← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 111

Sashe 13

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke dalla malama kyaleni, na dade ina addu'a Allah ya bayanamin ita ko tazo ta daukeshi sutafi nima in wala, yau naganta kuma saiki hanani murna?"

"Mtcheew, ke kika sani ai... Ina yini anty" inji teema tana kallon Saudart da tundazu binsu kawai take da kallo.

Murmushi ta qaqaro ta amsa tana cewa "bismillah Ku zauna mana"

Harara suka gallama juna teema da baby sannan baby taja kujera takawo kusada Saudart tazauna tana cewa
"Kusada anty ta zan zauna"

Ta6e baki teema tayi tana harararta.

"Dadin abin ba taki kadai bace"

Murmushi Saudart tayi dukda haryanzu bata ganesuba Amma sai gani take kamar ta ta6a ganin fuskar baby wani waje Amma takasa tunawa.

Ido tayima maryam akan akawomusu abin ta6awa.

"Sannunku yanmata"

Tare suka amsa da Yauwa, baby na dorawa da

"Ina wuni antyna ta kaina"

Murmushi tayi sannan ta amsa da
"Lfy qalau... Saidai ban wayekuba"

Caraf baby tace "laa anty baby ce halan yasha baki labarina nidince baki ta6a ganiba"

Kan Saudart ne ta kulle

"Baby?"

Kallon teema baby tayi itakuma ta antayamata gwalo.

"Wato dan wulaqanci ko maganata baya miki kenan, kai yaya Ashraf?"

Jin ta ambaci sunanshi yasata gane kosu waye, sai yanzu taga Ashe kammanin take gani a fuskarta.

"Ba kece uwar cusa kai ba kwarjini ba? Ai kadanma kika gani" inji teema tana mata dariya.

"To waya Kasa dake? Yar sa eyes kawai" saikuma tajuyo kan Saudart.

"Anty ni sunana baby qanwar lovely dinki, Amma kina iya kirana da mhiz Meebee sunan da nikeso aringa kirana kenan Daga yanzu, baby yayi kauyanci dayawa, koba hakaba?" Tafada tana kallon teema daketa antayamata Harara tundazu

"Bansaniba, waike kam baki iya aro nutsuwa kona d'an lokaci bane? Gabanfa surukarki kike?"

Waro idanu tayi sannan tayi saurin kada kai sannan tajuyo kamar saliha tana sunsunne kai.

"Mun sameku lfy in-law?"

Kamar me ta6in hankali takuma zabura ta gyara zama tana antayama teema Harara.

"No way! Bawani kunya, nadade ina jiran tazo tarabamu da jalli joga kuma yau inganta kice zaki hanani bayyana murnata? Bakida hankali"

Yar dariya ta kufcewa Saudart daketa kallon ikon Allah tundazu.

Itama baby tawani maqe murya tana kwaikwayon dariyarta.

"Kai anty kin iya dariya, wannan da ita kadaima kina iya siye zuciyar kowama" tasake maqe murya tana qara dariyar.

Dariya Saudart tayi tana girgiza kai, lallai wannan uwar rawar kan ce kanwar A.A? Lallai tahuta dabata dauko baqin halin yayanta ba.

"Anty kiyi hqr wlh haka take wani sa'in kamar sabuwar kamu"

Dariya Saudart tasakeyi tace "A'a qanwata ba sabuwar kamu bace, ko baby"

Turo baki baby tayi "mhiz meebee dai anty"

Daga gira Saudart tayi tana cewa "oops na manta, mhiz meebee"

"Yauwa antyna, wlh bakiji yadda sunan yayi dadiba abakinki"

"Kamar yadda nake fadamiki kafin wannan amebo din ta katseni, ni qanwar lovely dinki ce, kuma auta agidanmu.

Ina schooling a Ahmad bello uni, yanzu haka ina level 200, best colour dina pink, best food dina shashaka, ingayamiki har saceni kina iyayi da ita, best hobby dina kwalliya, I can do make up for devil ma, bana tara tarkacen qawaye, wannan itace ma nake dan maneji daita, a rayuwa babu mai takurani kamar lovely dinki, ya matsa mini, kiyi hqr fa nasan da ciwo a kushe masoyinka Amma bakin gaskiya ta nake fada, dan Allah ki taimaka ki aureshi Kitafi dashi wlh dama nagaji dashi ya isheni sbd..."

