← Book details Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 111

Sashe 26

Auren Kwangila Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ok Kije ki kwanta, zan bugo later akwai maganar dazamuyi"

"Alright dad"

Datse kiran tayi tana Sakin ajiyar zuciya.

Haryanzu takasa yarda da abinda yafaru dazu, wai yaushe ma yadawo gidan bata saniba?

Allah kadai yasan tun yaushe yake zaune yana qaremata kallo.
Ashe shiyasa takejin kamar ana kallonta.

*idiot* tafada cikin jin haushi da takaici.

Babu abinda yafi qonamata rai kamar kallon rainin daya bits dashi.

Tsaki taja ta tashi tana tattare plates din dining din don abincin ma kwata kwata yafita akanta.

Saida ta dauraye plates din data 6ata ta gyare saman sannan ta haye da niyyar ita da zama qasa kuma har abada saidai ta sauko tayi abinda zatayi ta haye sama.

Kwance take rigingine akan gado fuskarta na kallon ceiling saidai idanunta a lumshe suke amma ba barci take ba don duk abinda Beebah ke fadi duk a kunnenta ne.

Saida takai aya sannan ta numfasa ta kalli suzyn dake kwance tundazu kamar mai barci.

"Toyaya kikaji tsarin?"

Kamar bazata motsaba sai can ta saki ajiyar zuciya tana bude qananun idanunta akan fuskar Beebah sannan ta motsa la66anta dakyar tace

"Kenan duk wannan shirin da kike lissafowa duk inanan ina sagale da baki ina ganin su a tare za'ayi shi? You don't get me Beebah, banaso, vanason inwayi gari da tunanin my man tareda kowacce irin tsinnana, I want him for me, me alone, bazan iya jira harna tsawon lokacin da kike cewaba, na tabbata izuwa lokacin zuciya ta tariga da ta tarwatse"

Zama Beebah tayi bakin gadon kusada ita tana cewa

"Suzy, wannan itace kadai mafita, ya kike magana kamar batareda ke mukaje wajen ta ba, kamar bakiga yanayinta ba, yarinyar nan yar barikice, tasan takan barikanci, kalamanta ma sun nuna hakan, kawai zuru ne zaici zuru, ta hanyar data biyomana tanan muma zamu bida ita, ashraf nakine ke kadai, kisa wannan a ranki" tafada cikin qarfafa gwiwa.

Haka taita lallaminta harta samu nasarar bida ita hanyar datakeso, bata bartaba har saida taga ta dorata akan abinda sukeson cimmawa.

Yau kwana biyu da faruwar wannan al'amari tsakanin Ashraf da saudart.

Basu sake haduwaba don kowa yasake Jan baya da Dan uwanshi fiyeda da.

Ita tabar dadewa a qasa shi kuma yabar dawowa dawuri.

Don haryanzu kowanne cike yake da takaicin abinda yafaru ranar.

"Dad, I really need to get back to my work, I can't take it anymore, kullum ni kadai acikin gida kamar mayya? Nidai zanyi resuming on Monday, nagaji ai wannan deal din maku be shafi aikinaba, so am resuming" tafada cikin yanayin jin haushi don jitake kwata kwata ta tsani zaman gidan.

"Ban qi ta takiba shalele, it's normal idan kikayi resuming amma baki tunanin yakamata kiyi advancing din profession dinki? A matsayinki na Matar A.A be kamata ace kina zuwa bakery ba da sunan aiki, it's embarrassing"

Jim tayi tana sauraron daddy tana jin maganganun nashi wani bambarakwai musanmman *Matar A.A* daya ambata.

"I don't get you dad" tafada cikin Rashin fahimta.

Gyara zama dad yayi a bangarenshi yana murmushin samun nasara.

"Abinda nake nufi shine, tunda kinada bakery kuma kina iya gudanar dashi ko kina nan ko bakya nan, why not kisamu wani aikin daban da takardunki?"

Jimm tayi tana sauraron daddyn lokaci daya kuma kwakwalwarta na nazari akan maganarshi.

Katsemata tunani yayi da cewa

"Kinga zakifi samun kudi, ga na bakery ga salary, nima nan am trying my best, kinga saimu hadu mu hada qarfi wajen hada kudin mijinki mu biya a warware komai kowama ya huta"

Shiru tayi na yan daqiqu tana nazari akan shawarar Dad.

