆

Tana cikin kiciniyar sawa taga an ziro an amshi belt din Wanda hakan yasa fatarsu ta gogu da tajuna.

Saurin sakar mashi tayi tana qamewa kujerar idanunta a ware tana kallon spotless light hannunshi harya gama dauremata ya janye yakoma ya jingina da seat dinshi ya cigaba da danne dannenshi cikin basarwa.

Ajiyar zuciya tayi ganin ya janye sannan ta gyara zamanta itama tana basarwa.

Jin anfara announcing jirgi zai tashi yasata fiddo wayarta tayi plugging earpieces ta maqalama kunne don batason jin tashin jirgin, she's so nervous ga tsoro fall cikinta saidai batason bada kanta musanmman datasan wannan marar mutuncin na kusada ita.

Lumshe idanu tayi tana sauraron waqarda ta kunna, Rabin hankalin kuma nakan tashin da jirgin keyi.

Jikinta a qanqame yake amma saika samata ido sosai zaka gane don kallon farko zakaga kamar she's normal.

Saida jirgin ya daidaita a sararin samaniya sannan taji normal tasaki jikinta.

Lafewa tayi a kujera idanunta a lumshe tana jinta duk a takure musanmman datasan yana gefenta ga qamshin turarenshi daya addabi qofofin hancinta.

Koda waiter din jirgin tazo tambayar abinda sukeso bata tambayeta ba don duk tunaninta barci take.

Ashraf kadai ta tambaya shima yace beson komai.

Tun tanajin abinda ake sama sama harwani barci mai shegen dadi yayi gaba daita.

*SPAIN - MADRID*

cikin barci taji kamar ana janye mata bargo, hakan yasata qanqame abinta tana yatsine fuska.

Jitayi an qara ja ana cewa "hey wake up"

Ahankali tafara bude lumsassun idanunta da barci be ishesuba.

Dishi Dishi tafara ganinshi har ganinta yadawo daidai

"Wake up sleepy head" yafada yana tashi tsaye

Saurin miqewa zaune tayi har bargon na faduwa.

Saurin duqawa tayi ta daukeshi zata linke sai wani tunani yafadomata arai.

Daga ina wannan bargon? Tasan daga ita sai kayan jikinta tayi barci, to shi bargon daga ina yafito.

Gani tayi wata waitress tazo taba Ashraf wata Leda tana murmushi.

Amsa yayi sannan ya miqawa saudart yana cewa

"Saiki basu bargonsu ko?"

Amsa tayi batareda tasan ko menene ba sannan ta miqama waitress din bargon tabi bayan Ashraf dayayi gaba.

Wani irin sanyi ya suroma saudart data fito daga jirgin, yadda kukasan tana cikin fridge

Qanqame jikinta tafara yi tana bin ashraf, saida suka amshi kayan su sannan Ashraf yajuyo yaga yadda take dan qanqame jiki.
Chapter 35 · 0% Book details