Dundu teema takaimata abaya har saida ta duqe.

"Wlh bakiyiba baby, shegiya naga Wanda zai qara rakaki wani waje" inji teema tana harararta.

"Anty kin ganiko?"

Saudart dataci dariyar dramar su tace
"Haba kyaleta, yanzu dai ga wannan kudan ta6a" tafada tanama maryam ido dake tsaye tundazu tana dariyar dramar baby akan ta qaraso.

Qarasowa tayi ta ajiyemusu , snacks ne wadda sukeyi da drinks.

Gutsira daya baby tayi ta Waro idanu, tauna take tana lumshe idanu harda wani rausaya kai.

Teema kau kamar taita kifamata mari don takaici.

"Wow anty, anan akeyin snacks dinnan?" Kadamata kai Saudart tayi tana murmushi.

"Wow yummy, insha Allah anan za'ayi mana snacks din birthday dina kou?" Ta qarashe zancen tana kallon teema.

Guzurin Harara tasamu awajenta hakan yasata kauda kai.

Haka taita zuba surutunta hankali kwance, Saudart kau sosai baby kebata dariya saboda surutunta da rawar kanta.

Tun bata biyemata harta fara biyemata, Tass ta cinye snacks dinta yayinda teema tarage itama kawai saboda kunya, itakau baby ko a jikinta acewarta ai antynta ce bawani kunyarta dazataji.

Haka Saudart ta zagaya dasu bakery din part part, sosai baby ta dinga santi tana yaba bakery din itadai Saudart dariya ne nata.

Saida suka zagaye koina a bakery din sannan suka dawo nanfa baby tafara daukarta hoto. Ta dauketa ita kadai suyi selfie gabadaya.

Haka sukayitayi Tun teema na Dari Dari harta ware itama ganin yadda Saudart ta saki jiki dasu, abinka da wayyaya.

Sai anan Saudart tagane Ashe Duk jirgi daya ya kwasosu don zani ce ta tarda muje.

Sai qarfe biyar suka bar bakery din Bayan sunyi exchanging din number sannan Kowanne tacika mashi shopping bag da kala kalan snacks.

Haka suka dawo gida sunata labarin kirkin Saudart...✍

Ummin fasihu ce🧚‍♀

🤵🏻👰🏻AUREN KWANGILA👰🏻🤵🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Sorry for the late post, wata hidimace ta tasomana yanzu qila sau daya zan dinga post arana, Amma idan nasamu sarari zaku samu ko sau biyune.

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

021

Knocking da akayi a kofarshi yasashi dagowa.

Sake knocking akayi, ahankali ya bude baki kamar mai ciwon baki yace
"Yes? Come in"

Ahankali aka bude kofar aka shigo, haryanzu be dago kaiba ta kalli mai shigowa ba don Duk a tunaninshi Sadeeq ne yagama wasan 6uyar dayake dashi yazo.

"Hellooo my man"

Hakan yasashi dagowa ahankali, idanunshi ne suka sauka akanta.

Kamar kullum tana cikin tsukakkun kaya, wando high waist baqi da shoulder less vest fara sai rolling din dan yalolon gyale fari datayi.

Cikin karairaya fuska dauke da murmushin barikanci ta qaraso gabanshi taja kujera ta zauna, kafa daya kan daya.

Dauke kanshi yayi batareda yace mata uffan ba yacigaba da harkan gabanshi.

"Man?.. Ya kake?"

Banza yayi daita

"My... Am talking"

Sai alokacin ya dago ya kalleta Saidai qala bece ba.

"Man, Baka maraba da zuwana ne?"

Nanma shiru Saidai bebar kallontaba.

Narke fuska tayi cikin duniyanci

"Man, why are you giving me tough time? Meyasa kakeda riqo? Nasan nayi kuskure ada, Amma izuwa yanzu ya cancanta ace ka yafemin, man nobody is above mistake kaima kasani, am sorry, nayi nadama please give me another chance" ta qarasa zancen tana qaqalo hawaye

Maida kallonshi yayi akan abinda yakeyi batareda ya sake bi takanta ba.

"Man.."

"Look Suzy, please get out, why zakizo kina distracting dina? The last time I checked na hanaki zuwa office dina, then why zaki addabeni?" Yafada cikin Fushi

"Haba man, what happen to us, da ba haka kakemin ba, nasan nayi laifi, kuma na tuba, ko Allah mukayiwa laifi muka tuba muka roqi yafiyarshi yana yafemana, bare mutum"

"Ni laifi kikayi min? Bakiyimin komaiba, idanma kinyi na yafemaki, Shikenan?" Yafada cikin qosawa.