Eh hakane, wannan shawara ce, dukda bata cika son aikin office ba tana iya daurewa tayi kodan fita daga wannan vanzar deal din marar kan gado.

"Ya kikace shalele?"

"Deal, saidai ta ina zan fara?"

"Bakida matsala sweetheart, ba ganiba? Daddy zaiyi komai wa shalelenshi" yafada cikin fara'a.

"Awnn! Thanks dad, I love you"

"Love you more"

Tunda suka gama wayar yaketa aikin zabga murmushi.

"A.A, yanzu lokacina ne" yafada yana shafa gemunshi.

"Ummy please.. Zan kawota, I promised" yafada kamar zaiyi kuka

"Ni dalla tashi min, haka kake cewa kullum, sai yaushe zaka kawota din? Nida diyata ace sai an Mani rowarta? To wlh kaji na rantse gobe gobenan nakeson ganinta kaji ba gayamaka" tafada tana tureshi daga kan cinyarta.

Qin daga mata cinyar yayi, data tureshi saiya koma.

Itakau baby na daga can gefe akan kujera tana satar kallonsu tana ta6e baki.

"Wai bazaka tashi ba saika karya ni?" Inji Ummy tana qara tureshi

"Ummy please mana, wai me nayi ne?" Yafada yana qara komawa

"Mekayi? I told you I want to see her kana min rowa?"

"To ai Ummy magana tariga ta qare tunda har kinyi rantsuwa, you'll see her tomorrow, saiki cinyeta karki barmin ko kingi"

Rankwashi tabashi lafiyyaye

"Eh din zan cinyeta din, dagani"

Shafa kan yake yana yamutsa fuska kamar zaiyi kuka

"Kai Ummy wlh yanzu kinbar so na"

"Dama, ai yanzu nabar wayata yayinka, yanzu lokacin autata ce bakaiba godai godai dakai"

Kallon saitin baby yayi daketa Satan kallonsu tundazu tana qumshe dariya.

Ganin zai kallota yasata saurin kawar da idanu tana duba littafin hannunta a wayance.

"Ke jeki hadomin coffee" yafada yana tamke fuska.

"Bazata hadoba, kaje Matar ka ta hadamaka"

"Kai Ummy..."

"Ke tashi kiwuce sama kaima katafi gida ka baro diyar mutane ita daya"

Da sauri baby ta tashi tayi sama don dama tunda yace ta hado coffee take jinta kamar saman qaya.

Haka ta tisoshi gaba har wajen motarshi riqeda kunnenshi daya shikau sai qara yake saki qasa qasa, Kai kace ba A.A bane uban yan ji dakai.

Haka ta turashi mota ta rufe taja baya tana dagamashi hannu harya fice yana zum6urar baki...✍

No editing, kuyita hqr da mistake please🙏

Ummin fasihu ce🧚‍♀

👰🏻🤵🏻AUREN KWANGILA🤵🏻👰🏻
(Contract marriage)

Allah ka yayemana wannan annobar (covid19)🤲

Allah ka bamu zaman lfy a qasarmu Nigeria🤲

Allah ka ji6anci lamuranmu, karka barmu da kanmu🤲

Story written by Ashaanty love
(Ummin fasihu)

Note: nayi mistake a page daya gabata, page 34 ne maimakon 33 Danasa.

So yanzu na 35 ne zamu tashi.

Ina fans din Auren kwangila? Your comments is making me go gaga💃

Ina godiya, keep it flowing💖

Ina cigiyar sis hajara, maman twins da maman fateema, fatan suna lfy.

Koko babu data ne😂 gaskiya karku badamu please, kar ayimana dariya, kufito saudart na kewarku.

The page is dedicated to all Auren kwangila fans, kuyi yadda kukaga dama dashi💃💃💃💃💃

035

Tana kwance tana sliding din wayarta tana shiga da fita acikin groups don yanzu itama tafara gwanancewa a chatting don shi ke debemata kewa yanzu tunda tarage zaman qasa.

Tana cikin shafe shafen taga massage yashigo na baby.