"Ba Shikenan ba, yakamata mukoma yadda muke da idan dagaske ka yafemin din"

"Wannan kuma ne ake kira impossible tense, idan an mutu ba'a dawowa baby, so forget"

Kukan munafirci ta fashe dashi

"Look, this is an office ba kasuwa ba, please get out"

"Man.."

"Out or I Call the security"

"Yanzu Ashraf ni kake kora? Nice fa, suzyn ka"

"Ada kenan, that's past tense, yanzu nasan kinfini sanin matsayinki awajena, and don't forget very soon zanyi aure to the love of my life, nasan kina sane da hakan, so please get out before I throw up"

Shiru tayi takasa cewa komai sai kallonshi datake ga hawaye sai bin kuncinta suke.

Ganin yafara danna landline nakusadashi alamun zaiyi kira yasata tashi afusace.

"Ok muzuba mugani. Zan fita Basai ka hadani da qatin banzaba, zan fita office dinka Amma bazaka ta6a fiddani a rayuwarkaba, I will hunt you till eternity, kai nawane ko kaqi ko kaso so is better kama so"

"Naji fita"

"Zan fita din ne, zan fita!" Tafada tana daukar Jakarta ta fice a hasale.

Guntun tsaki yaja sannan ya maida hankalinshi saman system dinshi.

Bayan mintuna biyar sai gashi an sake knocking, be dagoba bare ya amsa.

Sake knocking din akayi nanma shiru hakan yasa mai knocking din budewa yashigo.

Kobe dagoba yasan Sadeeq ne.

Qarasowa Sadeeq yayi sai rarraba idanu yake alamun rashin gaskiya sannan yaja kujera ya zauna.

Ko dagowa ya kalleshi beyiba bare yasa ran zai tankashi.

"Sir A.A barka da warhaka" inji Sadeeq kamar wani na Allah.

Dagowa Ashraf yayi ya antayamishi wata uwar Harara.

"Ka gama guje gujen?"

Dariya kesan kufce mashi yayi saurin maidata

"Guje guje kuma sir?"

"Zakaci ubanka ne, wato dan ka maidani sa'anka kawani gayyatomin yan jarida ko and to add salt to injury ka tafiyanka da drivern ko?"

Yar dariya Sadeeq yayi sannan yace
"Afuwan sir, wlh tsoro naji, ganin antayen hararan da kakemin yasa naji tsoro nagudu, Amma kaika maidata gida?"

Wata uwar Harara yasake lafta mishi

"Zakasan Wanda ya maidata ne idan wannan watan kaji muqui"

Zaro idanu Sadeeq yayi

"Haba ranka shi dade, wlh natuba,ka riqemin salary ai kagama dani, please Allah ya huci zuciyarka"

"Zakayi bayanine"

"Haba ango mai jiran bed wajen amaryarshi Saudart, please inci alfarmar antyn tawa mana"

Jifanshi yayi da pen din hannunshi

"Kasake kiramin sunan nan a office dina saina sa6amaka"

"Ohh sorry to masoyi a wajen Suzy baby yar kwalisa"

Tamke fuskarshi Ashraf yayi ba alamun wasa.

"Ina wasa dakaine Sadeeq, ka mance agaban boss dinka kake? Tafi nayi suspending dinka na wata daya"

Wani tsalle Sadeeq yayi sai agabanshi

"Sus- me? Haba boss Dan Allah kayi hqr natuba"

Saida ya wanashi sosai sannan ya haqura.

"Ashraf naga fitowar Suzy Daga office dinnan, metazo yi?"

"Bansaniba"

"Please mana"

"Kacika gulma ko?"

"Ba gulma bace wlh, please gayamin"

Resting yayi a kujerarshi yana dan jujjuyawa

"Wai tazo inbata second chance"

"To bata din zakayi?"

Harara ya gallamashi

"No chance in hell dude"

"Hmm Baka ganin yakamata Ayi a daura auren nan ko ta sararamaka?"

Banza yayi dashi.

"Ashraf magana Nike, kabashi kudin yanzu shi yarage yabaka"
Chapter 13 · 0% Book details