Shiga tayi don gani

*yeee sweat Matar yaya💃*
Abinda taga ta turo kenan

*hmm ina sallamar kuma?*

*oops na mance, am just too happy ne wlh*

*ai haka kike, yar rainin sense😒*

*kai aunty wani sa'in ke joy killer ce wlh😕*

Sticker dariya saudart ta tura mata

*😆😆 lol, seems autar tamu farinciki, am sorry to, fesamin naji👂*

*anqi din😏*

*haba autaras, c'mon please🤕*

*anqi din, sai kinzo zakigani, bake bace kike cewa ban iya girki ba? Gobe ki sako wani extra takalmi a jakka don saikin mance na kafarki don santi😂*

Dariya saudart tayi a zahiri, sosai take jin baby har cikin zuciyarta, shirmenta da barkwancinta ba qaramin sata nishadi yake ba.

*Tofa, zuwa zakiyi kiyi girki ne*

*laa badai be fadamaki gobe zai kawoki ba?😳*

Daga gira daya saudart tayi, cikin zuciya tana cewa 'to haka akayi?'

*dagaske😳💃💃💃 yee finally! Kullum saina mashi nacin zuwa yana cewa ba yanzu ba, qila surprise zaiyimin*

Ta tura tana ta6e baki tana yatsine fuska.

*oops🤦‍♀ ko meyasa na fadamiki? Please karkice nafada maki👏*

Murmushi saudart tayi sannan ta turamata

*zanyi tunani akai😎*

*please anty ta ta kaina, mata a wajen sweet Ashraf dinta, an buga dake anbarki, daga ke babu qari, kiyi Kane Kane kiyi bake bake ki wala ki sarara keda kishiya saidai kiji wai, wai dinma wai😜*

Sosai saudart tayi dariyar kirarin datayimata.

Haka sukayita fira har goman dare sannan suka sauka.

Sosai saudart taji dadin fitar daxatayi gobe, ko babu komai zata fita ta shaqi iskar rahama.

Bata Dade ba sosai barci yayi gaba daita.

********************************

Tunda gari ya waye take jiran tsammani, tasan dolene yazo yayimata maganar tafiyar amma shiru kakeji wai mallam yaci shirwa.

Yau Friday so sai wajajen 10:30am yafito.

Kamar kullum batareda ya kalli side dinta ba ya nufi stairs, yana tafiyarshi daya saba hannu daya cikin aljihu dayan kuma riqeda briefcase.

Tabbass taji fitowarshi hakan yasata gyara zamanta tayima kofar ta quri tana jiran jin yabugo tana ayyana Jan ajin dazata yimashi kafin ta budemishi.

Batayi auneba taji tashin mota.

Da sauri ta miqe ta nufi window dinta dagudu saidai harya fice daga gidan.

Wani Abu taji ya tokareta a wuya.

Kutt.. Badai playing dinta baby tayiba?

Gashi tasaka ran fita sosai, a hassle ta jawo wayarta da niyyar kiran baby sai kuma tafara tunanin me zata gayamata? Ai hakan kamar tona asirin yanayin zaman su ne.

Haka takoma ta zauna cikin jin haushi da mutuwar jiki.

Haka ta yini a ranar tana jinta wata suku suku daita.

Tana kwance wajajen qarfe dayan rana taji ana Danna doorbell.

Tsaki taja ta gyara kwanciya.

Jin ba'a da niyyar bari yasata tashi ta yafa gyale ta sauko fuska babu walwala don haryanzu takasa daina jin haushi.

Tana budewa tayi tozali dashi.

Kallon sama da qasa tayimashi tana nazarin shigarshi.

Cikin girmamawa yadan russuna.

"Good evening ma'am"

Bejira amsarta ba ya cigaba dacewa

"Sir yace inzo inkaiki anguwa"

Tsayawa tayi tana kallon shi.

Lallai so yafi qarfin ya kaita shi? Hmm tafi nono fari dama batada niyyar sake ganin wannan mummunar fuskar tashi.

"Ok am coming"

Ta koma ciki ta rufe kofar shi kuma yakoma mota.

Haurawa sama tayi da sauri don kawai saita tsinci kanta cikin farinciki.

Quick shower tayi sannan tafito ta shirya cikin wani dakakken lace maroon da ratsin fari anmata style din simple Zane sa half gown mai tsaga gefe da gefe sannan tadaura kallabi style din zahra buhari ta Dora farin gyale akanta ta yafa ta dauki handbag fara takalmi ma farare, hannunta na dama daure da wrist watch fari sai zobunna.
Chapter 26 · 0% Book details